Chapter 52

173 22 8
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
            By
    🌹Teemahcutey🌹

Page 52.

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

AHMAD's POV.
Zaune yake se faman tsaki yake ja, saboda tin a daren jiya ya yiwa Meenah missed call, kuma haka a yau ma yana kiran ta but is not reachable, duka se yaji ya damu.

Haka dai yayi mata sending text sannan ya cigaba da gudanar da binciken nashi, duk da beyi delivering ba.

Da farko yayi binciken Haidar tun daga gurin aikin shi, kuma an tabbata mishi akan  ba yada wani problem, haka ma ba yada  abokin gaba, kuma an gayamishi a kan son da yake yiwa fiancee inshi domin da wuya ka zauna da shi ba tare da ya baka labarin ta ba.

Haka dai ya cigaba da binciken, although duka a gidajen biyu ya san cewa akwai adopted childs wa'enda ainahin ba a nan ne gidajen su ba, wato Abrar da Zeenatu.

Beyi wani dogon bincike a kan su ba, shiyasa ma ya tsallake lamarin nasu ya cigaba da na sauran.

Baya wani yawan zama a bakin gate in gidan su, ko aiki ya dawo a gida yake zama baya fitowa se da dalili.

Hutun da ya d'aukar wa kan shi domin wannan binciken shi yasa ya fara zaman bakin gida yana watching gidan su Meenah da kyau da kyau, haka ma yana kula da shige da ficen duka mutan gidan da kuma wa'enda ke zuwa.

Yawan fita da Abrar keyi a koda yaushe tun baya kulawa har yazo ya fara saka mata ido, a kullum idan tazo fita yana bin ta da kallo, kawai abun da yasa beyi yunk'urin komai ba, be kawo komai a ran shi ba, kuma idan yaga fitar tata bata rage ko ta daina ba ya d'i barwa kanshi lokacin da ze fara aiwatar da binciken shi a kan ta.

AMMIE's POV.
Yau kam Ammie ciyon kai ya matsa mata, shine dalilin da ya hana ta saukowa breakfast, tayi tsammanin jin shigowa Meenah amma shiru, amma ta danganta hakan akan k'ila yau bacci take, domin ta na da tabbacin inda ta farka to babu shakka gurin ta zata fara zuwa.

Kiran wayar Meenah tayi but is not reachable.

Tana cikin wannan zancen zucin nata se ga sallamar Captain.

"Ammie an tashi lafia? Ya k'arfin jikin dafatar kin samu sauk'i?

"Lafiya" ta fad'a a tak'aice ta sha murr.

Ganin yayi shiru kuma ya sha jinin jikin shi yasa ta fara zargin shin ko dai tunanin da tayi d'azin gaskiya ne?

"Me kaje yi tin da duhun subahin a d'akin baby? Itace tambayar ba zata da ta watso mishi.

Zare ido yayi yana scratching  neck inshi..
"Ehh! Amm... dama...." haka dai ya dinga in inaa ba dan yasan takamamiyar amsar da ze bata ba.

"Je ka kiramun ita"

"Ammie, dama abun da yasa kika ga na je d'akin ta d'azun, kiranta na gani a waya na, ni kuma a lokacin da ta kirani ina sallah, so bayan na dawo ne se naje gurinta, na isketa tana sallah bayan ta kammala tace min da Allah tana son taje gida da safe, abunda yasa ta kirani domin ta gayamin saboda taga bakyajin dad'i kuma da safe take son zuwa, bata son ta tayar dake.
Shiyasa ta gayamin idan kika tashi se na gayamiki, to shine dalilin zuwa na acan d'in"

(Nace ahh su Captain an iya tsara labarin k'arya.)

D'an gajarta kallan shi Ammie tayi.
"Allah sarki ok to babu damuwa, dama abunda yasa na tambaye ka na d'auka wani problem ne shiyasa ka je can d'in"

Ammie ta fad'i haka ne saboda kada tilon d'an nata yayi wani tunani akan bata yarda da shi ba ko yayi irin tunanin da tayi.

Murmushi k'arfin hali Captain yayi.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now