2

920 55 11
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣


Jikinshi har rawa yake saboda sauri, duk bayan minti d'aya sayya duba agogon dake d'aure hannunshi yaja tsoki saboda lokacin rufe ziyara ya kusa......!
da sauri yayi parking a parking space ya fito gudu-gudu yake tafiya har yana tuntub'e, "excuse me Sir,
yaji an fad'a lokacin dayake k'ok'arin shigewa ciki        batare daya tsaya neman izinin shiga ko sign  in kamar yadda dokar Prison din ta tanadar ba,
" where are you heading to...?

Baturen ya fad'a yana kallan Barrister Shatima, " I'm sorry, I want to talk to my client,
" who is she?

Dabarbarcewa Barrister Shatima yayi saboda bai ma san wacece itaba balle yasan sunanta, a halin dole saika fad'i sunan wanda kazo gani ka kuma rubuta a rubuce,
ID Card Barrister Shatima ya fiddo cikin Aljihunshi ya nunawa Baturen Police d'in yana fad'in " like you don't recognize me...!,

" I Barrister Shatima.... kafin ya k'arasa maganar Baturen Police d'in ya tare shi da cewa " even if you are president, I will not allow you to enter, until you follow our rules,
I knew, you know the rules, so please obey the rules, ya k'arasa maganar yana had'e mishi hannuwanshi had'i da rusunawa alamar girmamawa,
dole tasa Barrister Shatima ya juya badan ya so ba, dan yasan idan zai kwana anan yana begging babu wanda zai kalleshi,
gashi ba irin k'asarmu bace balle yayi tunanin bada *CIN HANCI* anan k'asar koda wasa kayi tunanin bada *CIN HANCI* koda akan rashin sani ne sai kayi gidan yari na wata uku,
jiki a sanyaye ya shiga motarshi ya dafe kanshi, ya rasa dalilin dayasa yake jin yarinyar a ranshi, ya rasa me yasa ta tsaya mishi cikin kanshi,
ya rasa dalilin dayasa ya nace sayya ji labarinta da *SILAR ZUWANTA GIDAN YARI...* a k'asar daba tata ba,
a hankali ya d'ago jajayen idanuwanshi da suka gama rinewa ya kalli agogo, dogon tsoki yaja mtswwwww, yasan ranar yau kam ta wuce shi,
dole duk abinda zayyi sai yakai gobe, mafita d'aya ke gare shi, itace court Order,  ita kad'ai ce zata iya bashi damar ganin yarinyar,
itama court order sai idan yasan sunanta da k'asarta da yarenta da kuma addininta dole da wad'annan abubuwan zai cike foam kafin ya samu damar samun file d'in da zai bashi damar ganinta,
ya zurma cikin tunanin mafita k'arar wayarshi ya cika mishi kunne saida yayi tsaki kafin yayi picking wayar bakinshi d'auke da sallama,
"Okey.... kawai yace yayi dropping call d'in had'i da yiwa motar key yabar harabar Prison d'in.

A gidanshi ma sama-sama sukayi hira suka ci abinci ya shige d'aki ya rufe dan karma a shigo a dame shi, matarshi tasan halin kayanta sarai, haka yake yi idan case yasha mishi kai, dan haka ta bashi abinda yake buk'ata wato kad'aici,
in banda kai komo babu abinda yake cikin d'akin, "why na damu kaina akanta...?

"Meyasa gaba d'aya na kasa samun sukuni da walwala akanta?

"Wai meke shirin faruwa dani ne....?

"Ya Allah....

Ya fad'a yana dafe kanshi while yana zama bakin gado, cikin sakin jiki ya jingina bayanshi da fuskar gadon, yana tunanin ta yadda zai samu damar shiga Prison gobe koya samu sanin abinda yake buk'ata wanda zai cike foam, ya samu damar ganinta kai tsaye,
guntun murmushi yayi yana shafa kanshi, lokacin da dabara ta fad'o mishi, cikin farin cikin ya samu mafita bacci me dad'i yayi awon gaba dashi,
bai farka ba, sai asuba yayi sallah ya maida kai, bai tashi ba sai 8:30am na safe a gurguje ya watsa ruwa, ya fice, babu inda ya tsaya sai a Prison,
ya fad'a musu yazo ganin Yuk ne, yayi sign in ya shiga, fakaitar idon 'yan sandan yayi ya rab'a ta wajenta kamar zai wuce, yayi sa'a yau bata sallah ko addu'a,
sai dai bakinta na motsi da alama lazimi take.

Sallama yayi mata ta amsa mishi batare data dago kanta ta kalleshi ba, dan girman Allah zanyi miki wasu tambayoyi ki bani amsarsu a gurguje dan bani da enough time yau,
cikin nutsuwa ta d'ago kanta ta zuba mishi kyawawan idanuwanta farare tass kamar takarda, da k'arfi k'irjinshi ya buga, yaji wani abu dabai tab'a jinshi a iya tsayin rayuwarshi ba,
ya tsarga mishi tun daga babban d'an yatsan k'afarshi har tsakiyar kanshi, kwat yawu ya wuce mishi ba shiri batare daya sani ba,
d'auke idanuwanta tayi daga kanshi, sai da ya tattaro d'an k'arfin halin daya rage mishi kafin yace " kin.... ji..... me.... nac.. e....?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now