34

454 49 7
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣4️⃣


D'aya daga cikin mutanen ne, ya k'araso gabanta ya tsaya hannunshi d'auke da d'an k'aramin kaskon zuba abinci, ya d'an jima yana kallanta ido cikin ido kafin ya k'arasa inda take,
ya durk'usa ya aje abincin a gefe kana ya kunceta, a galabaice ta zube k'asa tana numfarfashi, "ruwa..!

Kamar yaji abinda ta fad'a ya mik'a mata ruwa a k'ok'o hannunta na kakkarwa ta karb'i ruwan takai bakinta ta shanye tass, k'ok'on ta mik'a mishi ya amsa ya mik'a mata kaskon abincin ta warta da k'arfi har tana d'an kartar mishi hannu, ta soma ci hannu baka hannu kwarya kamar mahaukaciyar data shekara bata ci komai ba,
ya d'an kalleta kana ya juya yabar wajen bai dad'e ba ya dawo hannunshi d'auke da wani ruwan ya sake d'ebo mata,
duk yawan abincin ta cinyeshi tasss dan bata san adadin kwanakin datayi bataci ba, saboda batasan iya kwanakin datayi cikin ruwan tana yawo a sume kafin igiyar ta jawota ta kawo nan ba..

Kascon ya karb'a ya mik'a mata ruwan ta amsa ta shanye tas, a fili tace " Alhamdulillah! tsayawa yayi yana kallanta sosai.

"Nagode sosai!.

Tace tana kallanshi, bayyi magana ba bai kuma nuna alamun yaji abinda tace ba.

"Thank you.

Maryama ta sake fad'a dan a zatonta idan baya jin Hausa ai baya kasa jin turanci ba, still bai nuna alamun yaji abinda ta fad'a ba.

Saida ta juya manyan fararen idanuwanta masu kama da madara kana tace " shukran!

Still yana tsaye inda yake bai motsa ba.

"Merci..!

Ta fad'a da zaton yana jin France, zaman da tayi wajensu Djeneba da Gidan Mania ta koyi France, bayyi mata magana ba ya juya yabar wajen, tana k'ok'arin d'an kishingid'a tad'an runtsa ya dawo,
bayyi mata magana ba, ya kinkimeta ya mayar jikin bishiyar zai d'aureta, ganin yana shirin d'aureta yasa Maryama cewa " dan Allah ka barni nayi sallah.

Saurin cewa " je veux prier, danta lura kamar yana jin frence, bayyi mata magana ba ya saketa, da hannu yayi mata nuni dasu je, yana gaba tana binshi a baya har suka isa bakin wani d'an k'aramin ruwa,
ya juya baya, alamun ta kama ruwa idan tana da buk'ata, bayanshi ta kalla sosai ta tabbatar baya ganinta sannan ta tsugunna,
bayan ta gama ta koma gefe tayi alwala, kana ya dawo da ita, yana gefe yana jiranta tayi salloli kana ya d'aureta amma ba tamau ba, yayi mata sakwa-sakwa.

Ya juya zai tabar wajen ta bud'e baki cikin sanyinta tace " Merci..!

Ya juyo ya d'an kalleta kad'an kana yabar wajen, a haka a wahalce bacci marar dad'i ya d'auketa cike da mugayen mafarkai..

Washe gari ma babu wanda ya kalli inda take har rana ta fito tayi tsaye alamar azahar tayi, tana kallansu suna ta hidimominsu, wasu na kamun kifi wasu hawa bishiyoyi kome sukeyi akan bishiyoyin oho,

Ga mata da yaransu birjik, wasu na girki, wasu shara, wasu kula da yara kowa da abinda yake yi, babu wanda ya kula da ita, ita babbar damuwarta sallar da batayi ba, ko asuba batayi ba gashi yanzu da gani azahar tayi.

Yauma shi ya nufo ta hannunshi d'auke da abinci da ruwa, bai tsaya kamar jiya ba, yana zuwa ya kunceta ya bata abincin ta ci tasha ruwa.

"Je veux prier! (Zanyi sallah).

DUK NISAN DARE....Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu