44

559 47 3
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


4️⃣4️⃣

Babu wanda ya iya kwakkwaran motsi, ko magana gaba d'ayansu ido suka zuba mata, har lokacin babu wanda ya kula da Marshall balle sauran mutanen,
d'aya daga cikinsu ne ya ruga cikin gida da gudu yana kwala fad'in " kowa ya fito ga Maryama ta dawo, Umma na zaune kan sallaya tana jan carbi ta jiyo ana kwala Maryama ta dawo,
jikinta na wata irin rawa ta mik'e ta fita,
Mama da sauran matan ma duk suka fito suka nufi get da gudu.

Da gudu Maryama ta nufi Abba ta rungumeshi tana sakin kuka me cin rai, wani abu daya tokare mishi mak'ogwaro shekara da shekaru yaji ya wuce, ya rungumeta sosai hawaye na gangaro mishi,
Mama na zuwa ta fad'a jikin Abba da Maryama bata damu da akwai mutane a wajen ba, ta saki kukan da uwace kad'ai zata fahimci irinshi.

"Maryama! Umma ta furda muryarta kunshe da abubuwa da dama, takai hannu ta jawota daga jikin Mama da Abba ta kifa mata mari kowa yayi tsit,
tasa hannu ta jawo Maryama ta fad'a jikinta suka durk'ushe a k'asa kowannensu ya saki kuka.

"Meyasa Maryama?

"Meyasa kika tafi kika barmu batare da kinyi la'akari da halin da zamu shigaba?

Umma tayi maganar muryarta d'auke da nauyi, deep down tana jin nauyin daya danne mata k'irjinta yana washewa, " kuyi hak'uri Umma, k'addara ce, babu yadda zamuyi da hukuncin Allah,
haka Allah ya tsara babu yadda zamuyi mu sauya, kuyi hak'uri ku yafe min, duk da nasan hak'uri yayi kad'an ya goge taban dana bar muku a zuciyoyinku.

Marshall tsaye yayi had'i da kafesu da ido yana mamakin son da akeyiwa Maryama a zuri'arsu, amma saboda shi ta tsallake kowa shiko dame zai biya yarinyar nan?

Bayan an natsa an gama rungume-rungume da koke-koke idon Yuraam ya sauka akan Marshall saida ya murza idonshi ya sake kallanshi,
a hankali ya nufi Marshall yakai hannu ya tab'ashi danya tabbatar, wani irin ihuuu Yuraam yayi had'i da buga tsallake yana fad'in " unbelievable Leo Marshall a gidanmu?

Sai a lokacin hankalin kowa yakai kan mutanen, Yuraam kusan haukacewa yayi ya rasa inda zai saka ranshi, ya tabbatarwa kanshi Maryama tayi mishi nisan nisa na har abada.

A babban falon gidan aka hallara manyan nakan sofa yayinda yara na k'asan kafet, Yuraam na kusa da Marshall,
tuni Marshall ya fahimci Yuraam shine Yuraam na labarin Maryama, bayan an nutsa aka bud'e taro da addu'a, Maryama ta nefi yafiyar iyayenta suka yafe mata Abba ya d'ora da fad'in " ba ke kad'ai keda laifi ba, har muma muna da laifi Maryama,
mu muka assasa tafiyarki, dan in banda na matsa miki kan auren yuraam da baki bar gida ba, nima me laifi ne ina da saka hannu aduk abinda ya samu rayuwarki,
ki yafe min Maryama, Abba ya k'arasa maganar kuka na kufce mishi.

"Bakayi min komai ba Abba, idan ma kayi min na yafe maka, Allah ya yafe mana gaba d'aya, kowa ya amsa da Amin,
kan Yuraam k'asa yace " kiyi hak'uri  da abubuwan da suka faru Maryama, nine babban me laifi dana matsa kan maganar aurenmu,
kuma na farfad'a miki bak'ak'en maganganun da su sukayi sanadin barinki gida, kiyi hak'uri, murmushi tayi dashi kad'ai ya fahimci ma'anarshi
idonta kan Marshall tace "bakomai, aini taimakona kayi tunda gashi na cika burina na samun cikon muradina, ai Allah ne meyi, kuma ma wayasan gobe in ba Allah ba?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now