36

457 42 8
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣6️⃣

Gaba d'aya wajen babu wata halitta sai birarruka, k'anana da manya sun cika wajen mak'il, sun wuce tunanin me karatu, kwakwalwar Maryama birkicewa tayi,
kanta ya juye ta kasa fahimtar komai, babu abinda ke motsi a jikinta, wani abu take ji yana shigarta tun data tafin k'afarta har tsakiyar kanta,
k'irjinta ya rink'a bud'ewa da zafi yayinda zuciyarta ke tsalle tamkar zata fasa k'irjinta ta fito, jinta take tana yawo a saman iska,
kamar wacce aka d'aure a jikin bishiya haka take jinta tana reto, idan ka tsaga jikinta bazaga jini ba, takai mak'ura a kid'ima da tsorata,
yadda kasan wacce ake bugawa gangi haka jikinta ke tsuma yana rawa, tana daga tsayen take kokawa da numfashinta dake barazanar barin gangar jikinta,
babu yadda batayi ta saita numfashinta ba amma ta kasa, hancinta ya toshe dud'um babu ta inda iska zata shiga, a haka a tsayen ta suma batare data fad'i ba.

Taf taf taf takun babbansu ya cika wajen, birarrukan suka rink'a darewa suna bashi hanya harya iso tsakiyarsu gaban Maryama,
tab! yadda kasan d'an k'aramin gidan bene haka girmanshi yake, yafi duk birarrukan girma, k'aton gaske ne, na gaban kwatance, ga muni ba kyan gani, ya iso gabanta ya tsaya, Maryama ta koma kamar d'an tsako a gabanshi,
kallo ya k'are mata sosai kana ya d'anyi gurnani, gurnanin dayayi ne ya farkar da Maryama daga suman datayi, tana farkawa tayi arba dashi gaf da ita,
sai a lokacin suman gaske yazo mata, danji kake timmm ta yanke jiki ta fad'i k'asa tana kaf-kaf-kaf da idanuwa kamar wacce aka yanka.

Tamkar 'yar tsana ya sureta da hannunshi yabar filin da ita, k'atuwar fada ya shiga gwaggwanin birurruka suka bishi d'uuuu ya aje Maryama a k'asa, ya taka ya zauna kan karagar mulkinshi,
ihuuuuu yayi me k'arfi wanda yasa gaba d'aya ginin soma girgiza k'asa ta fara zubowa, yadda kasan rugugin ruwan sama,
a d'imauce ta farka tayi zumbur ta mik'e tana rarraba ido, gaba d'aya a birkice take,
'yar k'aramar kwakwalwarta ta juye tana neman tarwatsewa, rasa abinda zatayi yasata fashewa da rikitaccen kuka harda ihuuu...

Ido shugaban gwaggwan birin ya lumshe yana sauraran kukanta, har cikin ranshi yake jin dad'in sauraron sautin kukanta sosai,
ji yake kamar tana rera mishi wak'a, tayi me isarta ta gaji tayi shiru, jin tayi shiru yasashi bud'e jajayen idanuwanshi masu kama da garwashi ya zuba matasu,
fitsarin da bata san tana ji ba ta saki, ya matsa daf da ita ya daka mata tsawa had'i da yin gurnanin, tsananin kad'uwar datayi yasata tsayawa cak had'i da zuba mishi ido.

Hargagin ya sake yi mata amma tsoro ya hanata yin ko gezau, d'an kallanta yayi cike da mamaki kana yakai d'an yatsanshi ya d'an dungureta,
tayi baya ta fad'i ashe a sume take a tsayen numfashinta ya dad'e da d'aukewa, d'aya daga cikin birarrukan yayiwa gurnani,
yayi saurin barin wajen bai dad'e ba ya dawo tare da wata mata tsohuwa wacce shekarunta zasukayi sittin 60yrs,
Babbansu ya kalleta ya kalli Maryama yayi mata gurnani, abun mamaki da al'ajabi ta gane abinda yake nufi,
ta nufi inda Maryama take tayi mata kallan tsanaki sarai tasan duk inda ta fito 'yar africa ce musamman kalar fatarta da gashin kanta,
komawa tayi ta d'ebo ruwa ta dawo ta yayyafawa Maryama, a fili ta sauke ajiyar zuciya me radad'i had'i da fitar da numfashi me nauyi.

Kuka ta sake fashewa dashi harda kuruwa tana shura k'afa, " na shiga uku, na jefo kaina cikin masifa, wannan wacce irin k'addara ce?

"Allah na tuba ka yafe min, Astagfirullah Astagfirullah, Allah na tuba ka yafe min, na gaji, na gaji wallahi, na gwammaci mutuwa, daga wannan tashin hankali, sai wannan masifar, kana fita daga wannan ka fad'a wannan?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now