Chapter 44

207 21 10
                                    




🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 44.



*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️
Kayan ta ta kwasa bayan sun kammala shiryawa. Umarni Ammie ta bawa d'aya daga cikin guard in Captain akan yayi driving motar Meenah, mota d'aya suka shiga tare da d'aya a gaban su ta security ,se ta Meenah a baya making 3 cars kenan.
Bayan isowar su ne suka gaisa anan Meenah tace wa Mommah:
"Hmmm!! Nikam inaga Mommah kin fidda ni cikin iyalan gidannan, ace za'a kawo wa Adda na lefe amma sedai naji ga shanun tallah! Ta k'arasa tare da karya kai gefe kamar ta kwarai..
Dariya Mommah tayi;
"gani nayi idan kina gun Ammien ki bakya jin hass, kuma anan gida abubuwa sunyi yawa shiyasa ba'a gayamiki ba da zummar se a yau za'a gayamiki.

Dariya Ammie tayi tace; "hmm to Mman Maneer dame dame aka shirya ne na tarbon lefe?

"Ehh to dama yanzu zuwa anjima kad'an nakeso muyi doughnuts, chickens kuma se gobe da safe a soya, se alale da meat pie da qanin mahaifin ta ya d'auki nauyi, jalkar fura da gashashen rago kuwa dangi na zasu kawo, se drinks da already an siya sunanan aje"

"Yawwa to, kinga maganar doughnuts da zakuyi a yau a barshi, haka ma kajin a barshi duka na d'auki nauyi, yanzu zan bada order a Shanghai bakery akan suyi 200 doughnuts, 100 semosa, se na bada order paper chicken 100 guru a Mr Biggs."
Godiya Mommah tayi tace amma ai kamar kayan sunyi yawa, bakomai Ammie tace sedai fatar ayi lafia a gama lafia kuma ayi biki lafiya cikin k'oshin lafia.

"Ameen kowa yace suka cigaba da firar su ta yau da kullum.

Marece yayi har dare ya gabato, inda ba abunda Jauro ya saka acikin shi da sunan abinci, a yanzu ko da yaushe ya maida iccen mangon nan shine cin shi da shan shi, bayan ya dawo ne ya shige y'ar bukkar su zagayya ta ginin jar laka, wanda d'aki d'aya ne kuma ba wadatacce ba, ba komai a cikin d'akin se gadon kara guda biyu da fitilar shi acibalbal., Bukkar tasu zagaye take da ginin laka wanda duk ya b'urme, yaci ya zagwanye wanda ko wata muguwar banka kayi mishi ze iya rushe wa , a tsakar gidan kuwa can b'angare d'aya aka killace domin zagawa wato band'aki, anyi amfani da gadon kara da y'an tarkace kwanuka a kayi band'akin, wanda idan kana ciki kana wanka to ya zama dole ka zauna kayi domin idan ka mik'e tsaye to wanda ke waje ze iya ganin ka, wannan ne yasa suke da y'ar kujerar su ta tsuguno wacce suke amfani da ita gurin wanka. Azzikin da Allah yayi musu shine kawai rijiyar da suke da ita a tsakar gidan, se iccen durumi da ya wadace gidan da inuwa. Rataye jakarshi yayi, bayan yayi sallah ya kwanta.

Ammie bata bar gidan ba se da magriba tayi sosai kamun tayi musu sallama da sunan gobe da sassafe idan Allah ya yadda zata zo.

Captain kuwa se around 10:33pm suka dawo coz dama bada niyar kwana suka je ba.

********
Gida ya cika mak'il taro yayi taro kowa ka kalli fuskar shi agun cikin farin ciki da walwala se jiran y'an kawo lefe ake.

A b'angaren Miemie kuwa ta bar gidan tun safe taje nan gidan neighbours insu bada nisa ba.

Hakama Zeenatu da Abrar ba abunda suka fasa na akan abunda suke da k'udurin yi, sun shirya komai yanda ya kamata, fatan su d'aya shine tarko ya kama mujiya.

Zaune take cikin k'awayen ta se faman kekewa suke suna dariya, wayar tace ta d'auki ruri a karo na barkatai amma bataji ba saboda hayaniyar da ke akwai agun, duk rurin da wayar keyi akan idon Abrar wanda taji kamar ta sabatta ta akan rashin d'auka, lura da tayi cewa ba taga ana kiran nata ba ne yasa tace;

"Miemie, kamar ana kiran wayar ki ko?

Hakan yasa Miemie ta juyo ta d'auki wayar, ta d'aga kiran, batajin abunda ake fad'a a d'aya b'angaren hakan yasa ta mik'e tabar gun, wani k'ayataccen murmushi Abrar tayi da take gefe. Shiru shiru Miemie bata dawo ba hakan yasa Abrar mik'ewa tace bari taje gun y'an tarbon lefen.
Miemie kuwa futowa tayi inda ba hayaniya hakan yasa ta k'ara d'aga kiran da ke shigo wa, abunda taji ance shine;

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now