37

433 41 8
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣7️⃣

Ajiyar zuciya ta sauke babu d'igon tsoro a tattare da ita kwata-kwata, yadda kasan ba a cikin tarko take ba.

"Wannan karon ko cikin wacce irin masifa na fad'a oho?

Tayi maganar cike da k'osawa, bata jima ba ta fara jiyo taku kamar na mutane yana nufota, sai dai takun yafi na mutane k'arfi,
tananan d'aure tana lilo jikin bishiya tana jiran ikon Allah ya sauka akanta mutanen suka iso,
kallo ta d'auko tun daga k'afafuwansu har kansu, tab! tace a fiki batare data sani ba, bakinta bud'e cike da matsanancin mamakin girman mutanen tace " bana kuma nan muka fad'o..!?

Wasu irin k'attin mutane ne jibga-jibga suffarsu irin ta mutane amma sunfi mutane girma nesa ba kusa ba, dan duk mutum d'aya nasu ya kai girman mutum uku kamar mu,
yadda kasan samudawa, kamar 'yar tsako d'aya daga cikinsu ya sab'ata a kafad'arshi sukayi cikin  daji da ita,
saman dutse suka hau saida suka kai har k'ololuwar dutsen, acan duniyarsu take, ba laifi grain nasu nada d'an girma,
gaba d'aya garin irinsu d'aya, ai suna ganin Maryama suka rink'a tasowa suna kallanta, wasu na dilalan yawu, ba'a ajeta a ko'ina ba sai a fadar sarkin garin,
saurin mik'ewa yayi ya sauko daga kan karagar mulkinshi yana kallanta, tsinkakken yawu irin na kwad'ayin nan ya zubo daga bakinshi,
ya d'aga kanshi ya kalli wad'anda suka kawo ta, ya dafa kafad'ar d'aya daga cikinsu ya jinjina musu, cikin wani irin yare me kama da zarwance yace " kunyi babban k'ok'ari da kuka samomin abin kalaci,
raban danaci naman mutum harna manta, zan biyaku da tagomashi me gwab'i, sukayi ihuuu, d'aya cikinsu yace " nidai ina san kason idonta da b'argonta,
sarkin nasu ya turb'une fuska tare da cewa " ai ka kwashe dabgen dad'in, yo wanda yaci ido da b'argo ai shiya sha damge, sam bazaka samu ba,
ya koma kan karagar mulkinshi ya zauna tare da bada umarnin akai Maryama mayanka, batare da b'ata lokaci ba d'aya daga cikinsu ya sureta ya fita da ita,
baiji abinda sarkinsu yace sosai ba, sayyaji kamar yace akaita madafa, dan haka yakaita madafa, ya damk'ata a hannun wanda keyiwa sarki girki, ya k'ara da " ka dafata, ta dahu luguf,
hannu yakai ya wafce Maryama daga hannun wanda ya kawota yana dariya had'i da dilalan yawu danya san shima yau zaisha dabge, ko romo yasha ina laifi,
wanda ya kawo Maryama ya rik'e hannun wancen yayi k'asa-k'asa da murya yace " kada ka manta dani, me madafa yace "karka damu.

Nan da nan ya tashi girki, ya had'a komai cikin babbar tukunya yadda kassan mutane goma za'a dafa ba mutum d'aya ba, ya d'auko Maryama ya cire mata kayan cikinta tsaf ya dannata cikin tunkunyar,
sai lokacin Maryama ta fahimci hannun masu cin naman mutane ta fad'o,
yasa k'aton ludayi ya juya sosai kana ya d'ebo ruwan ya d'and'ana yaji komai yaji, ya d'ago ta cikin ludayin ta sauke ajiyar zuciya da k'arfi dan yadda kasan a teku aka jefata ba'a tukunya ba,
yakai hannu ya tab'a nononta ji yake kamar ya cisgesu ya danna a baki ya cinye, a ranshi ya aiyana yau kam koda sarki zai gane sayya saci nononta d'aya yaci,
mayar da ita cikin tukunyar yayi ya rufe tukunyar ruf da k'aton murfi, ya had'a wuta ya fita, cikin sa'a Maryama dake yawo cikin ruwa tana kokawa da numfashinta ta damk'i wani abu dabatasan komeye ba tahau ta zauna,
a hankali tukunyar ta soma d'aukar zafi, ruwan ma ya fara zafi, tashin hankali wanda ba'a saka maka rana, numfashinta ya soma k'ok'arin d'aukewa saboda zafi da rashin iska.

Sosai take kokawa da numfashinta ga matsanancin zafin daya fara yiwa tukunyar da ruwan yawa, ta tabbatar idan batayi da gaske ba,
tana iya mutuwa, kuka ta saki me cin rai da tab'a zuciya had'i da d'aga hannayenta sama ta soma addu'a.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now