Chapter 45

206 20 4
                                    




🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
            By
    🌹Teemahcutey🌹

Page 45.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Kallan kallo suka shiga yiwa juna kamin Ajmal tace; "kamar d'azu naga ta fita tana amsa waya"

Zama sukayi domin jiran dawo war ta, shiru shiru kake ji bayan shud'annin wasu awanni.

Tini y'an tarbon lefen suka fara watse wa se makusan tan y'an uwa d'ai d'ai ku.

Mommah ce ta kira Meenah tace;
"Ya kamata ku dawo gida saboda an watse a nan"

Shiru Meenah tayi kamin tace;
"Tau Mommah, amma Adda Miemie muke jira"

"Jira? Kamar ya jira? Ina ta tafi ne?

Shiru Meenah tayi saboda rashin sanin takamammiyar amsar da zata bata, in i'na Meenah ta shiga yi;

"Ehhh!! Amm..!! Ai... dama.. d'azu da nazo ne friends inta suka cemin ai sun ga kamar ta fita"

"Toh ni dai dan Allah ku dawo idan ta dawo" "kitt" Mommah ta datse kiran duk da hankalin ta ya kasa kwanciya, amma ba ta kawo komai a ran ta ba dan gane da y'ay'an nata.

Lokaci ya tafi sosai inda k'awayen ta suka gaji da jiran ta suka fara wuce wa Meenah na yi musu godiya kuma tana basu hak'uri, haka dai a kayi ta jan lokaci har Magriba ta gaba to.. to fa nan hankalin Jama'a ya fara tashi, sosai aka shiga neman layin wayar Miemien amma yana ringing ba'a d'aga wa.
Mommah ce da Meenah da kuma sauran y'an uwa kowa ya kasa tsaye ya kasa zaune, duk inda ake tunanin zata iya tafiya an kira amma ba labari, abu wasa wasa har aka yi magriba ana batun isha'i, wani irin tashin hankali ne ya bayyana akan kowa, da sauri aka kira Poppah aka sanar mishi abunda yake faruwa, shima karan kan shi hankalin shi ya kai mak'ura gurin tashi, ba tare da b'ata lokaci ba aka bazama neman ta lungu da sak'o amma shiru.
K'ara tambayar Abrar a kayi akan ai suna tare a cikin wane yanayi ta fita?

Bud'ar bakin Abrar tace; " suna zaune ne, kawai ta fita cikin fara'a tana amsa waya,"

Jinjina kai kowa yayi ana taradadin wannan abun da kuma jiran tsammani, anyi compiling case gurin police, suma suna iya k'ok'arin su, inda a ka saka matakan tsaro ko ina ana neman ta, haka ma hukumar gidan talabijin da radio ba'a barsu a baya ba, suna k'ok'ari tuk'uru gurin bayar da sanarwa a kai a kai ko Allah ze sa a dace.

Dare ya gaba to sosai amma ba labari,
Meenah kam zauce wa ne kawai ya rage tayi, haka kawai ta zare hijab ta bi hanya, Mommah ce ta yiwa Abrar umarni a kan tabi bayan ta ka da taje ta aika ta ba dai dai ba coz tasan halin ta.

Haka a kayi kuwa tabi bayan ta.

Ko ina akwai haske na manyan fitilu da gidaje daban daban hakan yasa ta hango ta acan, tabi hanyar gidan d'azu, wanda suka je ga kawo lefen, dama gidansu k'waar Miemie ne Ajmal, a mai makon ta bi kwanar da zata sada ta da gidan se tabi wata daban.

Abrar dake ta faman doka sauri domin ta iske ta a take gaban ta ya fad'i, zaro ido tayi ganin Meenah na bin exact hanyar da Miemie tabi har aka sace ta wato k'wasai, wani kakkauran yawu ta had'iye muk'urt.

K'ara saurin tafiyar tata tayi duk da tasan ba abunda zata gani, amma dai ta tsorata da lamarin, da sauri kuma iske ta tace:

"Ke Meenah, ina zaki haka wai?

"Zani neman Adda"

"A nan d'in? Haba!

"Eh mana wata k'il Allah yasa na dace"

Haka ta ci gaba da tafiya Abrar na binta, bata taka burki ko ina ba se a daidai inda aka saka Miemie a motor..

Jikin Abrar ne ya d'auki rawa matuk'a.
Ganin Meenah ta tsaya tan dube dube yasa taje daff da ita tace;

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now