12

422 29 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*Please masu yi min Slm na amsa a tambayeni ya kike na amsa bayan kwana d'aya ko biyu a sake cewa slm ya kike, should you stop it please, haba wannan wanne irin abu ne, kayiwa mutum sallama ya amsa, ka tambayeshi ya yake ya amsa meye kuma bayan kwana d'aya ko biyu ka sake yi mishi sallama da tambayar ya yake? Baku da abin cewa ne? Ko kawai jin dadin hakan kuke yi? Ni dai dan girman Allah ku daina yi min bana so, idan anyi min sallama na amsa an tambayeni ya nake na amsa please don't repeat it, just go to the point na abinda kazo dashi direct please*

*Masu Tambayar* '''SAKI RESHE...'''
*yana Wattpad ko YouTube channel d'in TSAKAR GIDA*


1️⃣2️⃣


Sosai Maryama tayi muguwar tsorata amma ta dake bata bari tsoranta ya fito yadda zai gane ba, cikin tsiwa ta fisge hannunta dake rik'e cikin nashi tace " kar ka soma karka kuskura kama fara,
tsayuwarshi ya gyara had'i da kallanta sosai yace " me ke damunki?

Banza tayi dashi tare da rab'awa ta gefenshi zata wuce, can k'asan zuciyarta ji take kamar ta kurma ihu saboda tsoro, gabanta yasha tare matse ta sosai yace " wai kina cikin hankalinki kuwa?

"Kin manta me ake nufi da aure?

Kallanshi tayi ido cikin ido, while gabanta na tsananta fad'uwa amma tar ta bud'e idonta cikin nashi ta saki murmushi me kama da dariya ta k'ara matse tazarar dake tsakaninsu, tace " a'a Malam Yuraam ban san me ake kira da aure ba, amma kai tunda ka sani ina san ka sanar dani yanzu.

"Ina san ka sanar dani meye aure?

"Me ake nufi da aure?

"Me Kalmar aure take nufi?

"Ina san jinsu duka daga bakinka kai da kasan aure, ta k'arashe maganar tana d'an ja baya, sosai mamakinta ya cika shi, duk da yasan tana iyayin fiye da haka idan ranta ya b'aci,
" uhunnn go on ina jinka.

Ta fad'a tana gyad'a kanta, murmushi yayi yace " shine nake san sanar dake yanzu ai, ta matso da kunnenta kusa da bakinshi tace " uhunnn ina jinka ai.

"Ai ba a baki miji yake sanar da matarshi meye aure ba, sai dai muje turaka kan shinfita sai na sanar dake acan ya k'arashe maganar yana kashe mata ido d'aya, rassss! taji gabanta yayi mummunar fad'uwa,
amma ta dage ta kalleshi sosai tace " kafin aje nan ka bari saika san sauran hak'k'ok'in miji akan matarshi ka koyi yadda ake sauke su sai kazo mu shiga turakar har mu kai ga shinfid'a,
zayyi magana tayi saurin shigewa bedroom ta banko mishi k'ofa, ya bita da kallan mamaki.

Ya dad'e tsaye yana juya abun cikin kanshi kafin yaja kafuwanshi da suka saki yabar wajen.

Tana shiga d'aki ta fad'a saman bed had'i da rufe idonta siraran hawaye nabiyo saman fuskarta.

Ta rasa a yadda zata fassara wannan auren ta rasa da wanne suna zata kira aurensu, ta rasa a wanne matsayi zata ajiye kanta a wajenshi.

A iya saninta tasan yadda miji ke d'okin amaryarshi, tasha jin labarin yadda Ango ke mugun zumud'in daren farko amma ita nata mijin babu ko d'aya daga ciki, ball ta fiye mishi komai a rayuwarshi.

"Har ke?

Ta tambayi kanta, k'untataccen murmushi tayi me ciwo tana bawa kanta amsa a fili da fad'in " har ni mana, tunda gashi ya tabbatar min da hakan.

DUK NISAN DARE....Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin