24

358 26 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣4️⃣


Sai da ta d'auki lokaci sannan a hankali ta kuma furta " na yarda zanyi fashi da makami tare daku...

Gaba d'aya suka saka dariya, Djeneba ya mik'e tsaye ya daki k'irjinshi da duka hannayenshi biyu yana ihuuu me rikitarwa ya fara yiwa kanshi kirari.

"Sai ni kuturwar uwa a zauna dani dan dole, kurman daji me wuyar fuskanta, dogo sa gabanka inda kake, bak'in daji na wuce ratse, dakalin majina ahauni a zame kududdufin barkono iyakacin mace gwiwa, daji ba'ayi maka kyaure sai  mahaukacin kafinta,
ruwan kogi nake da na wuce murfi, kowa yayi karo dani sayya fad'i, ihuuu ya kuma yi yaranshi ma suka fara ihuun, tsagaitawa sukayi da ihuuun Djeneba yayi gyaran murya ya kalleta yace.

"Muna da dokokinmu da sharadd'anmu, wanda idan kika sake kika karya koda d'aya daga cikinsu sakamakonki mutuwa,
doka ta farko ba'a guduwa, ba'a cin amana ko fitar da sirrin k'ungiya, bama munafurci ko nuna bambamcin yare da k'abila da addini, ba'a amfani da waya a mafakarmu dan ana iya bin diddiginmu,
sannan babu wanda yake amfani da sunanshi na ainahi.

"Duk cikinmu babu wanda yasan sunan wani na gaskiya, haka gari da yarenka babu wanda yasan komai akan kowa,
idan kika fitar da sirrinki wani ya sani ruwanki, abu na biyu kuma na k'arshe bama sanya mata a harkarmu,
kece mace ta farko data fara shigowa kungiya dan haka dole mu sauya miki kammani, shigarki, sunanki, daga mace zuwa na namiji.

"Aski....!

"Aski..shine farkon abinda zamu fara yi miki, sai a lokacin Maryama ta d'ago kanta ta kalle shi, kallo d'aya tayi mishi ta d'auke kanta dan bazata iya jure kallan mummunar fuskarshi ba,
tana ji tana gani aka aske mata gashin kanta da take yiwa mugun so kamar rai, Maryama irin matan nan ce masu gashi kuma masu san abunsu, zakaga dayawa mata masu gashi, gashin bai wani dame su ba,
amma banda Maryama dan sosai take san gashinta take kula dashi, had'i dayin gayu da abinta, kwal-kwal sukayi mata tasss k'ok'on kanta ya fito rantal, Djeneba yasa d'aya daga cikin yaranshi ya kwashe gashin yakai ya zubar.

"Daga yau sunanki *SEYDOU* ba ruwanmu da sanin tsohon sunanki, yaranki ko addiniki da k'abilarki balle kuma k'asarki....

Ya mayar da kallanshi ga Adaamah yace " abata kaya.

Jikin wanda aka kira na rawa ya durk'usa cikin girmamawa ya amsa da " to, kana yabar wajen, bai dad'e ba ya dawo hannunshi d'auke da bindiga, kwari da baka, da sark'ar harsashi da suke ratayawa a wuyansu, sai banten ganye da Bra ta ganye itama.

Kanshi k'asa ya rusuna gaban Djeneba ya mik'a mishi Djeneba ya amsa ya aje gefe kana ya d'auki Bante ya mik'ewa Maryama yana fad'in "saka.

Abun da bata san menene ba tabi da kallon rashin fahimta, ganin kallan da take yiwa Banten yasashi cewa " irin kayan jikinmu ne ki amsa ki saka a jikinshi, kayan jikinsu tabi da kallo da suke rabi tsirara wanda akayi su da ganyen wata bishiyar,
al'aurarsu kawai ganyen ya rufe shima ba sosai ba, taso tayi gardama amma sanin bak'ar wuyar da zata sha yasata amsa ta rik'e a hannunta tana fad'in " ban iya sawa ba...

"Cire kayanki na saka miki...

Djeneba ya fad'a babu wata alama a tattare dashi..

Da kallan mamaki ta kalleshi tace " na cire kayana fa kace?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now