42

497 40 11
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


4️⃣2️⃣

Tun kan Marshall ya sauka yasa aka binciko mishi komai akan Barrister Shatima, dan haka jirginshi nayin landing a k'asar London ya shige d'aya daga cikin jerin motocinshi,
direct office d'in Barrister Shatima ya nufa, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya isa kan lokaci.

"Kayi tuk'i da sauri.

Ya fad'awa drivenshi, tun kafin motar ta gama tsayawa ya fito, securities d'inshi na biye dashi, mutane na binshi d'uuu sai d'aukarshi akeyi a hoto,
Barrister na zaune saman kujera a office d'inshi ya kifa kanshi saman table hannunshi rik'e da takardar da Maryama ta bari abun duniya ya isheshi,
yana ji aka bud'e k'ofar office d'inshi aka shigo amma bai d'ago ba dan a zatonshi sakatariyarshi ce.

"Hello please are you Barrister Shatima?

Marshall ya fad'a cikin nutsuwa, a hankali Barrister Shatima ya d'ago kanshi, ganin Marshall tsaye gabanshi yasashi saurin murza idanuwanshi had'i da mik'ewa tsaye,
dan yayi zaton gizo yake yi mishi, " ba mafarki kakeyi ba nine dai.

Marshall yayi maganar yana zama kan d'aya daga cikin kujerun dake fuskantar Barrister Shatima, komawa yayi ya zauna idonshi kan Marshall,
ya kasa yarda wai shahararran d'an kwallan k'afan nanne a office d'inshi yau.

"Naga duk abinda ya faru a media, please kozan iya samun k'arin bayani daga gareka?

Nannauyan numfashi ya fitar kana ya soma bawa  Marshall labarin tun daga ranar daya fara ganinta zuwa yau.

"What..!?

"Kace tabar gidanka yau?

"Ina ta tafi to?

Marshall ya fad'a cikin tashin hankali.

Barrister Shatima yace "Wallahi ban sani ba, shirun nan dakaga nayi na tunanin ta inda zan fara nemanta ne.

"Tashi muje muyi checking streets camera na unguwarku.

Ba musu Barrister Shatima ya mik'e suka fita shida Marshall, direct unguwarsu Barrister Shatima suka nufa Marshall da kanshi ya fito yana yawo a titi yana dudduba camera d'in kafin suka koma mota suka wuce security room,
inda zasu duba videos d'in camera, babu b'ata lokoci aka nuna musu, data fito daga gidan Barrister Shatima saida ta d'anyi tafiyar k'afa kafin tahau taxi,
basu ji abinda tacewa me taxin ba suka ga ta bud'e ta shiga, jikin Marshall na rawa yace " yi min zooming number motan, ba musu akayi mishi, ya d'aga wayarshi ya kira waya.

"Na turo maka hotan wata number mota ina san a kawo min motar dame motar yanzu.

Hannunshi d'aya cikin sumar kanshi yana yamutsawa while d'aya hannun ya rik'e k'ugunshi sai kaiwa da komowa yakeyi, duk bayan wani lokaci sayya duba wayarshi,
idon Barrister Shatima kanshi yana juya abun cikin ranshi, lalle duk duniya babu abinda yafi soyayya k'arfi,
yabar buga wasan world cup, ya fito yana yawo a titi yana neman mace, macen ma bak'ar mace 'yar Nigeria.

Duk sunyi shiru suna jiran tsammani wayar Marshall ta soma rori, saida wayar ta kusa sub'ucewa daga hannunshi saboda rawar jikin ya d'aga,
" yallab'ai gamu a waje.

Bayyi magana ba ya fita waje, suka bi bayanshi, jikin d'an tasin sai rawa yake yi, d'an kallanshi Marshall yayi kafin ya nuna mishi hotan Maryama yace " kasan wannan?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now