26

374 23 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣6️⃣

"Ruwa....

Ta furta a matuk'ar galabaice muryarta bata fita sosai...

Sai dana duba sosai kana na iya ganewa MARYAMA BUKAR BUGAJE'S ce.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, duk rashin imanin mutum idan yaga halin da Maryama ke ciki dole ya zubar mata da hawaye,
yau kimanin watanni shida kenan tana d'aure jikin bishiya duk rana, duk ruwan sama, duk zafi da sanyin da akayi akanta suka k'are,
shekararta d'aya kenan cif da barinta gida amma yadda kasan wacce ta shekara goma akan gadon asibiti,
ta jeme, fatar jikinta sai rawa take saboda babu ishashshen nama daga k'ashi sai fata,
azaba kam babu irin wacce bata sha ba, harma ta zame mata jiki, duk bayan minti biyar sai anyi mata bulala ashirin,
a rana sau d'aya ake bata abinci colaki biyar, ruwa sau biyu cokali uku-uku, dan haka ta saba da yunwa, k'ishirruwa ce ta kasa sabawa da ita har yau.

"Ruwa...!

Ta sake furtawa a karo na biyu, Djeneba ya kalli d'aya daga cikin yaranshi yayi mishi alama, zabgegiyar bulala ya d'auka irin ta dukan doki ya shiga zubawa Maryama,
Allah sarki, ko kwakkwaran motsi bata iyawa balle tayi kuka illa idonta kad'ai dake motsi hawaye na zuba.

Sai da ya gaji dan kanshi da dukanta ya had'a uban gumi yana haki, sai da ya mayar da numfashi kana ya d'auko ruwa a kofi ya d'iba a cokali ya mik'a mata,
dakyar ta iya motsa leb'enta ta bud'e bakinta ya bata ruwan, colaki uku ya bata kamar kullum...

Idonta ta d'aga sama ta kalli sararin samaniya ta tabbatar lokacin sallar la'asar yayi, tana a yadda take tayi niyyar sallah, bayan ta idar ta kuma d'aga idonta sama tana addu'a cikin ranta.

"Ya Allah kada ka sallama zukatanmu ga wanda basa k'aunarmu, ya Ubangiji kada ka mik'a lamuranmu ga wad'anda basa tausayinmu, Allah kada ka mik'a rayuwarmu a hannun wad'anda suke san tozarta mu,
ya Ubangijin Al'arshe, ya Ubangijin sammai da k'assai ka tausaya min ka kawo min d'auki ka fitar dani daga cikin mummunnar azaba dana saka kaina,
na sani ni me laifi ce kayi min baiwa ban gode maka ba, kayi min ni'ima nayi maka butulci, Allah ka yafe min,
ya Allah ka bud'e min k'ofofin walwala da farin ciki, da kwanciyar hankali, ka kulle min k'ofofin damuwa duniya da lahira,
Ubangiji kai me tausayi ne, kai me jin kaine, kai me afuwa ne, kai me yafiya ne, Allah ka kub'utar dani daga hannun wad'annan azzaluman.....

Saida yamma tayi lik'is kana Issah ya bata rud'an tuwo cokali biyar yaso ya k'ara mata tsoro ya hanashi, yasan bazasu k'ara bata abinci ba sai gobe kullum sau d'aya ake bata abinci, Issah kad'ai ke d'an tausayawa Maryama.

Haka rayuwa taita tafiya lokaci na wucewa, duk wannan tsayin lokacin da aka d'auka Maryama bata samu sauk'i ko sassauci ba,
saima k'arin azaba da wahala data samu, gaba d'aya rayuwarta ta k'are a tsaye d'aure jikin bishiya.

Dare mahutar bawa inji Malam Bahaushe gwanin iya magana, amma a wajen wasu dare tamkar rana yake a wajensu, sun mayar da duhun daren da Allah yayi mana danmu hutu, kamar wata kafa ta aikata mugayen ayyuka...

Western Sahara shiru tsit baka jin motsin komai sai sautin kukan tsintsaye dake tashi lokaci zuwa lokaci, sararin samaniya yayi fayau da hasken farin wata,
d'an motsin da Maryama taji ne ya farkar da ita daga wahalallan baccin da take yi, wasu irin k'attin mutane ta gani burjik a gabanta ba adadi,
da farko ta d'auka su Djeneba ne saida tayi musu kallan tsanaki ta fahimci ba su bane, d'aya daga cikin mutanen ya isso gaban Maryama yayi tsaye k'ik'am,
wani irin mugun tsoro ne ya shige ta lokaci d'aya, jikinta ya shiga tsuma da kerrrrma, ta bud'e baki zatayi ihuu, ya buga mata gudumar hannunshi,
aiko sai jini kanta ya fashe, cikin wani irin yare da bata fahimci wanne bane yayi mata magana,
kwata-kwata bata gane abinda ya fad'a ba, amma ta fahimci abinda yake nufi musamman daya d'ora hannunshi saman k'aton leb'enshi me kama da shantu, ta gane tayi shuru yake nufi,
nuni yayiwa sauran dasu shiga ciki suka d'iba d'uuuuuu, Maryama dai da ido take binsu.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now