20

489 39 2
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣0️⃣


Lab'ewa tayi saida aka shiga sallar ishaa bayan anyi sujada ta fice tana sauri, duk ilahirin jikinta na kerrrrma, harta d'anyi nisa ta tsaya had'i da juyowa ta zubawa gidan ido hawaye na bin fuskarta,
fuskarta ta rufe da nik'ab, ta tare me adai-daita sahu ta shige, "ina za'a kaiki Hajiya?

Me adai-daita sahun ya buk'ata "tashar Kano, ta bashi amsa tana sunkuyar da kanta k'asa, babu b'ata lokaci yaja adai-daitan.

Tana cikin adai-daita sahun tana lek'e-lek'e kamar wacce tayi kisan kai,  tayi sa'a suna zuwa mutum d'aya ake jira ta shiga ta zauna bayan ta sallami me adai-daita sahun, bata jima da shiga ba mota ta tashi zuwa Kanon dabo...

A cikin motar ta rubuta musu text

'''"Assalamu Alaikum ina me baku hak'uri idan har kun samo sak'ona, nayi-nayi na rarrashi zuciyata akan ta hak'ura da abinda Allah ya k'addara min na auren Yuraam amma na kasa dan haka na yanke hukuncin guduwa, na sani banyi dai-dai ba amma hakan shi nake ganin ya fiye min, kuyi hak'uri dan Allah ku yafe min ku tayani da addu'a nagode.'''
*Maryama Bukar Bugaje'.*

Tana tura musu sak'on ta cire layin ta yarr dashi ta windon motar dan tasan ana iyayin tresing layin.

Basu isa Kano ba sai k'arfe shida na safe, sallah ta fara yi tayi addu'o'i, sannan ta tambayi wata mata " dan Allah inace kasuwar 'yan gwal a Kano?

D'an jimm matar tayi kana tace kije kasuwar rimi ko saban gari saiki tambayi 'yan gwal, godiya tayiwa matar sosai kana ta hau napep ya kaita kasuwar saban gari, da sukaje kasuwar ba'a bud'e ba saida ta jira sosai mutane suka fara fitowa kana ta tambayi 'yan gwal har layin wani mutum ya kaita tayi mishi godiya kana ta shiga wani shago.

Bayan sun gaida ita ta bud'e jakar gwalagwalanta tayi musu talla, muguwar tsorata sukayi suka shiga kallan kallo a tsakaninsu, babban cikinsu ne ya kalleta yace " muna zuwa bari muyi shawara, suka fita kamar bazasu dawo ba sai gasu.

"Na waye wad'annan gwala-gwalan?

Ya tambayeta, "nawa ne mana, kallanta yayi sosai kana yace " ina rasidinsu?

Dubawa tayi cikin jakar ta zaro ta basu, ya duba sosai yaga original receipt ne, ya kuma dubanta yace " ya sunanki?

Ya tambayeta dukda yaga sunan a jikin receipt d'in,  kanta tsaye tace " Maryama Bukar Bugaje,
sunan Bukar Bugaje ba b'oyayye bane a cikin Nigeria,
yasan sunan sosai, dan haka yad'anyi tantama, jinjina kanshi yayi yace " please ko zaki bani tambaci akan abinda kika fad'a?

ATM Cards d'in da National ID Card d'inta ta nuna mishi, ya karb'a yana dubawa yace " meyasa zaki saidasu?

"Saboda nawa ne kuma ina buk'atar kud'i shiyasa, ta fad'a a d'an zafafe, " am kiyi hak'uri Hajiya kin san yanayin abunne yanzu dole saida taka tsan-tsan saboda kaucewa matsala kiyi hak'uri.

Dayake mutumin nada tsoran Allah yasa yasiya ya bata kud'inta cif bai cuceta ko sisi ba, ya tura mata kud'in ta accout duk da taso ya bata cash dan tana tsoran kada su rufe mata account, dubu d'ari biyar ya bata cash ta zuba su cikin trolley tayi musu sallama ta fice.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now