3

763 49 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*ZAFAFA BIYAR (5)*
*ZAZZAFAR TAFIYA...*

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261

3️⃣


Wayar ya shiga juyawa tunaninnika na cika mishi kanshi, a hankali ya sauke ajiyar zuciya had'i da zubawa hotunan Maryama ido,
bai san yadda akayi bacci yayi awon gaba dashi ba, sai jin kiraye-kirayen sallar asuba yayi, da d'an hamzarinshi ya mik'e ya shiga toilet ya d'auro alwala ya fita zuwa masallaci,
sallar kawai yake yi amma can k'asan zuciyarshi tunanin Maryama ya hanashi sakat,
ko a office ma dakyar ya iya saita kanshi ya d'an tab'a aiki, ya kasa aiwatar da komai, duk abinda yake yi yarinyar na manne cikin zuciyarshi,
b'as-b'as da hannu Barrister Ezreal yayi a fuskar Barrister Shatima, yayi firgigit ya farka yana fitar da numfashi.

"What is going on?

"Are you normal?

Barrister Ezreal ya fad'a yana zama kan d'aya daga cikin kujerun office d'in idonshi kan Barrister Shatima, d'an gajeren murmushi Barrister Shatima yayi had'i da basar da maganar,
"Lafiya lau.

"Amma kake irin wannan zurfaffan tunanin?

"Kai ne ya d'auki caji, kasan yayin aikinmu ga cases sunyi min yawa na rasa yadda zanyi.

"Kaji manya, agogo sarkin aiki, kadai rinka samawa kanka sauki, ina dalili kaje ka kashe kanka a banza.

"Hmmmmm toya zamuyi da hakkin Al Umma dake kanmu?

"Kaga ai dole mu sauke shi, Barrister Shatima ya fad'a cikin murmushi yana samun sauk'in abinda yake ji a zuciyarshi,
sun dad'e suna magana kan cases d'in da suke yi kafin kowa ya tafi gida.

Da fara'arshi ya shiga gida ya zauna cikin iyalanshi, sukayi hira sosai suka ci abinci tare, dakanshi ya koya musu assignment, bayan yaran sunyi bacci a jikinshi, Khadija ta mik'e cikin nutsuwa ta d'auki Hanif ta nufi d'akin yaran dashi,
cike da tausayawa yabi bayanta da kallo, ta kwantar da dashi akan gadonshi ta shafo funkarshi tana murmushi ta tofa mishi addu'a Barrister Shatima ya shigo d'auke da Hanifa a hannunshi ya kwantar da ita, ya tofa mata addu'a, ya kashe musu fitilar dak'in, yabar musu dump light.

Suna zuwa tsakiyar falo ta kalleshi fuskarta manne da sassanyan murmushi me b'oye abinda ke zuciyarta tace " sai da safe k'aunata, ta fad'a cikin sanyinta tana k'ok'arin barin falon,
ya fahimci tana cikin damuwa sosai, saboda rashin bata kulawa da bayayi cikin kwana biyun nan, yasan tana da hak'uri kuma tana hak'uri da yanayin zamansu wasu lokutan,
dan lokuta da dama idan kanshi ya d'au zafi kan shari'a sayyayi sati bai sata a idonshi ba, kuma yana gidan tana gidan itama.

Jawota yayi ya rungumeta ta baya ya kewayo da hannunshi saman cikinta ya d'ora hab'arshi saman kafad'arta, muryarshi can k'asan mak'oshi yace " kiyi hak'uri Abin So na,
Siraran hawaye ne suka zubo saman fuskarta dukda tana iya k'ok'arinta wajen danne abinda ke taso mata.

"Kiyi hak'uri dan Allah, na sani bana kyautawa lokuta da dama, yayi maganar yana goga kumatunshi a gefen fuskarta.

"Na sani nima bana kyautata miki, ya fad'a yana juyo da ita, suka fuskanci juna, hawayen daya gani yana bin kumatunta yasashi zaro ido waje, "bun har ya kai haka Abin So na?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now