1

2.6K 96 10
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


1️⃣

*LONDON*
Holloway, City of Landon Goal,
Women prison

Da sauri yake taka steps d'in yana shiga cikin Prison hannunshi rik'e da wasu littattafai while d'aya hannunnashi yana rik'e da bak'ar rigar lauyoyi, yayinda kanshi ke d'auke da hularsu ta Barristers kallo d'aya  zakayi mishi kasan Lauya ne.

Yana d'an hanzari ya shiga da gani sauri yake, agogon hannunshi ya kalla a karo na ba'adadi yayi d'an guntun tsoki had'i da d'an basarwa,
" Excuse me Sir......!
Yaji an fad'a daga bayanshi, cikin nutsuwar addinin *MUSULUNCI* ya juya, tare da zubawa matashin baturen da yayi mishi magana ido,
" are you Mr Hateme?

Murmushi ya saki jin yadda baturen ya fad'i Shatima, had'i da bashi amsa da fad'in " yeah! , baturen dan sandan yace " you're the one who want see Yuk?

"Yes! I'm her Lawyer, Shatima ya bashi amsa yana cigaba da kallanshi, " okey fallow me, a baya Shatima yabi shi ya raka shi har wajen wacce yake karewa, ya bud'e mishi d'akin da Yuk take yana fad'in " you've 10 minutes,
"Thank you, Shatima yace yana shiga, a nutse ya zauna had'i da k'urawa Yuk ido na tsayin lokaci " are you here to watch me like a TV or you come here talk to me?

Yuk ta fad'a batare data kalli Shatima ba, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tattara gaba d'aya hankalinshi ga Yuk yace " I think since before I collected ur case, I told you, you've to trust me, an don't hide me anything, because slice mistake can make us loose this case, cikin mamaki Yuk tace " what did I hide you now?

"Am not hide you anything, I have already told you I'm not layer, if i kill him I swear I will tell you the truth, I was told you anything I knew about him,
idon Shatima cikin na Yuk yace " did you told me he's your Ex?

"What?

"My Ex?

"How?

"That's what I want to know from you, how he was became your Ex Yuk?

"If he's my Ex how can I  kill him?

"Think Barrister, think twice,
"You can..! You can kill him, because maybe he cheated you, or he do something wrong...

"No Barrister, how can I kill man...?

I'm a woman Barrister , how can I kill strong man like him?

"Think Barrister.....

Shiru Shatima yayi yana nazari, ya bud'e baki zayyi magana yaji ance " your time is over, bayyi musu ba ya mik'e yana kallan Yuk cikin turanci yace " k'aramin abu yana iya sawa mu fad'i,
bai jira jin abinda Yuk zata ce ba ya fice, doka ce a Prison d'in duk wanda ya shigo sai yayi sign in haka idan zai fita ma sayyayi sign out, dan haka direct wajen da zayyi signing ya nufa,
ya d'auki biro zayyi signing yaji karatun Qur'ani yana tashi k'asa-k'asa a hankali, cikin matsanancin mamaki ya d'ago kai yana neman wanda ke karatun,
" sign Sir..! dan sanda dake tare dashi ya fad'a, ganin ya d'auki d'an lokaci bayyi ba, signing d'in yayi ya fita cike da mamakin jin karatun Quran yana tashi a Prison.

Cikin nutsuwa ta rufe Qur'anin ta aje shi a gefe had'i da d'aga hannunta sama idonta yana zubar da hawaye ta soma addu'a, ta dad'e tana zuba addu'a kafin ta shafa.

Yana fita daga prison din direct Office d'inshi ya nufa, ya dad'e can yana dube-dube kafin ya fita ya soma binciken case din Yuk,
tunda yake a rayuwarshi bai tab'a shari'ar dake neman saka shi ciwon kai ba sai wannan, ya rasa ta inda zai b'ullo mata,
gaba d'aya kanshi ya gama kullewa duk ta inda ya biyo yake ganin akwai mafita sayya rasa,
yasan duk wad'anda suka shirya wannan abun sunyi shi cikin tsari da gani sun dad'e suna shirya plan din, bai kwanta ba sai wajen 3:40am na dare kafin bacci barowa ya sace shi.

DUK NISAN DARE....Место, где живут истории. Откройте их для себя