Chapter 5

391 24 4
                                    

      5
🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na🧚🏻‍♀️
     Na
💕Teemahcutey💕
One can pay back the loan of gold, but one dies forever in debt to those who are kind. 
Thank you for your duas 💕💕💕

📝Cute writing association 📝

Koh da suka shigo school har an kammala assembly, ba tare da b'ata lokaci ba suka wuce classes.

Nidai Meenah zan bii domin na d'akko muku rahoto.

Ko da Meenah tazo class har mister Frank ya shiga wanda yake d'aukar su taking darasin Fine Art.

Leqa ajin nasu tayi bata ga alamun Waleedah tazo ba hakan yasa ta nemi guri a gaban ajin ta zauna.

Kamar daga sama taji an rufe mata idanu, ranta in yayi dubu ya b'ace, ba dan komai
ba sai dan mascaran da ta shafa kada ya goge, budar bakin ta tace; "Wace y'ar kutumar bu.... "keee dakata malama nice"
Walida ta fad'a tare da zagayowa suka yi hugging juna.

"Ai na d'auka wata yar rainin sense ce zata gogemin mascara" Daria sukayi suka tabe.
Anan fira ta b'arke tsakanin su domin har sun manta da akwai teacher aclass insu.

Kamar daga sama sukaji ance "hey what are your doing here?
Mrs frank ne yace haka..

"Sir we are just coming.. suka hada baki suka fad'a!
"Why did u came late?
"Sir it a pity we're sorry" suka fad'a.
"Ok come in..
"Thank you sir" Se suka qarasa a ajin

Dodecagone and polygon yake zana musu, a board.

"Qasss qass qass!!
Mrs frank ya juyo, "who's chewing gum in my class? Students can't you hear me?
Don't u dare let me repeat my self again!!Mrs frank ya fad'a.

Shiru sukayi ga baki d'ayan su domin ba wanda ya san me cinsa, bayan Walida da tasan Meenah ce, dama a front seat suke zama. Shiru ajin ya d'auka still aka rasa mai tankawa.

"Class rep stand up" Mrs frank ya fad'a..

Miqewa Meenah tayi; "yess sir.
"Tell me who's chewing gum in my class?
"Ehhhh ahmmmm Ehmmm sirrrrr it's me but sorry sir I won'.....

"Shut up your mouth stupid, get the hell out of this class" ya fad'a.
"Sorry sir it's a Pitt..!ya ka tseta ba tare da ta qarasa ba.
"Sorry for ur self get out.

Ba tare da b'ata lokaci ba meenah ta fita tana rangwada.
yaci gaba da abunda yake.

Meenah tarasa inda za taje domin tasan da an ganta waje zaune during class hour without any strong reason to za'a sakata punishment.

Kawai ta yanke hukuncin xuwa field acan bayan classes, gossip chair ta samu ta zauna ita kadai kamar mayya. Sai
warar idanuwa takai.
Daga can nesa ta hango wasu mage guda biyu kamar suna fada, haka kawai taga sha'awar zuwa gurin, ba tare da b'ata lokaci ba ta isa gurin.

Magen da tafi   girma ne ta kada d'ayan musan tanata yaqushin ta gwanin tausayi, Meenah taji tausayin qaramar musar... kawai tasamu dutse ta jefi wannan babbar dake kan qaramar.
Aikuwa ta tashi, se qaramar ta miqe tayi wuf tazo gurin Meenah tana kawowa daidai qafafun ta ta b'ace b'att.

Meenah ta duba bayan ta da gefenta tana tunanin, a ina qaramar musan ta tafi?
Ko dai ta wuce ne?
Ko da ta qara dubawa a inda suke fad'a taga ko da zata ga babbar amma bata ganta ba koh ita.
Kawai tace qila  sun gama fad'ansu sun wuce, ta tab'e baki ta wuce abunta, ta koma inda ta taso.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now