Chapter 36

303 23 8
                                    




🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
            By
🌹Teemahcutey 🌹

Page 36.

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

         *^*^*^*^*^*^*^*^*^*^*^*^*^*^
"Allhamdulillahi, jikin ta da sauk'i sosai, saboda ma a yanzu tana iya magana amma ba sosai ba".

"To masha Allah, Allhamdulillah, ai da'zu nayi waya da Alhaji uthsman in har ya shaida mun akan baya asibitin, da naso nazo tare da iyali na amma Allah bai nufa ba, Allah dai ya k'ara sauk'i, zan tafi amma ga wannan a bawa mara lafiyar"

K'in kar6a Mommah tayi ganin wannan kayan arzik'in da mak'ocin su ya kawo,

"Ahhh!!! Haba Haba Alaji hadda wata d'awainiya? To an gode Allah ya biya"
Sannan ta k'arba ta ajiye.

Tashi Mommah tayi bayan abokin Poppah kuma makwabcin su ya wuce, ta bawa Gwammah abinci domin a yanda jikin ta yake, da yar dar ubangiji za'a 'iya discharging nasu anytime.

           <><><><><><><><><>
"Na kasan ce firstborn a gidan mu, kuma inada 3 sisters and one brother" numfashi tajaa inda ta d'ora da cewa
" tunda aka sakani a gaba aka maido ni skt haka kawai aka rabani da friends ina da duka lovers ina na KD aka rabo ni da farin ciki na domin inada burin nayi service ina tare da k'awaye na, na tak'aice miki zancen kawai Allah ne ya nufi se na kammala digree ina da ba dan haka ba da tuni aka rabani da karatu na na dawo tsugune, wannan dalili na yankan k'auna da a ka mun, na dawo dani SKT bayan har ga Allah bana son zama anan na fison KD, yasa na k'udurci raba suma 'ya'yan nasu da duk abunda ze saka su cikin farin ciki, domin kuwa har ga Allah ina jin haushin yadda na dawo nake agolan ci agidan wasu, duda 'yan uwa nane na jini amma bana tunanin iya juriyar hakan.
Na d'aura d'amaran saka 'ya'yan su cikin masifa da k'unci kamar yadda suka sakani, ina rayuwa ta da bariki na cikin jin dad'di tare da wayayyun k'awaye na amma aka raboni da can.
Shiyasa da na rasa ta inda zan 6ullowa lamarin kawai se ga mafita na samu agun ki... ashe ba ni kad'ai nake farautar su ba."

Ta k'arasa zancen tana sakin murmushi ganin duka hankalin Zeenatu ya raja'a gunta tana sauraren ta, duk da tasan da cewa wannan zancen haka yake ba k'arya aciki kawai dai abu d'aya ta b'oye shine son da take yiwa Haidar in. Tasan da cewa idan ta gaya mata to fa plan inta ze lalace ga baki d'aya.

Jinjina kai Zeenatu " not bad, if I were you, i'll do the same. The problem is that ni basu cin amana ta ba, da sunyi kuskuren yin hakan, i won't hesitate to kill all of them"
Saurin dwad'e bakin ta tayi jin kalmar da ta fad'a daga k'arshe.

Killer smile Abrar tayi " poor girl, mye na rufe baki? Lmao!  Ai is nothing.. even me I can kill.... because na ta6a yin wani saurayi a KD a gaba na ya kashe wani a club saboda kawai yace yana sona, so ba abunda akayi saboda he's reach, everybody is afraid of him nd his father, m welling to kill anybody akan duk abunda ya giftomin a rayuwa wanda nake ganin ze iya zamar mun matsala....  i mean anybody, include my closet people" Shine abunda ta k'arasa fad'i ta tsare Zeenatu da manyan idanuwan ta.

"Hmmm hakan yana da kyau, ya kamata mu zage dantse dan ganin cikar burin mu, nima I'm capable of doing anything, I'm so much happy to have u as my acquaintances"

Daria Abrar tayi tace "most welcome sweetheart, our Errand will going to be unambiguously consummate, we will always count of each other"

Daria sukayi tare da tafawa. Anan suka bada order snacks suka d'an ci suna yi suna fira, atake wata yarda da juna ya shiga tsakakanin su. Nace hmmm Anya?

[][][][][][][][][][][][][][][]
Zaune take cikin gardiner ba abun da yake mata dad'i a rayuwa, abu d'aya tasani shine yanda rayuwar Captain ta canja lokaci d'aya akan Afrah domin kuwa da alama gani take kamar sun fara soyayya.
Tinani ta shiga yi akan wayar da ta ta6a jin Afrah nayi agun, aikuwa atake ta hasaso wani MUMMUNAN AL'AMARI na shirin faruwa, saboda itakam abu d'aya ta sani shine indai tana da rai da lafiya ba wanda ya isa ya cutatar da Ammie da Captain. Base an fad'a mata ba tariga tasan cewa Afrah na son Captain, wanda yasa take jin haushin ta saboda gani take kamar ko ita tana so nai, bayan ba haka bane ita bata ta6a jin tana son Captain ba sedai a matsayin yaya.
To a iya sanin ta ko ada, yanayin rawar k'afar Afrah da shishshigi shiyasa gabaki d'aya Captain baya ra'ayin ta, but now why the sudden change? Anya kuwa?? Ruwa baya tsami banza, abu d'aya nasani shine nasan duk wani abu da zatayi ya dinga rawar k'afa da ita be wuce SIHIRI, kuma da yaddar Allah ko ma menene se na gano, musamman da nasan cewa ba son tsakani da Allah take mishi ba duk yadda akayi.
Duk a cikin zuci Meenah ke wannan maganar.
Tana cikin zancen zucin nata kawai se taga Afrah kamar daga sama tsaye tsangam bisa kanta.

Abun Alfahari Na✅Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin