Chapter 13

255 22 0
                                    



🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
💐Teemahcutey💐



Page 13

Ah bangaren poppah kuwa suna mamakin irin juriya da dauriar mahaifiyarsu gwammah.
Domin kuwa duk irin bala'oanda suka faru ah wannan qarnin kama daga batan Meenah har sace gawar mijinta bata wani tada hankalin ta bah gwarama batan Meenah ta fi nuna damuwa dashi akan komai.

Poppah ne da Mommah zaune ah parlour suna kallan news ah Aljazeerah wayan poppah yay ringing dagawa yayi tare dakara wayar ah kunne.

Ya d'auki kusan minti Gomah yana wayar kamun daga bisani ya katse wayar.

Ahankali ya kalli mommah yace mata yanaganin cikin yan kwanakinnan tafiya xata kama shi zuwa abuja...

Tau tace tabishi da kyakyawar adua.

🏢🏢🏢🏢🏢🏢🏢🏢
Bayan yagama yimata bayani akan abunda ze kaisa se tajaa dogon numfashi tare da furzarwa, "Alal haqika son bawai bana son katafi wannan aikin bane, amma kawai inajin shakku idan zakuyi aiki akan ire iren waennan hamshaqan masu kudin, Amma ba komai addua tah takariya zata bika ah koh ina. Son. Akwai abunda yake damuna wlh akan mahaifinka" Ammie tace haka tare da kallan captain.
"Nima nima Ammie narasa gane kan mahaifina, ban san dalilinda yasa idan yana harkokin gabansa bah kwata kwata baya tunawa da iyalansa"
"kul son kada kaqara cewa haka Noo bawai baya kula da iyalansa bane kawai dai baicika son zama sokoto bah sedai Abuja"
to Ammie da yaddar Allah jibi idan zan wuce zan biya ta gurinshi,

Bayan sati daya.
Ayaune captain yake shirye shiryen tafiyarshi wanda xe fara zuwa Abuja Yh kwana biyu kamun ya wuce wanda yay daidai da poppah mah ayau ze wuce Ah Abujan shima.

Drivern su poppah bayannan though shi yasaba kaishi airport sannan yadawo da motar gida.

Har yacewa Mommah bari ya kira Omar ya kaishi se tace aa yau zasu raka ashi dagannan se tadawo da motar, to yacemata kamun yace su shirya domin jirgin 12:30 ne kuma yanxu pass 11.
********

Bacci takeyi sosai duk da bata saba irin wannan baccin bah tunda taxo gdan.
Ganin har 10 tawuce bata zo bah yasa Ammie yanke hukuncin xuwa dakinta.

Koh da taje seda tayi kusan 10mnt tana tadata Abun yabawa ammie mamaki.
Tashi tayi tana mutsutsuke ido....
Kallan Ammie tashigayi tana wani tunani, kanta taji ya sara se Ammie tace baby kitashi mana kinsan ayau yayanki xe wuce kuma yace xaki rakashi har Airport. Juyawa tayi bayan ta ajiye mata wata haddadiyar maroon jallabiya wacce jiyane wata qawarta ta kawomata su tare da perfumes tsara bane, amma rigar bata yiwa Ammie acewarta ta yarace.

Bayan Ammie tafita se Meenah ta tashi zaune tana safa da marwa...

Itadai ah iya saninta saceta akayi,
Amma taga alamar wa'ennan mutane sunada kirki. To ya akayi taxo nan din?????
Tinanin rayuwar da tayi ah gdan takeyi se taji kamar ba da gaske bane mafarki ne.

Wanka tayi ta shirya yaukam tayi fes domin hadda yar kwalliya tayi 🤣

(Topha kwalliya tadawo the real Meenah is back.)

Tunanin y'an gidan su ya fad'o mata arai zabura tayi ta miqe tafito ahankali tana sanda har takawo qofar fita daga bangaren Ammie se tayi Karo da captain, gabanta ne ya fadi tuno da rashin mutuncin da ta mishi lokacin da ya watsamata ruwan qazanta, cikin tane ya bada wani sound qululuuuuu.
Jaatayi gefe ta tsaya, kallan kallo suka shiga yi tsakanin su,  Captain yana mata kallan tayi kyaune sannan kuma kamar yana d'an son ya gano wani abu daga gareta domin ya ga yanayin yanda take kallan shi yaga ya sauya.

Ah bangaren Meenah kuwa tana jiran matakinda zaidauka ne akan rashin kunyarda tamishi wani sashe na zuciyanta kuwa yana tunamata da xamanda sukayi tare.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now