27

382 30 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣7️⃣


D'an guntun murmushi Djeneba yayi yace " eh! shed'anci ne yasani barin addinina, addinin gidanmu na koma wani addinin.

Murmushi Maryama tayi tace " wato idan Allah yana nufinka da alkhairi sayya jarrabeka, jarabawa ba alamace ta rashin nasara ba,
kanshi ya d'aga har lokacin yana zubar da hawaye, Maryama ta rarrasheshi kana ta musuluntar dashi, a daren kafin gari ya waye ta koya mishi abubuwa masu matuk'ar fahimmanci cikin addini ta d'ora da fad'in.

"Kada ka sake kayi wasa da sallah koda wasa, ko a cikin wanne hali ka tsinci kanka da rayuwarka, ba lallai saikayi alwala ba, kana daga zaune kayi ta koyaya ne, yinta yafi rashin yinta alkhairi,
yayi mata godiya sosai.

*MOROCCO..*

Cikin babbar kasuwar garin suka zarce kowa ya kasa hajarshi, akaita siyan bayi, wani mutum da kallo d'aya zakayi mishi kasan baida d'igon imani ko kad'an ya sayi Djeneba,
tun daga kasuwar yake ingiza k'eyar Djeneba da mangari, ya juyo ya kalli Maryama hawaye na gangaro mishi, itama hawayen take zubarwa abin tausayi kamar sunyi zaman mutunci,
shiyasa akace sabo turken wawa, kunga dai kwata-kwata ba zaman dad'i tsakanin Djeneba da Maryama amma saboda sabo harda kuka da zasu rabu...

Satinsu d'aya a Morocco suka saida bayinsu tass banda Maryama ita kad'ai tai kwantai, babbansu ko sai fad'a yake yi mata harda duka,
wayya gaji da ci da ita, daga yanzu duk sanda zai bata abinci sayya nad'a mata duka.

Duk wani aiki na bauta da wahala ya dawo kan Maryama har kiwon dabbobinsu da yi musu wanka ita keyi, ta share turken dabbobi,
duk da haka idan zai bata abinci ko ruwa sai jikinta ya gaya mata dan saitaci uban duka kafin ya bata d'igon ruwa...

Da asuba sukayi shiri suka cigaba da tafiya, kasancewar Maryama ce kad'ai baiwar data rage yasa ba'a d'ora mata mangala a wuya ba,
sai dai sun d'aureta da sark'a k'afa da hannu, sosai ta jigata dan ko hanya bata gani sosai, yunwa da k'ishi sun had'u sunyi mata katutu, tafiya kawai take batare data san inda take jefa k'afarta ba tana tafe tana tangad'i kamar zata kifa, idanuwanta a lumshe,
suna bodar dake tsakanin Morocco da Algeria ta kifa k'asa, tsaki babbansu yayi kana cikin fad'a yayi magana da yarensu,
d'aya daga cikin yaran ya zare bulala yayi ta zubawa Maryama danta tashi amma a banza ko idonta bata iya motsawa balle tayi k'ok'arin tashi..

Yaran ya kalli shugabansu cikin yarensu yace " inaga ta mutu ba, ko tana gaf da mutuwa idan aka cigaba da dukanta zata mutu..

Sakkowa yayi daga kan rak'uminshi ya tako zuwa kanta yasa k'afa ya shure ta yana fad'in " tashi.. da yarensu, amma kwata-kwata babu alamar akwai rai a tattare da ita, k'ugunshi ya kama had'i da yin kakin majina ya tofa mata yace " la'ananniyar banza.

Ya juya ga yaranshi ya basu umarnin su yada zango anan, ba musu suka yada zango, har dare tana nan kwance inda ta fad'i, mataimakin shugabansu ya iso wajen ya d'aga butar giya ya tuttule mata a fuskarta,
nannauyan ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi, idonta ta soma bud'ewa a hankali duhun dare da kuma daji ne ya hanata fuskantar komai,
jikinta a mace ta tashi zaune tana bin ko'ina da kallo, ganinshi tsaye kanta yasata saurin yunk'urawa zata mik'e,
da hannu yayi mata alamar karta tashi ta cigaba da zama, ya juya ya tafi, bai jima da tafiya ba saiga d'aya daga cikin yaransu ya dawo d'auke da gurasa da dabino da ruwa ya kawo mata, hannunta na rawa ta amsa.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now