Chapter 1

1.7K 91 20
                                    

Assalaum Alaikum warahmatullah

sunana Fatima Bashir, ina fatar wannan littafin zai k'ayatar kuma ban yadda wani ko wata yayi amfani da wannan damar gurin juyamin labari na ta ko wace siga ba, yin hakan ya sa6awa k'aida kuma babban kuskure ne, ina fatar zai samu kar6uwa a gurin ku.

Allah bamu amfanin abubuwan amfani da suke cikin wannan littafi mai suna ABUN ALFAHARI NA.







          ABUN ALFAHARI NAA

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai.

🧚🏻‍♀️ABUN ALFAHARI NA🧚🏻‍♀️

Zauna take kan kujera tana tunanin abubuwa da dama wa'enda suka wakana a rayuwar ta.

Ta zabgaa uban tagumi kawai kamar daga sama taji ana kiran sunan ta;

"Meenah! Meenah!!

"Na'am Mom" shine abunda yarinyar ta fad'a tare da tashi ta nufe inda taji kiran. Wani k'ayataccen falo ta nufa mai d'auke da dallah dallahn kujeru masu kyau, tsayawa tayi a nan tare da zaunawa tana jiran momy ta fito, Ac falon ta qarawa gudu domin dai bata cikin dad'in rai kwata-kwata ayau



Tana zaune sai ga momy ta fito, gaida ita tayi cikin rashin natsuwa kamar yadda ta saba  a nan Mom ta tambaye ta;

"Me kike yi a d'akin ku tun d'azu ke kad'ai? Ba an hana ki zama a d'aki ke d'aya ba? Me yasa da bakya jin maganar mu ne Meenah??

Sosa kai tayi tace;

"Ba abunda nake kawai ina neman wani abu ne"

"To shikenan kinsan dai bama son abunda zai ta6a lafiyar ki ko? Ki kula sosai kinji, dama ina son in aike ki ne gidan Hajiya Ramatu"

A nan ta bata sak'o kamin ta wuce d'aki Meenah tace;

"Mommah dan Allah ki aramin motar ki naje da ita!

Harara Mommah ta jefa mata;

"Ke bana son shashanci kinji ko, gidan wa kika koyi mota ne? Dallah b'ace min da gani shirmammiya kawai"

Kud'i ta d'akko mata wanda zata hau napep, kar6a tayi ta wuce tana y'an kunkunai.

D'akin su ta wuce ta yi wanka a gurguje ta sauya kawa ta saka duguwar riga na atamfa mai blue and dark blue da ratsin ruwan d'orawa, d'inkin ya kar6eta kasancewar ta dirarrar mace mai kyan halitta, fara ce komai na fuskar ta mai kyau ne musamman hancin ta mai tsawo da shi.

Gashin kan ta ta taje wanda ya kasance mai yawan gaske duk da ya kasance ba shida mahaukacin tsayi amma yanada mawadacin yawa wanda ba kowa yake son yi mata kitso ba, hakan yasa ta gwammace ta fake abunda ta saka ribbon, dama can ba ma'abociya won kitso bace

D'an kwali ta d'aura ta d'auki baqar jakan ta kasancewar baqar jaka ta fitar yar qarama mai kyau kana ta fice..

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now