28

391 24 1
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣8️⃣


Matar da aka aika a kirawo tare suka dawo da 'yar aiken, kallo d'aya zakayi mata kasan kwankwararriyar 'yar duniya ce, hancinta duka side biyun a huje,
hujin kunne kam bazasu 'irgu ba, ga zuben k'afa da sark'ar k'afa.

"Nini..

Mania ta kira sunan matar, kana ta d'ora da " ga sabuwar kyankyasa nan, a bata hora me kyau, Nini ta kalli Maryama tana murmushi tace " ah kice duniya tayi saban tunbud'i?

Kafin Hajiya Mania tayi magana wani D'an Daudu yayi caraf ya amshe da "ke wannan 'ya! meya kaiki barin gaban tsaffi?

"Hala ce miki akayi jeki kya gani, in ba haka ba, babu abunda zai had'aki damu?

"TANGARAN...! Mania ta fad'a cikin k'osawa, ya karya k'ugu yace " siyan me kasada, kana ya d'ora da  " kinga ni taimakeni na tsaida ruwan miya..!

Ta gane abinda yake nufi amma tai kamar bata fahimce shi ba, tasan kud'i yake san ta bashi...

Nini ta tauna cingam k'as-k'as tace " kaidai hannunka bai cud'i bayinka ba wallahi.

"Ke kinga ni bana san habaice-habaicen nan naku na 'yan bariki, dan haka ki kama kanki, Nini zatayi magana Mania ta d'aga mata hannu had'i da cewa " jeki abinki.

Nini ta kalli Maryama tace " muje, batare datayi magana ba tabi bayan Nini,
Tangaran yabi bayansu da kallo yana fad'in "an tafi zunkwi-zunkwi ance da makaho bi nan, ya k'arashe maganar had'i da yin k'as da cingam d'in bakinshi,...

Batabi ta kanshi ba, dan tasan halin Tangaran ba gajiya yake ba, sai su kwana sunayi, suka bi ta wata 'yar k'ofa suka fita wani babban fili,
lalle gidan Mania babban gida ne, dan yakai girman wani d'an k'aramin k'auyen,
yaran mata da zagada-zagadan 'yan mata birjik kowacce na harkar gabanta, wasu sun ci kwalliya kamar zasuje wajen gasar zab'ar sarauniyar kyau.

D'aya daga cikin  b'angaren gidan suka shiga, babban falo ne me d'auke da manyan d'akuna, komai a tsare cikin tsafta da gayu tsaf-tsaf...

Maryama ta duk'a zata zauna Nini ta daka mata tsawa " dalla tashi, ke bakiga yadda kike bane  jiki duk k'azanta da tsami?

Kallan tiles d'in da tayi niyyar zama aka daka mata tsawa tayi, ko tiles d'in d'akin me gadin gidansu bai kai ba,
band'aki ta shiga ta had'a mata ruwan wanka, kana ta dawo falon ta kalli Maryama tace " muje ko?

Zungwi-zungwi tabi bayan Nini har band'aki, " cire kayanki ki shiga cikin nan, d'an jimm Maryama tayi tana  kallan Nini, " nace ki cire kayanki ki shiga, ta fad'a a tsawace, bakin Maryama na rawa muryarta na sark'ewa tace " in cire kayana a gabanki...?

Dariya Nini ta saka harda tafa hannu tace " aci ba'a siyar ba kwai yafi doki yarinya, kuma ko ina kwak'ular mata na rasa wacce zan haik'ewa sai ke?

"Ai ko dana wulak'anta wallahi, Maryama zatayi magana Nini ta zazzaro ido waje kamar zasu zazzago k'asa dama gata da manyan ido, cikin k'ubula ta finciko Maryama ta fincike kayan jikinta ta zuba a shara,
ta dannata cikin ruwan wanka data had'a, Nini takai kusan awa d'aya tana yiwa Maryama wanka da wankin kai da k'afa saida taga ta rage kusan kaso 60 na dattin dake jikin Maryama kana ta hak'ura,
Maryama na d'aure da towel tana biye da Nini, wani tangamemen d'akin kwalliya suka shiga, Tangaran na zaune yana ta faman shafe-shafe da goge-goge yaci uban jan janbaki, yayiwa Nini kallo d'aya ya watsar had'i da tab'e baki yace " can dasu gada zomo yaji kid'an mafarauta,
dariya Nini tayi tace " dad'in abun babu yadda gara zatayi da dutse sai dai ta lasa ta guiguya tabarshi wallahi, tayi maganar tana zaunar da Maryama a d'aya daga cikin kujerun dake gaban mudubi...

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now