25

385 23 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

2️⃣5️⃣

Hannun Maryama na kakkarwa ta d'ebi abincin takai bakinta cike da bak'in cikin karya azuminta data d'auka aka sata ta karya ta tauna ta had'iye,
ido suka zuba mata gaba d'ayansu na wajen minti biyu kana Djeneba ya bada umarnin kowa yaci, mik'ewa tayi tabar wajen ta koma can gefe ta zauna,
yanayi ta kalla ta tabbatar yanzu sha biyu na rana tayi amma shegen yasata karya azuminta.

Tun daga wannan rana Maryama ta zama 'yar aikin 'yan fashi, basa fita fashe da ita, tana zaune a bukka tare da mutum d'aya da aka aje dan gadinta,
ita keyi musu komai na bauta, shara, wanke-wanke, girki, goge bindigoginsu da wuk'ak'ensu, d'ebo ruwa duk ita keyi, Allah ya sani Maryama ta dad'e tana neman hanyar guduwa,
amma ta rasa wannan mutumin da aka lak'aba mata duk inda take yana biye da ita shine ya hanata samun damar guduwa,
amma tasha k'ok'arin guduwar, haka Djeneba yana yawan yi mata kashedin karta sake tayi tunanin guduwa dan shi kanshi bai san kalasar azabar dazai gana mata ba,
dajin nan gidanshi ne duk inda ta shiga a cikinshi sayya naimota, basu tab'a k'ok'arin hanata yin addininta ba, dan yawancinsu kowa addininshi daban awajen..

Tana zaune tana wanke-wanke, d'an satar kallan Youf me gadinta tayi ya kishingid'a yana gyangyad'i kawar da kanta tayi gabanta yana fad'uwa,
harta gama wanke-wanken gabanta yana fad'uwa, tanayi tana satar kallanshi, kanta gama wanke-wanken bacci me nauyi yayi awon gaba dashi,
lallab'awa tayi taje kanshi tayi mishi kallan k'urulla harda kad'a mishi hannunta a fuskarshi danta tabbatar da baccin yake yi kokuwa...

Cikin sa'a baiko motsa ba, while gabanta na tsananta fad'uwa, da wani irin mugun gudu tayi baya-baya kana ta juya ta shiga cikin dajin sahara tayi ta runtuma guda..

Youf ya tashi zaune yana sakin murmushi had'i da bin bayanta da kallo yana dariyar mugunta dan yasan yau kashinta ya bushe, dama ba baccin yake ba, duk abinda takeyi yana kallanta, ya gwada tane ya gani...

Mik'ewa yayi ya kakkab'e jikinshi yabi bayanta da gudu shima, bisa mamakin Youf baigo hango inda Maryama tayi ba, balle yasan inda ta nufa, hankalinshi inyayi dubu ya tashi,
duk ilahirin jikinshi rawa yake yana kerrrma had'i da tsuma, zuciyarshi ko kamar zata fasa k'irjinshi ta fito saboda yadda take bugawa fat-fat-fat da tsananin k'arfi,
yasan muddin bai nemo Maryama ba mutuwarshi tazo sai dai idan shima ya gudun danya tsira da rayuwarshi, yana gudu had'i da runtuma mata kira gumi na d'iga tsabar tashin hankali,
tsaye yayi hannunshi d'aya a k'ugunshi yayinda d'aya hannun yana saman kanshi sai juyi yake a tsakiyar sahara ya rasa inda zai nufa,
dishi-dishi ya hango kamar mutum d'auke da mutum a kafad'arshi ya nufo shi, a hankali ya fahimci abinda ke nufo shi, Djeneba ne d'auke da Maryama a kafad'arshi,
jikin Youf har rawa yake yana tsuma ya nufi Djeneba da sauri ya tare shi, hannu ya mik'a da nufin karb'ar Maryama daga hannunshi,
cikin matsanancin b'acin rai ya kutufeshi da iya k'arfinshi, saida Youf ya juya yayi katantanwa kana ya kifa, take bakinshi da hancinshi suka fashe...

"Ku d'auko min wulak'antaccen..!

Djeneba ya fad'awa yaran batare daya kallesu ba..

Wani irin mugun wurgi yayi da Maryama k'asa, in banda akan yashin Sahara ta fad'a da taji jiki, d'aya daga cikin yaranshi ya kalla batare dayace komai ba,
jikinshi na rawa yayi saurin nufar inda yake ya duk'a Djeneba ya hau gadon bayanshi ya zauna daram kamar ya samu kujera,
wuyanta ya shak'o ya mik'e tsaye da ita a hannunshi k'afafuwanta na wutsil-wutsil idanuwanta duka sun fito waje jajir dasu, gumi da hawaye had'i da majina sunyiwa fuskarta kace-kace.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now