18

386 22 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


1️⃣8️⃣


Jin Umma ta rantse yasashi tsayawa cak bai k'ara binsu ko yayi magana ba, kallan kinga abunda kika jawo yayi mata, har suka shige part d'in Umma...

Iska ya nausa yana fad'in " oh! Sheet!

Babban abunda ya dameshi family meeting d'in da Umma tace za'ayi akanshi a kuma bincike shi, tashin hankalinshi d'aya kada suyi mishi mummunan zato ko wata fassarar ta daban.

Ga tozarcin da za'ayi mishi gaban kowa, kila ma wasu su fara tunanin ko baida lafiya, saurin komawa cikin gidan yayi ya canja kaya had'i da fitowa yama rasa meye abinyi ya rasa mafita gaba d'aya kanshi ya kulle.

Part d'inta Umma takai Maryama tana ta faman bambami.

"Dan zalunci da bak'ar mugunta a aura maka yarinya amma ka kasa tab'a ta shege sakarai kawai.

"Kema da laifinki munafuka ke me miji shine kika rufa mishi asiri maimakon ki sanar ayi bincike in lafiya ce baida ita a sani tun wuri a nemar mishi magani, haka idan wani abun nema a binciko gaskiya.

"Zauna nan bari naje na fad'awa Abbanku shi zai san abunyi.

Hannunta Maryama ta kama cikin sanyi da nutsuwa har lokacin bata bar kukan ba tace " please Umma karki fad'awa Abba maganar dan Allah bana san a shirya mu.

Cikin rashin fahimta Umma ta jiyo tana fad'in " me kike nufi Maryama?

"Kodai tsiyar daga wajenki take?

"Dama naga alamar kamar ke kika hanashi kanki, Maryama zatayi magana Umma ta katseta da cewa " kinga fad'a min gaskiya ke kika k'i bashi had'in kai?

Tsoron abinda zaije ya dawo yasa Maryama duk'ar da kanta k'asa batare datace komai ba.

"Koma dai meye ku kuka sani idan iyayanku maza suka ji sa tsananta bincike akanku.

Fita tayi ta nufi part d'in Abba ta iskeshi zaune a falo Mama na kusa dashi, gefenshi daga d'aya b'angaren ta zauna had'i da sauke ajiyar zuciya.

"Lafiya dai Amarya ran gida?

Abba ya fad'a cikin barkonci.

"Ina fa amarya yara na neman saka min ciwon kai, gyara zama Abba yayi yana fuskantarta sosai yace " wanne yara?

"Maryama da Yuraam mana!.

"Me sukayi miki?

"Wai ashe kana ji Alhaji tunda akayi auren basu tab'a had'a shinfid'a ba.

"What!?

"Me..!? Cewar Abba, Mama ta kalli Umma tace " au dama ba ciki ne da ita ba?

"Ta ina za'a samu cikin Falmata?

"Babu fa abinda ya tab'a shiga tsakaninsu ko d'aki d'aya basu tab'a kwana ba.!

jinjina kai Mama tayi tace "Kai haba zancensu ne wannan yama za'ayi hakan ta faru..!?

"Impossible! Abba yace yana d'orawa da " wata bakwai fa kenan da auren.!

"Kallanta ya tsaya yana yi duk wannan watannin ko me?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now