DUK NISAN DARE....

By HauwaAUsmanjiddarh

23.4K 1.6K 135

Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and last... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
41
42
43
44
45

40

542 40 5
By HauwaAUsmanjiddarh

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

4️⃣0️⃣

D'ogawa tayi daga jikinshi fuskarta cike taf da hawaye, cikin muryar kuka take yi musu godiya, wani d'an jarida yace " meye babban burinki a halin yanzu?

"Inga iyayena da 'yan uwana, na koma k'asata cikin dangina na bud'e ido na ganni a gidanmu.

"To yanzu ya batun soyayyar da kikeyiwa Marshall, d'an guntun murmushi tayi had'i da cewa " tananan a raina har abada, sai dai ta zama tarihi.

Zasu sake yi mata tambaya Barrister Shatima yajata suka bar wajen, a mota ma babu abinda takeyi sai faman kuka, gefen titi ya gangara yayi parking, ya zuba mata ido.

"Haba Maryama, to yanzu kukan na meye?

"Ai ba kuka ya kamata kiyi yanzu ba, kamata yayi ki godewa Allah kiyi farin ciki na samun freedom, hawayenta ta goge tana kallan Barrister Shatima tace " na daina, yayi murmushi had'i da cewa ko kefa! Mrs Marshall!
d'an guntun murmushi tayi batare datace komai ba.

Bayyi parking a ko'ina ba sai a harabar gidanshi, ya zagaya ya bud'ewa Maryama mota yace " fito!.

"Ina ne nan?

"Gidan Mania na dawo dake, ya fad'a cike da tsokana, gajeriyar dariya tayi batare datace komai ba ta fito, tana biye dashi a baya har suka shiga falon gidan,
Khadija na zaune a falo saman sofa tana kallan Aljazira tana sauraran labarai, duk abinda ke faruwa ta sani, tasan labarin Maryama tun daga farko har k'arshe duk da Shatima bai fad'a mata ba,
tana bibiyar labarin, dai-dai lokacin da suka shigo dai-dai lokacin aka haskosu rungume da juna a k'ofar kotu,
idon Khadija nakan tvn tana kallan abubuwan dake faruwa, saida yayi sallama tasan ya shigo dan bataji shigowarsu ba, da sauri ta mik'e ta taresu fuskarta d'auke da fara'a,
duk da taga Maryama rungume a k'irjin mijinta hakan bai hana ta karb'eta hannu bibbiyu ba kasancewarta mace me fahimta.

Hannayen Maryama ta rik'o ta zaunar da ita saman sofa fuskarta cike da annuri tace " wai! sannu kinji, kinsha gwagwarmayar rayuwa,
BS ya zauna idonshi kan Khadija deep down yanajin mugun tausayinta, dukda taga Maryama rungume a jikinshi amma ko'a fuskarta bata nuna ba,
" ki bata d'aki tayi wanka ta kwanta ta huta, Khadija taja hannun Maryama zuwa bedroom, " ki duba closet akwai kaya idan kinyi wanka ki canja, bari na nema miki abinci,
" nagode! kawai Maryama tace, Khadiya tayi murmushi batare datace komai ba ta fice, falon ta dawo ta sameshi zaune, bayan ta zauna ya kalleta sosai yace " zata d'an zauna anan tare damu kafin komai ya lafa.

"Bakomai, Allah ya bamu hak'uri da juna, bata sake magana ba ta mik'e ta shiga kitchen, duk yadda BS yaso ya karanci yanayin Khadija kasawa yayi,
Maryama tayi wanka ta wanke gashin kanta sosai, ta fito busar da gashinta da hand dryer,  ta shirya cikin atamfa riga da siket sunyi mata kyau sosai, ta tada sallah.

Shima d'akinshi ya wuce yayi wanka ya fito sanye da farar jallabiya, Khadija na shirya abinci a dinning table ya fito, " yau me aka dafa mana?

"Yau kam girkin ba naga bane na Maryama ne, waige-waige ya farayi yana cewa " ina Maryaman?

"Tunda ta shiga d'aki bata fito ba har yanzu, " bari na kirata, yace yana nufar d'akin jikinshi na rawa, tabi bayanshi da kallo batare datace komai ba, zaune ya sameta saman sallaya rik'e da Al Qur'ani tana karantawa,
ya zauna a bakin gado yana jiranta, ganin ya shigo yasata kai aya tare da rufe Qur'anin ta kalleshi fuskarta d'auke da murmushi. "food is ready! ke muke jira a dinning, batayi magana ba ta mik'e suka fita tare jikinta sanye da hijabi,
Khadija ta d'aga kai ta kallesu sun jeru sun nufo dinning d'in kamar couples, saurin d'auke idonta tayi daga kansu tana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un cikin ranta dan gudun kar shaid'an ya samu gurbi a zuciyarta.

Hanif da Hanifa yaran BS suka rugo da gudu suka fad'a jikin Daddynsu, ya rungume su, sai daga baya hankalinsu yakai kan Maryama "Daddy wacece wannan?

"Auntynku ce, yaran suka nufeta da murna, ta d'aga Hanifa sama tana dariya tace " ya sunanki?

"Hanifa, "kaifa?

"Hanif, yace yana dariya, cikin fara'a Khadija tace " tuwon shinkafa da miyar wake nayi miki, naji a labarinki kince kinasan tuwon shinkafa da miyar wake,
cike da farin ciki Maryama baki bud'e, tayi mata godiya sosai, tana kai lomar farko ta lumshe idonta had'i da cewa " uhmm masha Allah an dad'e ba'a had'u ba,
Hanif da Hanifa tana zuba mata surutu amma da im, um um take binsu, BS da Khadija nayi mata dariya, sosai taci tuwon ta k'oshi ta d'ora da fad'in " idan yayi saura a rage min shi zanci da daddare na d'umama da safe,
" keda abinki wazai hanaki?

"Zama ki samu, "yauwa Aunty Khadija nagode.

Sosai Maryama ta saba da Khadija da Hanif da Hanifa, musamman yaran  sunfi sabawa da ita, suna zamansu lafiya, sai d'an matsalolin BS dake damun Khadija dake nunawa Maryama wasu abubuwan a gabanta, ita kanta Maryaman tana jin kunyar Khadija idan yayi wasu abubuwan.

Marshall...

Kwance yake saman makeken ruwan swimming dake gefen gidanshi, idanuwanshi rufe, ba bacci yake ba, haka ba tunani yake ba,
yadai yi shiru ne kasancewarshi ba mai san yawan magana ba, bodyguard da ma'aikatanshi na tsaye gefe, wayarshi datayi k'ara yasashi bud'e manyan idanuwanshi dakyar badan yaso ba,
ya kalli inda wayar take, da sauri d'aya daga cikin ma'aikatanshi ya mik'a mishi, manager shine, saida ya d'an yatsina fuska kana yayi picking kiran,
"Okey, kawai yace a tak'aice, bai sake komawa ya kwanta ba, ya jirkice daga gadon ya fad'a cikin ruwan, yayi nutsu kana ya fito,
saurin mik'a mishi rigar wanka wani matashin bature yayi, ya amsa ya saka, ya sake mik'a mishi towel ya karb'a yabar wajen yana goge kanshi,
gaba d'aya suka biyo bayanshi ya d'aga musu hannu alamar su dakata, cak suka tsaya babu wanda ya sake motsi,
ya taka steps yayi k'asa ya b'ullo wani wawakeken falon da ya kusa girman filin ball, zaune ya iske manager shi yana kallan news a tv, kallo d'aya yayiwa Tvn ya kauda kai,
ya zauna a d'aya daga cikin kujerun falon had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallan manager shi batare dayayi magana ba.

Ganin gaba d'aya hankalin manager yana kan Tvn yasa Marshall sake kallan tvn a karo na biyu, hoton Maryama ya gani manne jikin allan tvn,
ya k'ura mata ido yana san tuno inda ya tab'a ganin fuskarta amma ya kasa, ya tabbatar da ya tab'a ganin fuskar dan bashi da mantuwa,
da yana da mantuna daya manta labarin mahaifinshi wanda yasashi tsanar mata dama soyayya gaba d'aya wanda shine dalilin dayasa har yanzu bayyi aure ba,
even budurwa bai tab'a yiba dan yayi believing no true & real love in this world, dan haka ba ruwanshi da mata balle aure, shidai yasha giya da koken yayi mankas shikenan buk'atarshi ta biya.

Saida ya jima yana tunani kana ya tuno inda ya santa itace wacce ta suma danya d'aga mata hannu, kanshi ya kawar ya mayar da kallanshi ga manager shi cikin turancinsu na turawa yace " an gama shirya komai ne?

"Eh! an gama kai kad'ai ake jira, bayyi magana ba ya mik'e yabar falon batare daya sake kallan tvn ba, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito cikin shirinshi tsaf,
wando ne 3 Quater a jikinshi da riga fara sai takalmi boot shima fari, manager shi ya mik'e suka fita tare, inda private jet d'inshi ya sauka nan cikin gidanshi ya nufa, suna shiga pilot ya lula dasu zuwa Qatar inda za'ayi world cup.

Waye Marshall...

An haifi Leo Marshall a America a North Carolina a shekarar 1995, tun yana d'an shekara 2 mahaifiyarshi Mia Loe ta mutu, mahaifinshi yaci gaba da kula dashi,
har yakai shekara 7 mahaifinshi bai sake yin wani auren ba, wata rana mahaifinshi da Marshall sun fita yawon shan iska ya had'u da Amelia,
tun daga nan soyayya me k'arfi ta shiga tsakaninsu, basu d'auki lokaci ba sukayi aure, abinda ya k'ara burge Leo yadda Amelia take san Marshall,
bayan anyi aure Marshall ya fara gane halin Amelia duk da a lokacin shekarunshi 8, ta rink'a azabtar dashi tana gana mishi azaba kala-kala,
amma a gaban idon Leo yadda kasan kwai haka take lallab'a Marshall, a hankali ta soma azabtar da Leo cikin ruwan sanyi batare daya sani ba, while tana cigaba da bawa Marshall bak'ar wahala, ta cireshi daga makarantar kud'i ta mayar dashi public school,
wuya kam ta duniya Marshall yashata a hannun Amelia, tana nunawa Leo mugun so da kulawa agaban kowa kamar gaske,
shiyasa Leo bai gano abinda Amelia keyiwa Marshall ba,   ta kware a bariki da munafurci dan bai isa ya gane ba, yadda Amelia ke nunawa mahaifinshi so, sosai yake bashi mamaki,
abun yana d'aure mishi kai, shi kanshi yasan Amelia tana san Leo, ya hak'ik'ance ya yarda, sai dai ya rasa dalilin dayasa bata sanshi, ya tsayar da tunaninshi akan kodan ba ita ta haifeshi ba, shi d'an kishiyarta ne shiyasa bata sanshi.

Bayan wani d'an lokaci Leo ya mutu, kuka kam gun Amelia kamar zata mutu dan sai da aka rufeta a d'aki, shi kanshi Marshall sai da ya tausaya mata, a lokacin yana da shekaru 10,
bayan mutuwar Leo da wata biyu ya shigo gidan yaji Amelia na hira da k'awarta, wai dama tun farko ba san Leo take ba, asalima bata tab'a sanshi ba, dan dukiyarshi ta aureshi dataga bazata ci ba shiyasa ta kasheshi,
yanzu kuma saura Marshall take jira ad'an lafa shima ta kasheshi ya zama dukiya gaba d'aya ta zama tata, sosai Marshall ya tsorata, bai shiga gidan ba ya fice yakai kanshi gidan marayu ya nuna ID Card d'in iyayanshi yace duk sun mutu sai da aka bincika aka tabbatar da mutuwarsu kana suka karb'i Marshall,
anan gidan marayu ya taso bashi da kowa a duniya, tun daga wannan abu da Amelia tayi ya tsani mata kuma ya sawa ranshi babu soyayyar gaskiya a duniya......


*JIDDARH....* ✍🏻

Continue Reading

You'll Also Like

3.1K 338 32
...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ษ—ansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this fairy tale of love,jealousy and ultimat...
23.8K 1.5K 23
*แ€กแ€ฌแ€ธแ€ธ!! แ€แ€„แ€นแ€™แ€บแ€ฌแ€ธแ€€แ€˜แ€ฌแ‚€แ€€แ€ฎแ€ธแ€œแ€ฒ" "แ€€แ€ญแ€ฏแ€šแ€นแ€€แ€œแ€ฌแ€ธแ‹ แ€กแ€ผแ€”แ€นแ€ธ แ€€แ€ญแ€ฏแ€šแ€นแ€€ แ€™แ€ฝแ€„แ€นแ€…แ€ฌ" ๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค
3.3K 430 11
They built their own dream to live together to their last breath. They promised to stay with eachother , stick with each other till the last day of l...
147K 2.3K 28
bl . Taekook ๐Ÿ”ž๐Ÿ”ฅ แž”แž˜แŸ’แžšแžถแž˜:แž€แŸ’แž˜แŸแž„แž€แŸ’แžšแŸ„แž˜18แž†แŸ’แž“แžถแŸ†๐Ÿ™ แžŸแžผแž˜แžขแž—แŸแž™แž‘แŸ„แžŸแžšแžถแž›แŸ‹แž–แžถแž€แŸ’แž™แž–แŸแž…แž“แŸแž˜แžทแž“แžŸแž˜แžšแž˜แŸ’แž™๐Ÿ™๐Ÿ”ฅ