Chapter 55

173 19 10
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 55.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Duk wanda ya kalli Meenah a karo na farko baze wanye ta ba, saboda tsananin canjawa da tayi, tayi bak'i tayi rama nesa ba kusa ba, duka tayi wani futu futu gwanin tausayi, Meenah y'ar gayu, y'ar wanka, amma kuzo kuga yanda takoma, ga tsananin yunwa da ta addabe ta, ga wata irin mumunnan rashin lafia dake k'ok'arin kama ta.

Da k'yar da taimakon Grandpa Meenah ke takawa saboda gwara shi ko ba komai zai fita jurewa saboda tsoho ne mai k'arfi kuma mai ran k'arfe.

Abinci da ruwa sune mahad'in rayuwa, duk wanda ya kasance cikin halin rashin su to tabbas ze shiga mawuyacin hali, musamman idan mutum ya saba yana rayuwar jin dad'i, a yau duniya ta juyawa su Meenah baya, da uwa da uba amma ba abunci ba ruwan sha, rayuwa suke amma basusan amfanin ta ba, inama inama! Kaico da wannan irin rayuwar garari da suke, a yau tsawon satin su d'aya kenan a wannan dajin, babu ci babu sha, idan da za'ayiwa Meenah tambaya akan jin dad'i zatace wallahi bata ta6a jin dad'in rayuwar duniya ba, zata iya cewa bata ta6a cin abinci a duniya ba, haka ma ruwa.

hmmmm!!! D'an adam kenan, haka Allah ke lamarin shi, a duk lokacin da ya so se ya juya al'amari babu wanda ya isa ya hana, ze jarabe ka a lokacin da yaga dama, haka ma ya yaye maka a lokacin da yaga dama, d'an adam mai manta kwanciyar hankalin shekara d'ari a lokacin da tashin hankalin kwana biyu ya same shi.

Dama haka rayuwa take, baze yu ace a kullum cikin jin dad'i da walwala kake ba, ya zama dole ubangiji ya jarabceka idan yaso a ko wane lokaci.

A duk yanayin da ka sami kan ka ya kamata mutum ya kasance mai yawan ambaton ubangiji haka ma mai yawan gode mishi.

Kana godewa Allah idan kana cikin walwala, cikin dukiya da nishad'i da farinciki, ba dabarar ka bace haka ma ba kai ka saka kan ka aciki ba, to dan me da bazaka godewa Allah ba idan ka tsinci kanka a kishiyar hakan?
Dabarar kan ka ne?
Babu!!
Ko d'aya ba haka bane.

Kada kayi tambaba kada kayi k'asa a gwuiwa a duk lokacin da ka tsinci kanka a cikin halin farinciki da kishiyar hakan ba tare da ka godewa mahaliccin ka ba.

A kowane yanayi Allah na iya jarabtar mutum, to saboda haka ya kamata ace mu kasance cikin godiyar Allah da kuma tawakkali a kan duk abunda yanayi yazo dashi, wata k'ila abunda kake gani ba komai ba kuma kayi godiya akan shi zai iya sanadiyar shigar ka aljannah, WA TU'U MINUL BIL K'ADAR KHAIRIHI WA SHARRIHI bima'an: muyi imani da k'addara mai kyau ko mara kyau yazo a acikin KITABU FIQH.
Wannan yana d'aya daga cikin alamomin masu imani. Allah yasa mu dace.

Meenah kam a cewar ta lokaci kawai take jira, wanda idan ka kalleta zaka iya yadda da hakan, amma abunda bata sani ba shine wuya bata kisa.

Wahala takai wahala se da ya zamto cewa ko yawu babu a bakin su, ga baki d'aya magudanar yawun su ta k'arangahe, sau dayawa suke tunanin kamar su tsinki hakukuwa suci ko dan su rage wani abu, amma inaa!! Bazasu iya ba saboda ba abincin da Allah ya halittah bane domin d'an Adam yaci.

A yau kam a yanda suke gani, yanayin ni'imar da ke cikin wannan safiya, yasa suke tunanin mafificin alkhairii, domin an tashi cikin ni'ima Alhamdulillah, gari yayi lillilliff gwanin sha'awa, babu hasken rana ko kad'an kuma su Meenah sun ga kamar sun fara futo wannan dajin, ganin suna ganin d'ai d'aikun uncompleted buildings can ba'a rasa ba, haka ma suna ganin y'an shaye shaye can ba'a rasa ba, amma kam wannan karon gabaki d'aya babu tsoro balle firgici akan idanun kowanen su, babu alamar rahama ko walwala a fuskar ko wanne daga cikin su, domin kuwa zuciyar su ta riga da ta bushe, abu d'aya suka sani shine RAYUWA KO MUTUWA, to tabbas kuwa d'aya ne ze kasance.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now