19

428 29 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*Masu tambayata shin DUK NISAN DARE...! na kud'i ne ko kuwa? A'a bana kud'i bane free Novel ne*


1️⃣9️⃣


"Ku tashi kuje..! Cewar Abba yana k'ok'arin mik'ewa, cikin matsanancin kuka ta soma magana..

"Bana sanshi Abba, tun farko sai da nak'i amincewa da aurenshi amma aka matsamin gashi nan yana neman wargaza min rayuwata.

"Ko sau d'aya a cikinku dana ce bazan aureshi ba akwai wanda ya tambayeni dalili?

"Akwai wanda ya tambayeni shin zanyi rayuwar farin ciki dashi ko bazanyi ba?

"Akwai  wanda ya tab'a tambayata wacce rayuwa nake yi bayan auren?

"Abba bayan ka bani sati d'aya nayi shawara ka sake kira na kaji ta baki na ko kaji ra'ayi na da hukuncin dana yanke?

"Abba wanne irin mijine zai tafi kallan ball ranar da akai mishi amarya baibi takanta ba?

"Shi wannan abinda yayi min so ne?

"Ku tambayeshi shi yana so na?

"Ku tambayi shi da ball da matarka wanne yafi?

"Haka nayi rayuwar kad'aici a gidan har tsayin wata guda, dolece ta saka ni fara kallan ball.

"A ranar da akaini saboda yunwa kasa bacci nayi Abba.

"Wallahi shima baya so na, shima ba sona yake ba, akwai dalilinshi na aure na ku tambayeshi Abba.

"Ku tausaya min ku tausayawa rayuwata wallahi bazan tab'a yin rayuwar farin ciki dashi ba,
bazan tab'a farin ciki da auren nan ba, haka zan k'are kamar a keji Abba dan Allah ku raba aurenmu kar na fad'a halaka.

"Kada na saida duniya da lahirata Abba please ku taimaka min, ta k'arashe maganar cikin rikitaccen kuka mai k'ona zuciya.

Tsit d'akin taron yayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan Maryama, Abba zayyi magana mahaifinsu Bugaje Zanna yayi saurin dakatar dashi had'i dayin gyaran murya yace ..

"Dukkaninsu masu laifi ne, haka acikin maganganun Maryama akwai na dubawa, musamman datace kadata fad'a halaka, dan haka ina ganin a raba auren zuwa nan da d'an wani lokaci,
idan sun dai-daita kansu haka muka fi so, idan kuma Allah yayi hukuncinshi sai dai mu tayasu da addu'a.

Tsit d'akin ya kumayi na d'an wani lokaci kana Abba ya sake kallan Maryama yace " kije kiyi tunani da addu'a zuwa nan da kwana biyu, muga abinda Allah zayyi.

"A'a Abba na gama duk tunani da addu'ar da zanyi, dan Allah ni dai Abba...!

Shiru tayi ta kasa k'arasa fad'ar abinda tayi niyya, " kin tabbatar da hukuncin da kika yankewa kanki?

Abba ya sake tambayarta a karo na biyu, kanta tayi saurin d'agawa alamar eh, Bugaje Zanna ya mayar da dubanshi Yuraam dake jin kamar yayi hauka yace " kayi hak'uri Yuraam ka sawwak'e mata saki d'aya muga abinda Allah zayyi.

Kanshi ya shiga girgiza hawaye na zubowa daga idonshi yace " a'a dan Allah kar'a rabamu muna san junanmu, ina santa Abba nasan itama tana so na b'acin raine kawai.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now