Chapter 35

274 19 2
                                    




🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
           By
🌹Teemahcutey 🌹

Page 35.
*

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Zaune take tana tinani tare da juya wayar da ke hanun ta, a ranta take fad'ar to wannan wacece da tasan sirrin ta haka? Tambayar da take yiwa zuciyar ta kenan ba mai amsa mata.

Murmushi tayi kawai tare da danna wa number kira, ai kuwa cikin sa'a wayar ta shiga, amma kashhh!! Wayar har ta gama ringing ba'a d'aga ba.
A b'angaren Abrar kuwa wanka take shiyasa bata d'aga kiran ba, jin k'arar wayar tata ne yasaka a gurguje ta fito daga wankan.

Ganin number da ta kira ta seda taji wani irin dad'i. Batare da 6ata lokaci ba ta danna wa wannan number kira.
Bayan Zeenatu ta d'aga ne suka gaisa kowanen su cikin isa da izza... y'ar magana sukayi daga nan suka yanke hukuncin had'uwa kawai dan tattaunan wannan lamarin.. nace hmmmm.

A gaggauce Abrar ta shirya domin a yau ne suka aje zasu had'u saboda tsananin zumud'i da rashin hak'uri, da son tarwatsa rayuwar wasu.

Bayan ta fito ne though a yanzu Mommah bata cika zama gida ba, saboda kusan ita ke jinyar gwammah..

daga Meemee se Abrar ne a gidan.
Futowa tayi a shirye tsafff....

(Dama Mommah takan arawa Abrar motar ta sometimes saboda kada taji wani abu tunda Meemee nada motor.. sosai Mommah take k'ok'arin sakata ajiki saboda ta d'auka da gidan su da nan ba banbanci,so 2days inan Mommah bata zuwa da motar ta a asibiti sedai Poppah ya kaita. Ta na nan ajiye gida)

Direct key in motar ta d'akko tacewa Meemee zata d'anje unguwa, "ummm" kawai Meemee tace domin gani take dai a yanzu kamar bata ra'ayin ta, so bata son tana shiga lamarin ta kwata kwata.

Parking lot ta nufa tare da tada motar, me gadi ya bud'e mata gate ta cillah ta kan titi..

Kasan cewar Ammie bata nan taje gidan marayu kai taimako shiyasa Meenah ta fito a parlour a bunta ta kunna TV ta saka ST NOVELLA tana kallan series inan BLOOD SISTERS, sosai ta shagala gurin kallan series in tana yi tana cin popcorn, bata san da zuwan Captain ba kawai taji mutum a tsaye kanta, aikuwa wani irin super tayi ta koma d'aya b'angaren domin tasan Allah ne ya cece ta ya gwada mata shi da tuni taji rankwashi a kai.

" wayo Allah nikam Allah ya jarabeni"

Captain da ke tsaye yace "mye kika ce?

" cewa nayi Allah ya jarabeni ya baby nikam ban da shak'at? Wlh fa duba ka gani ga hular nan a kan hanun kujera fa kwanta wa nayi shiyasa ta zame, kuma shikenan mutum ba yada ikon sakewa ya bud'e kan shi ya sha iska? Ni Allah ma ya taimake ni nayi kitso, nasan da a banye yake da tuni ka chafko wutsiyar gashin"

Shikam Captain a yanzu he's already use to irin yawan zancen da take zubawa cikin k'ank'anin lokaci.

Kwafa yayi tare da d'an takawa, ai kuwa tashi tayi ta k'ara matsawa domin bata yadda da shiba.

Dariya Fahad yayi tare da fad'ar "oya baby come here kyaleshi"

Meenah kam tsayawa tayi kamar gauluwa tana kallan Fahad.

Kwai kwayon muryan shi tayi ta fad'i abunda ya fad'a,.. daga bisani se ta kwashe da dariya tana nunashi.
"Wai baby come here kyaleshi... kamar wata k'aramar yarinya..... dariya ta k'arayi tana nuna shi tace "lallai kana ruwaa"🤣

Shima kallan ta yake yana 'yar dariyar yak'e domin kuwa yasan ta sakammai shi.😂

"Kee!! Ashe bayan duka rashin kunyar da kikeyi ashe hadda raina mutane kikayi? Ki kama kanki fa baby Allah zanyi maganin ki, dan kawai kinga banasan miki fad'a koh? Zan..

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now