21

440 36 2
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣1️⃣


Sai da suka tabbatar kaso 70 cikin fasinjojin motar sun mutu kana suka lafa da harbin, takowa suka farayi suna tunkaro motar,
Maryama da tun bud'e wutar farko ta fita daga hayyacinta, ta d'imauce, nutsuwarta ta barta, duk ilahirin jikinta ya d'auki kerrrrma, ji tayi sauran mutanen da suka rage na magana k'asa..

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yau rana ta b'aci mun fad'a hannun muggan 'YAN FASHIN BAK'IN DAJI.

Kallo d'aya zakayiwa wad'anda aka kira da 'yan fashi kasan babu d'igon imani ko tausayi a tattare dasu, da alama basu san me kalmar hak'uri, tausayi da imani take nufi ba...

Kwata-kwata babu d'igon hasken musulunci da annuri a saman fuskokinsu, mutane masu kama da aljanu ko ma ace shaid'anu, wanda ganinsu kad'ai kan zauta mutum ya rikid'e.

D'ago kan da zatayi jikinta na tsananta b'ari tayi ido biyu da d'aya daga cikinsu, duk jikinshi a shafe yake da bak'in shuni, idonshi kad'ai ne fari.

Tsananin tsoro da firgici yasa Maryama sulalewa k'asa sumammiya, dariya d'aya daga cikinsu ya saki me kama da kukan jaki had'i da haurinta da k'afa,
ganin bata motsa ba yasashi kallan d'aya daga cikin 'yan fashin yace "éloigne-la-moi de moi (d'auke min ita daga gabana).

Cikin rawar jiki yaron da aka umarta ya amsa da " alors (to), ya kinkimi Maryama ya sab'ata a kafad'a yayi cikin daji da ita,
kallan sauran mutanen dake cikin motar yayi wad'anda tuni wasu sun gama jik'a jikinsu da zawo, jikinsu sai rawa yake yana tsuma hak'oransu suna had'uwa kaf-kaf-kaf, kamar masu jin sanyi,
"sortir, (ku fito waje) yace yana dubansu, kafin ya gama rufe bakinshi sun mik'e suna rige-rigen fitowa,
jerasu yasa akayi kana ya kallesu d'aya bayan d'aya yace " Que pensez-vous de la France ? (Akwai me jin fransanci).

Shiru sukayi suna kallan kallo a junansu, wata mahaukaciyar tsawa ya daka musu yana sake maimaita tambayarsu " Que pensez-vous de la France ?
(Nace akwai me jin france?)

Da sauri wajen rabinsu suka amsa da "oui, murmushi yayi me kama da kuka na jin dad'in yadda jikinsu yake b'ari ga tsoranshi k'arara a saman fuskarsu.

"une personne est venue et a interprété pour ceux qui ne pouvaient pas entendre
(mutum d'aya ya fito ya fassarawa wad'anda basa ji)

Jikin d'aya daga cikinsu yana kerma ya fito wanda kallo d'aya zakayi mishi kasan buzu ne, d'an fashin yayi dariya had'i da cewa " Dis-leur que je connais tous leurs vêtements et leurs corps.

Mutumin ya juya ya kalli sauran mutanen cikin 'yar hausarshi ta buzayen Niger yace " mutunnan yace yana san kayanku kuma harna jikinku, dan haka ku cire kayan jikinku ku aje,
jikinsu na b'ari suka hau cire kayan jikinsu suna ajewa mazansu da matansu.

D'an fashin ya kuma cewa " et puis je connais la voiture avec tout son contenu donc tu dois en choisir une et tu entreras dans la forêt et finiras ton trajet à pied ou vais-je te l'écourter en te tuant ?

Jikin mutumin me fassara ne k'ara d'aukar tsuma tsoro da firgicinshi suka kuma nunkuwa suka fito k'arara harshenshi na hard'ewa yace " yace kuma sannan yana san motar da gaba d'aya kayan cikinta dan haka sai ku zab'a cikin biyu zaku shiga daji ku k'arasa tafiyarku a kafa ko kuma ya gajarce muku ita, ya hutashsheku ta hanyar kashe mu?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now