30

416 45 5
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣0️⃣

Reras suka jeru a gaban Mania tana shan k'anshi, sai da ta d'auki lokaci me tsayi kana ta soma magana kamar bata so.

"Yau saura sati d'aya zab'e dan haka kowaccenku ta zauna cikin shirinta, haka Nini zata k'ara kulawar datake baku, gyaran da ake yi muku ma zai k'aru, dama dan ranar na tsumaku kuka tsumu dan haka ranar d'aukar dashin dana zuba ta kusa zuwa..

Sai da suka sake d'aukar wani lokacin kana tayi musu alama dasu tafi da hannunta, sun juya zasu bar wajen tace.

"Yauwa ku nutsu dakyau dan bana san wata ta bani matsala, duk wacce ta bani matsala zan bata matsalar data fi wacce ta bani, ku tambayi Bintu idan baku san bada matsala ta ba..

Kansu k'asa suka amsa mata, dan a dokar gidan babu wanda ya isa ya had'a ido da Mania, hannu ta d'aga musu ta sallamesu duk suka fice..

Tun kafin su k'arasa shiga part d'insu Maryama tace " meyasa naji Mania tace a tambayeki bada matsalarta?

"Wani abu ya tab'a had'a ku ne?

"Murmushi Bintu tayi dan ta dad'e da sanin Maryama nada surutu, ita kuma gata Allah yayita da rashin san magana, itafa magana danta zame mata dole ne da batayi ta ba,
a hakan ma bata wuce kalma biyu zuwa uku..

"Ke kinfiya miskilanci wallahi, ayitayi miki magana kiyiwa mutane shiru..

Murmushi ta sake yi dan murmushi d'abi'arta ce, tace " haka nake ba shiru nake yi miki ba.

"To dan Allah fad'a min wacce matsala Mania ta tab'a baki?

"Kamar dai ke d'in nan dana zo haka akayi saboda ina da kyau da surar jiki ta nunawa, dan haka Mania tasan zata samu kud'i dani, ta turke ni har zuwa ranar zab'e,
da ranar tazo aka zab'e ni shine ni kuma naso guduwa, da aka kamoni na tufawa Balaraben daya siye ni yawu a fuska na gantsara mishi cizo...

Dayaga haka shine yaso bawa Mania matsala dan dakyar tashawo kanshi ya yarda ya hak'ura, aka canjeni da wata..

Tun daga nan Mania ta d'aureni a d'aki da sark'a, sau d'aya ake bani abinci da ruwa suma badan na k'oshi ba, d'an tsirit ake bani kamar wanda za'a bawa jariri..

Sai da nayi shekaru hud'u a haka, babu irin dukan da banci ba, haka fyad'e bazan iya irga adadin mazan da sukayi amfani dani ba, dakaina na dawo ina rok'on a fito dani zanyi yadda ake so ranar zab'e,
dakyar ta yarda ta amince aka fito dani, da sharad'in idan ba'a zab'eni cikin wad'anda aka zab'a ba, ko kuma na bada matsala hukuncin kisan kaine...

A tsorace Maryama ta zaro ido kamar zasu fad'o k'asa saboda tashin hankali da tsoro, cikin firgici tace " kisan kai fa kikace?

"Dama bayan duk wad'annan abubuwan da Mania keyi har rai tana kashewa?

Murmushin da bata gajiya da yinshi tayi har hak'oranta suka bayyana tace " da alama har yanzu baki gama sanin Mania da gidan Mania ba,
baki gama sanin irin abubuwan da ake aikatawa a gidan Mania ba, to saurara kiji wanne irin gida ne gidan Mania...

"Duk wani aikin sab'o da kika san ana aikatawa a duniya to ana aikatashi a gidan Mania..

"Ana shan giya, ana luwad'i, ana aikata mad'igo, ana had'a auren jinsi, maza na neman mata ta baya, caca kam kamar gidan na rage, giya ko ba'a magana,
duk wani babban mashiriki ko 'yan fashi nan ne gidan holewarsu.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now