DUK NISAN DARE....

By HauwaAUsmanjiddarh

23.4K 1.6K 135

Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and last... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
40
41
42
43
44
45

39

397 31 0
By HauwaAUsmanjiddarh

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

3️⃣9️⃣

Kafin awanni 24 da Barrister Shatima ya ambata labarin Maryama ya cika Media kaf, yadda kasan guguwa haka labarin yabi iska ya shiga duniya,
ta kowanne b'angare na duniya maganar da akeyi kenan, har tashoshin CNN, BBC da ALJAZIRA sun haska labarin, sosai labarin ya tab'a zuciyar mutane, aka rink'a fitowa ana yin video ana wallafawa a kafafan sada zumunta,
turawa da 'yan Nigeria suka fara zanga-zangar lumana suna yawo da allunan rubutun JUSTICE FOR MARYAMA, wasu suka rubuta FREE MARYAMA SHE'S INNOCENT,
kafin kace me manyan celebrities na duniya sun fara magana akai...

Maiduguri...

Abba na zaune a falonshi saman sallaya Yuraam ya shigo da wani irin gudu babu ko sallama, duk da yaga Abban na lazumi bai tsaya ba,
ya d'auki remote ya kunna channel d'in BBC k'aton hoton Maryama ne ya bayyana hannunta da k'afarta d'aure da ankwa,
jikin Abba na rawa ya warce remote d'in ya k'ara volume,
da gudu Yuraam ya fita tsakiyar Estate d'in ya tsaya ya d'aga murya yana fad'in kowa ya fito ga labarin Maryama,
jiki na rawa suka rink'a fitowa daga sashensu, duk wanda yazo sayya nuna mishi falon Abba, gaba d'aya gidan aka hallara a falon Abba ana jin labarin Maryama,
har Yuraam ya shigo zai zauna yaga babu Umma, yasan dama ba lalle tazo ba dan duk wannan tsayin shekarun basu shirya da Abba ba, anyi-anyi da ita har an gaji,
tana dai zaune kawai a gidan amma ba wata ma'amula ta auratayya dake shiga tsakaninsu da Abba a tsayin shekaru takwas da Maryama tabar gida,
sake fita yayi ya nufi part d'inta tana zaune a falo tana kallan film d'in Wata Shari'ar a YouTube Channel d'in Al Ajabi Tv, da yayi sallama ko motsi batayi ba,
balle ta d'aga kai ta kalleshi.

"Umma ga labarin Maryama, saurin kallanshi tayi had'i da cewa " a ina?

"Kizo part d'in Abba, duk muna can, d'an jimm tayi tana kallanshi dan tunda abun ya faru bata sake shiga part d'inshi ba har yau,
" idan kayi min k'arya ranka sayya b'aci ka sani ko?

"Waya isa yayi miki k'arya akan abinda ya shafi Maryama Umma?

Ya fad'a cikin girmamawa, dan kowa a gidan shayinta yakeyi yanzu, dan babu ruwanta zata zageka tass, jin abinda yace yasata wuceshi ta barshi nan tsaye,
kanta tsaye ta shiga d'akin tana bin ko'ina da kallo komai ya canja a falon dan ba kayan d'akin data sani bane, shekaru takwas kenan rabanta da part d'in,
ganin hotan Maryama yasata isa gaban TVn tana shafa fuskar Maryama hawaye nabin kuncinta.

"Shekaru takwas kenan raban dana ganki Maryama.

Ta fad'a tana jin wani abu na taso mata.

Tun daga farkon labarin sukaji har k'arshe, tun fitarta daga gida har kawowa ranar data bada labarin, sosai familyn Bugaje suka girgiza dajin labarin Maryama,
da irin wahalhalun data sha, da gwagwarmayar datayi, kaf d'insu babu wanda bai zubar da hawaye ba, harda masu rusa kuka kamar anyi mutuwa,
Abba kanshi sai da yayi hawaye, Umma kam ba'a magana yadda kasan ance mata iyayenta sun mutu.

"Dan girman Allah Alhaji ka nema mana Visan Landon mu tafi, muje muga Maryama, mu tsaya mata, Mama ta fad'a cikin sautin kuka,
ranar kam haka aka yini kamar Abban ne ya mutu, a ranar ya bugawa agent d'insu me yi musu visa waya, ya sanar mishi yayiwa Bugaje's gaba d'aya Visan Landon, ya amsa da " to zan zo na amshi passport d'inku, Abba bayyi magana ba ya kashe wayar.

Yuraam tuni yayi aure tun bayan tafiyar Maryama da shekaru biyu aka matsa mishi da farko yak'i amincewa yace ko shekara nawa Maryama zatayi zai jirata, saida Abba ya bud'e mishi wuta kana ya amince dole badan yaso ba,
aka aura mishi 'yar Massaa k'aninsu Abba, dakyar Yuraam ya amshi Meram matsayin mata har Allah yabasu haihuwar 'ya mace,
aiko ranar sunga ruwan bala'i wajen Umma wai an kori 'ya'yan gida bare sun baje haja harda haihuwa,
abunda ya rage rigimar Umman sunan Maryama da Yuraam ya sawa yarinyar ake kiranta da Lil Maryama,
yanzu haka yaranshi uku mata biyu da namiji d'aya me sunan Abba.

London..

D'an tasin daya d'auki Maryama ya rink'a yawo da ita suna neman Nigerian Embassy yayi video ya rantse yace ranar da abun zai faru shine ya rink'a yawo da ita a taxi suna neman Embassyn Nigeria, ya fad'i duk yadda sukayi da Maryama kuma ya aje number shi akan cewa idon ana nemanshi a kotu zai zo ya bada shaida,
ai videon na fita d'aya d'an tasin daya d'auketa yakaita Emirates Stadium ma yayi ya bada shaidar ranar shiya d'auketa yakaita Emirates Stadium,
videon shi na fita ma'aikacin Stadium wanda ya tasheta daga suman datayi shima yayi video ya wallafa yana bada shaida,
wad'annan videos d'in na fita duniya ta k'ara d'auka kan Maryama is innocent, saboda ga 'yan uwansu turawa nan sun fito sun bada shaida a waje mabambamta,
ba'a dad'e da fara abun ba Nigerian Embassy ta shigo, ta nemi ganawa da Barrister Shatima kafin Maryama.

"Yes! Yes..! Alhamdulillah Barrister Shatima yace yana dukan table d'in gabanshi tare da mik'ewa yana fad'in " in sun san wata ai basu wata ba, komai yana tafiya kamar yadda na tsara, addu'arki ta karb'u Maryama,
yanzu fad'an ba namu bane nasu ne mun barsu suyi abunsu su gyara da kansu, Barrister Ezreal yace " weldon Shatima gaskiya you are very try,
kayi namijin k'ok'ari sosai, kanka yana ja, wai ya akayi ma kayi wannan tunanin?

Murmushin jin dad'in ganin wutar dake tashi a social media yayi, yana duba wayarshi ya bawa Barrister Ezreal amsa da " gani nayi bamu da ishashshen lokaci,
idan nace zan tsaya b'ata lokacin tsayawa na bi kotu bazata kai mun ba,
danaga labarin Maryama yana da d'aukar hankali nasan idan ta fad'a ga 'yan jaridu abun zayyi kuma zai taimaka mana shiyasa,
kai Barrister Ezreal ya jinjina yana fad'in " gaskiya i salute you, duk suka sa dariya.

Women Prison..

Kamar yadda Nigerian Embassy ta nemi zantawa da Barrister Shatima yaje sun tattauna, inda suka buk'aci suna san ganawa da Maryama,
batare da b'ata lokaci ba Barrister Shatima yayi musu iso har Prison d'in, ID Card d'in Embassy d'aya daga cikinsu ya nuna aka barsu suka shiga,
kamar yadda ya saba shiga ya ganta yauma haka tana zaune tana karatun Al Qur'ani mai girma, saida ta dire aya kana ta d'ago cikin nutsuwa da kamewarta ta gaidasu,
Barrister Shatima yayi mata bayanin suwaye yake tare dasu, d'aya daga cikinsu yayi gyaran murya tare da soma magana.

"Dukkanmu nan aikinku mukeyi, dan ku aka ajeyemu ake biyanmu albashi, dan haka mu zamu tsaya maki, ajiyar zuciya ta sauke a fili had'i da cewa " to Alhamdulillah, nagode sosai,
ya cigaba da cewa " ke 'yar wacce k'asace?

"Nigeria, Barno State.

"Meya kawoki London, kuma ta wacce hanya kika shigo?

Cikin nutsuwa tayi musu bayanin komai, kanshi ya jinjina tare da furzar da iska daga bakinshi yace " Allah me girma, yanzu shekara nawa rabanki da gida?

"Takwas..!.

"8yrs kenan?

"Eh! tace cikin girmamawa, yace " shekarunki nawa a gidan yari?

"Shekara ta hud'u da wata uku a gidan yari, a hanya kuma daga Nigerian zuwa London saida nayi shekara hud'u da wata d'aya, sakamakon tsaye-tsayen dana samu a hanya.

"Yanzu shekarunki takwas da watanni hud'u rabanki da gida?

"Eh, tace tana kallanshi.

"Shekarunki nawa na haihu?

"25yrs kenan cif.

Cigaba yayi dayi mata tambayoyi tana bashi amsa cikin nutsuwa har suka gama, ya kalleta yace " da izinin Allah zaki fita ki koma k'asarki cikin 'yanci in sha Allah, tayi kyakkyawan murmushin jin dad'i tace " nagode sosai Allah ya biya.

Nigerian Embassy da kanta ta mayar da shari'a sabuwa ta hanyar d'aukaka k'ara a wata kotun, ranar da za'ayi zaman kotu na farko yadda kasan gwamna za'a kawo kotun haka k'ofar kotun ta cika mak'il da mutane, 'yan Nigeria da 'yan sauran k'asashe daban-daban.

Motar prison nayin parking mutane sukayi mata caa, Maryama ta fito sanye da ankwa a hannunta fuskarta d'auke da yalwataccen murmushi tana d'agawa mutane hannu,
bayan ta shiga cikin kotu an natsa kowa yayi shiru,
Barrister Shatima ya mik'e ya mik'awa magatakarda takardu,
ya amsa ya karanta gaban kowa, alk'ali ya nisa ya buk'aci Barrister Shatima daya tashi ya gabatar mishi da abubuwan,
Barrister Shatima ya tashi ya soma kwararo bayani cikin harshen turanci, kana ya gabatar da hujjojinshi na 'yan tasin nan guda biyu da ma'aikacin Stadium,
dan tuni ya nemosu, d'aya bayan d'aya suka fito gaban kotu suka bada shaida, bayan sun koma sun zauna Barrister Shatima ya fito da faifan videon d'aukar camerar tsaro,
ya haska gaban kowa, kowa yaga lokacin da Maryama ta shiga Stadium da sanda ta fito, ya d'auko wani faifan videon ya saka na lokacin da b'arayin sukayi fashi a banki,
lokacin ma Maryama na kwance a Stadium bata fito ba, haka da aka duba a videon su bakwai ne kuma dukkaninsu maza ne,
bayan duk wad'annan hujjojin da Barrister Shatima ya gabatar ya buk'aci kotu ta bashi damar gabatar da hujjarshi ta k'arshi,
kotu ta bashi dama, ya umarci 'yan sanda dasu shigo da d'aya daga cikin 'yan fashin aka fito dashi ya fito gaban kotu yabayar da shaidar cewa babu Maryama cikinsu,
bayan an natsa alk'ali ya nemi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, alk'ali ya nisa kana ya soma magana " kotu ta gamsu da duk hujjojin da aka gabatar abanta, sannan ta sallami Maryama ta kuma wanketa a idon duniya, sannan kotu na umartar hukumar 'yan sanda dasu biya Maryama tarar zaman yarin da suka sakata har tsayin shekaru hud'u da wata uku,
hukumar 'yan sanda zata biyata Europe 100,000, sannan kotu tana jinjinawa Barrister Shatima abisa namijin k'ok'arin da yayi ya gano gaskiya, k'asa nayi mishi godiya, kuma za'a bashi kyautar girmamawa,
daga nan kotu ta sallami kowa, Maryama ta lumshe idanuwanta hawaye na gangarowa daga idanuwanta,
"Alhamdulillah, Allah na gode maka, abinda take maimaitawa kenan,
Barrister Shatima yazo gabanta ya tsaya yana murmushi,
bata san sanda ta fad'a jikinshi had'i da fashewa da matsanancin kuka ba, dama neman wanda zatayi kuka a jikinshi takeyi, neman wanda zata rab'a taji sanyi take yi,
bata damu da yawan mutanen dake wajen ba, bata damu da videos da ake d'aukarsu ba, ta ruk'unk'umeshi sosai tana kuka kamar ranta zai fita,
wani abu me kama da sanyi-sanyi yaji yana ratsashi, yayinda zuciyarshi ke tsalle kamar zata tsaga k'irjinshi ta fito,
hannu yasa ya rungumeta tsam a k'irjinshi yana d'an bubbuga bayanta, a hankali ya soma tafiya da ita a jikinshi har suka fita daga kotun,
suna fitowa 'yan jarida sukayo musu caaa da tambayoyi, Barrister Shatima ya shiga kakkare Maryama........


*JIDDARH....* ✍🏻

Continue Reading

You'll Also Like

3.3K 430 11
They built their own dream to live together to their last breath. They promised to stay with eachother , stick with each other till the last day of l...
38.4K 957 29
This story is about strong love that is way beyond DISASTROUS. this story is about a Maiduguri girl and a yoruba kingdom, The Oba of lagos and the pr...
590K 19.8K 84
Child of the Eldest Gods from the East, Heiress of Earth and Legacy of Stars and Magic, Has the Affinity to Balance the Peace of Nature, Fated Love i...
55.2K 1.1K 68
A student from the Paldea region took an interest in traveling to other regions to learn new things.