43

557 37 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


4️⃣3️⃣

Jikinshi na rawa da kerrrma gami da tsuma ya d'auketa cak ya nufi mota da ita, bai damu da yadda take cikin datti da daud'a ba, sai tashin wari take tana d'oyi kamar ayi amai,
direct asibiti yakaita ganin wanda ya kawota yasa jikin nurses da doctors na rawa suka karb'eta aka shigar da ita emergency,
sintiri ya shigayi a k'ofar emergency room d'in ya kasa zauna ko tsaye ya rasa inda zai saka ranshi yaji dad'i, ba'a fito da Maryama daga Emergency room ba sai wajen asuba,
aka fito da ita kan gadon marasa lafiya ana turata, d'aki suka kaita had'i da juna mata k'arin ruwa, sun canja mata kayan jikinta zuwa na asibitin masu kalar light blue,
cikin nutsuwa ya tako ya iso bakin gadon had'i da zubawa kyakkyawar fuskarta ido,
tayi fayau da ita, fuskarta ta d'anyi haske sai rama data d'anyi, baccinta take yi cikin nutsuwa sai sauke ajiyar zuciya take yi,
ya juya zai fita yajiyo muryarta can k'asan mak'oshi tana fad'in " Marshall..! Marshall..

Siririn murmushi yayi had'i da shafa fuskarta yayi mata light kiss a goshi ya fice.

Bata farka ba sai can da yamma, a hankali ta bud'e idonta ta saukesu akan Barrister Shatima dake zaune gefenta, cikin nutsuwa ta yunk'ura ta mik'e,
idonta cike da mamakin ganinshi tayi murmushi tare da cewa " dama kai ne?

"Dawa kike tsammanin gani?

"D'an shiru tayi tana tunani kafin tayi saurin cewa " naga Marshall.

"Na ganshi da ido na, tayi maganar cikin zumud'i, shiru tayi had'i da marairaice fuska tace " kodan nasan ma mafarki ne,
a markin fa wai har ya d'auke ni,  murmushi Barrister Shatima yace " ba mafarki kikayi ba.

Cikin rashin fahimta tace " kamar ya?

Bai bata amsa ba illa murmushi daya sakar mata yana danne wani abu cikin ranshi ya kalli k'ofa, k'ofar itama ta kalla zuciyarta na wani irin mugun bugu da tsananin k'arfi,
a hankali ya turo k'afar ya shigo kyakkyawar fuskarshi d'auke da dogon murmushi, sai da numfashin Maryama ya nemi d'aukewa,
dakyar ta iya saita numfashinta gami da k'ok'arin mik'ewa, tana fad'in " gizo yake min ko?

"Ka ganshi wai ya shigo har yana yi min murmushi, yana nufo ni, kana ganinshi?

Tayi maganar out of control had'i da runtse idanuwanta da k'arfi tana cewa " kace mishi ya daina yi min gizo, ya daina wasa da zuciyata,
a hankali yakai hannunshi ya shafo fuskarta ya d'an ja hancinta,
idanuwanta ta bud'e kamar munafuka, ganinshi gaf da ita yasata zaro idanuwanta kamar zasu fad'o k'asa saboda tsoro da zallar firgici,
sama da k'asa numfashinta ya somayi kamar me asthma, yayi saurin rik'eta, ayya da Marshall yasan abinda zai faru da bayyi gangancin tab'a Maryama ba.

Zubewa tayi a sume, idan hankalin Marshall in yayi dubu ya tashi, jikinshi ya shiga b'ari yana tsuma, Barrister ya bud'e fridge ya d'auko robar ruwa ya b'alle bakinta ya zuma mata,
ajiyar zuciya ta sauke a fili tare da bud'e idonta.

Karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna, numfashinta ne ya soma k'ok'arin sake d'aukewa Marshall yayi saurin had'e bakinsu, wani abu Barrister Shatima yaji ya daki zuciyarshi da k'arfi,
murmushi ya saki had'i da mik'ewa ya fita daga d'akin gaba d'aya, sai da ya tsotsi bakinta san ranshi kana ya cire bakinshi daga nata ya zuba mata ido,
ido cikin ido suke kallan juna sun dad'e a haka kafin ta kawar da kanta gefe tana fitar da numfashi da sauri da sauri, cikin sanyinshi ya mik'e tsaye tare da ita a jikinshi ya kwantar da ita saman gadon.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now