Chapter 12

296 24 2
                                    



🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na🧚🏻‍♀️
      By
⭐️Teemahcutey⭐️
Page 12

Tsarabar ku ayau.

*SIRRIN RIKE MIJI*
Ina son kusani cewa rashin kula da al adar ki yana daya daga cikin ababen abubuwan dake haina mata haihuwa ko kuma samun jin dadin rayuwar auren su

Ga matar da take fama da ciwon mara musamman lokacin al'ada, ko idan zai zo yana zuwa da ciwon mara, wata ma zakaga hattana birgima a kasa, ko taji kamar ciwo marar sauki ya mata wuka, ko rikicewar haila, ko jinin ya rinka zuwa da wari, ko karni, ko baki, ko yana zuba sosai to sai a samu: garin gwaiba  rumzali na asali  lemun tsami  ruwa lita biyar (5lrt) sai a dafasu a rinka sha karamin kofi sau biyu (2) a rana za a'samu nasara insha Allah.

_DOMIN TSAFTACE MAHAIFA_ Tabbas tsaftace mahaifa yana da matukar mahimmanci a rayuwar mata

ga mai bukatar tsaftace mahaifarta da kuma karramata da kashe duk cuta ko kwayar cuta dake zama bakin mahaifa, to wannan hadin da zamu yi bayani yanada muhimmanci musamman ga mai zafin mahaifa, ko kuma  yara suna mutuwa a ciki, ko mai fama da toshewar bakin mahaifa ko kuma matsalar ta farune sakamakon amfani da wadansu magunguna na hana daukar ciki ba bisa ka'idaba, ko  sha wasu miyagun kwayoyi, ko kuma yawan zubar da ciki, kuma hakan yana iya faruwa idan aka samu mace mai yawan bin maza,hakan zai iya haifar da kamuwa da manyan cututtukan da zasu iya lalata mahaifar.

☘️ganyen gwaiba
☘️ganyen lemun tsami
☘️garin rumzali
☘️Ganyen na'a na'a
☘️kanunfari rabin gwangwani
🍀ruwa lita biyar(5lt)

💐sai a hadasu wuri daya a dafasu, sai a tace idan antace sai a rinka shan karamin kofi sau biyi a rana safe da yamma, zai wanke mahaifa da tsaftaceta da kuma kasha duk wata kwayar cuta da zata iya shiga cikin mahaifa ta kawo illa ga lafiyarki

Ina son yan uwana mata kusani cewa kuna kuskure sosai a yayin da baku kula da lafiyar farjinki.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Ayau ne ake cika kwana ukku da rasuwar marigayi Alhaji Shehu.
Bayan anyi taro anyi mishi adduoe aka shafah kowa yasani inda yay.

Dama ayau poppah yana da niyar ziyartar shi amaqabarta domin yaqara nemar masa rahamar ubangiji.

Koh da ya iso abunda yagani sumar dashine kawai beyi bah . Inalillahii akawai yaketa nanatawa seda ya sai saita natsuwarshi kamun daga bisani kwallah ta gangaro mishi.

Fita yayi da gudu domin neman mai tsaran maqabartar.

Acan ya hangoshi riqe da buta Da alamadai ya d'an zaga ne, koh gaisuwar da dattijon keyiwa poppah be tsaya saurare bah kawai ya jashi suka shiga cikin maqabartar.

Nuna mishi ramenda aka tone yake yana fadan ina mahaifina?? Ina aka kaimin mahaifi??? Yana fad'a yana jijajiga wannan dattijon.

Inalillahii wannnan datijon yay tare da cewa "Bawan Allah dan girman wanda ya Halicceka ka kwantarda da hankalinka ka tsaya muyi maganar fahimtar juna.

Batare da poppah ya daina matsanancin kukanda yake bah yace :
"bawan Allah dan Allah ka gayamin mafarki nake?? yanzu shikenan an d'auke min mahaifi? Yanzu shikenan tsafi zaayi da mahaifi na? Wa'ennan waenni irin azalumman mutane ne? xasuyi da gawar mamaci? Me yasa addini yay qaranci a yanxu?? Ynxu shikenan an sada mahaifina da makwancinsa na gaskia amma wasu azzalumai sin sace??

Qara fashewa da kuka yay cikin hikima wannan dattijon ya rarrashe shi.

Zaune suke dashi da anty zahra da uncle Omar da gwammah bayan ya gama zayyane musu abunda yaje ya tarar ah maqabarta

Kukah anty zahra ta fashe dashi tare da w "Innalillahi waennah ilaihi raji'un...
Wai mye mutane suka dauki duniya ne?
Ina suka kaimin mahaifina??
Mahaifina shine *Abun Alfahari Na*
Yau gashi mai rabawa ta raba tsakanina dashi bayan haka kuma wasu matsafan Banza wa'enda basu san Allah bah sun sacemin mahaifi 😭 Ya Allah ya tonawa masu harkan safarar gawar mamata asiri" adaidai nan ta qara fashewa da kuka kamar ba gobe.
uncle omar ya rarrashesu domin shi akwai juriya sossai.
Gwammah kuwa tana gefe daya ba chasssss bah assssss.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now