4

608 41 6
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


*ZAFAFA BIYAR (5)*
*ZAZZAFAR TAFIYA...*

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261



4️⃣


Kasa kwanciya yayi dole tasashi mik'ewa tsaye jiri ya d'ebeshi yayi saurin dafe bango dan karya zube a k'asa, gaba d'aya duniyar ta fice mishi a rai,
ya daina jin dad'in komai kwata-kwata, "Maryama nada aure...!, ya fad'a cikin sanyin murya yana dafe k'irjinshi dake barazanar tarwatsewa.

"Na shiga uk... , saurin yin shiru yayi, deep down yana mamakin kanshi.

Da sauri ya isa gaban mudubi ya tsaya tare da zubawa kanshi ido yana kallan kanshi yace " meke shirin faruwa dani ne?

"Badai san Maryama nak...

Kanshi ya shiga girgizawa yana ja da baya had'i da fad'in " a'a kai haba, yama za'ayi haka ta faru..?

"Meye damuwata dan tana da aure..?

Da k'arfi k'irjinshi yayi muguwar bugawa, maganganun Khadija ne suka fad'o mishi a ranshi.

"Ya Allah kada ka jarrabe ni da abinda bazan iya ba.

"Allah kada ka d'ora min abinda bazan iya d'auka da jureshi ba.

"Ka tausaya min Ubangiji, Allah na tuba ka yafe min, ya fad'a cikin raunanniyar murya yana k'ok'arin mayar da hawayen dake shirin zubo mishi,
cikin sanyin jiki ya koma kan bed ya matsa can k'uryar gadon ya rakub'e.

Bai tab'a ganin nisan dare a rayuwarshi irin wannan daren ba, daren yayi mishi tsayi sosai kamar daren mutuwarshi, ya k'agu gari ya waye, Allah Allah yake gari ya waye yaji gundarin labarinta, yaji shin da gaske tana da aure ko shaci fad'i ne irin mutane?

Cikin ranshi ya tsinci kanshi da addu'ar Allah yasa bata da auren, Allah yasa ba gaskiya bane.

Wata zuciyar tace " to kai ina ruwanka da aurenta?

"Daga ganin mace kawai ka d'orawa kanka damuwa akanta, ka hana kanka da zuciyarka sakewa, batare daka san girman laifin data aikata ba,
ka sani ma ko *FUSKA BIYU GARETA* kasan fa mutum abun tsoro ne, musamman 'ya mace tana iya rikid'ewa ta koma duk yadda taso a yayinda taso dan haka kabi a hankali.

Kamar yana magana da mutum ya girgiza kanshi tare da fad'in " Maryama batayi kama da irin wad'annan mutanen ba, batayi kama da wacce zata cutar ba,
siffatarta bata azzalumai bace, ina da yak'ini akanta,
Zuciyarshi tace " ta ina ka samu yak'ini akanta?

"Mace shu'uma ce tana iya canjawa aduk lokacin data so, ko Khadija tana iya shayar dakai gidauniyar mamaki balle wacce ka tsinta ka kuma san ance tsintacciya mage bata mage,
hannuwanshi ya sanya ya toshe kunnuwanshi yana fad'in " a'a bana son ji, amma still zuciyar shi tak'i  daina yi mishi maganar.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now