DUK NISAN DARE....

De HauwaAUsmanjiddarh

23.1K 1.6K 135

Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and last... Mais

1
2
3
4
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45

5

555 42 0
De HauwaAUsmanjiddarh

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

1- *KAUNA CE*
      NA UMM ASGHAR

2- *RUKUQI*
   NA FEEDHOM

3- *WANI SO*
      NA ZEE YABOUR

4- *SO DA ALAKA*
       NA UMMI  AISHA

5- *MUGUN GANI*
    NA SADIYA NASIR DAN

6- *ABDUL_HAMEED*
      NA NANA DISO

7- *MUKULLIN ZUCIYA*
        NA MAMAN KHADY

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*
+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki


5️⃣


*LABARIN MARYAMA...*

Gidanmu babban gida ne dan a k'alla part yakai 30 a ciki, akwai 'ya'ya da jikoki a ciki, duk wanda yayi aure anan ake bashi part ya zauna,
da wuya kaga familyn Bukar Bugaje a waje ba a cikin Estate d'inmu ba,  kakana Bugaje Zanna yana da matan aure uku da 'ya'ya ashirin, matarsa ta farko tana da yara goma wacce itace kakata data haifi mahaifina Bukar Bugaje, mahaifina shine babba a gaba d'ayan gidansu,
sai matarshi ta biyu tana da yara shida saita uku tana da yara hudu kunga su ishirin kenan cif kakana ya haifa, jikoki kam ba'a magana dan bazamu lissafu ba, kuma gaba d'ayan 'ya'yan kaka babu wanda yayi karatun boko saina allo,
mahaifina Allah yayiwa arziki sosai dan babu inda sunanshi bai kai a Nigeria da wasu k'asashen k'etaren ba,
babban d'an kasuwa ne da Allah yasa mishi albarka cikin kasuwancinshi, mahaifina yana da matan aure biyu Mama itace uwar gida sai Umma mumu goma sha uku ya haifa maza sha biyu sai ni mace d'aya,
Mama itace mahaifiyata ainahin sunanta Falmata, mu takwas ne a d'akinmu, Madu shine babba sai Abuwar, Baana, Bakura, Rawaana, Ari, Tujja, sai ni Auta Maryama,
a d'akin Umma, wacce ainahin sunanta Fandi, yaranta biyar, Massa shine babba, sai Zanna, Aduu, sai Aliyu da Adaa.

Mahaifina yadad'e yana san 'ya mace yana kuma addu'ar samunta, amma bai samu ba sai daga k'arshe, Allah ya bashi ni, yayi murna sosai da farin cikin haihuwata ya saka min sunan Kakarshi data rik'eshi ta jiya mishi dad'i sosai Maryama.

Na taso cikin so da k'auna da kulawar 'yan uwana dan san da ake yi min daban yake, kowa ni duk inda na juya ni, kamar ni kad'aice 'ya mace a gaba d'ayar zuri'armu, k'annan mahaifina 19 kowa yana da 'ya'ya mata daga mai biyu sai mai uku har da wad'anda mata kawai suka haifa ba maza, amma a danginmu 'ya'ya maza sunfi yawa.

Bamu da wata matsala ko k'alubale a cikin zuri'armu sai d'an abinda ba'a rasa ba, kowa yana zaune da kowa lafiya ba bak'in ciki, ba ganin kyashi ba hassada, lafiya lau muke zaune, gidan kowa na kowa ne, idan aka haifi d'a a zuri'armu duk shashen wanda yake san zama nan zai zauna har girmansa,
kuma baka isa ka gane ba'anan aka haifeshi ba, hakance ta kasance akan Yuraam tunda ya taso yake san b'angarenmu, sosai Yuram yake san mahaifina fiye ma da mahaifinshi, dan haka ya taso part d'inmu a hannun Umma kishiyar Mamana,
kar kuji ina cewa Umma kishiyar Mamana ku d'auna da wani abu, ko d'aya babu komai dan rabin 'yan d'akinmu a d'akin Umma suka taso,
haka itama gaba d'aya yaranta Mamanmu ce ta rik'esu, kuma duk bin kwakkwafin mutum bai isa yace yaga wani abu na aibu ba, kowa yana rik'e yaran kowa da gaskiya da amana da zuciya d'aya.

Tunda aka haifeni kowa yake san rik'e ni amma nak'i dan nataso da bak'ar k'iwa da k'ulafucin uwa, har girmana babu abinda yake rabani da mahaifiyata hatta wajen kwanciyarmu d'aya,
kuma saina rungumeta tsam a jikina nake iya bacci, dan haka kowa ya shafawa kanshi lafiya ya hak'ura da rik'ona.

Yuraam d'ane ga k'anin Abba na biyar Abuwar wanda yayana yaci sunanshi, Yuraam mutum ne mai fara'a da shegen surutu yana mugun SAN BALL(kwallon k'afa),
kowa yasan wannan dan bai had'a ball da komai ba a rayuwarshi, duk mahimmancin abu Yuraam yana iya bashi baya akan ball,
kasan maza akan ball sai dai ayi shiru, saboda san ball a jinin jikinsu take, amma sanda Yuraam yake yiwa kwallan k'afa daban ne, ya bata mahimmanci sosai a rayuwarshi, Abba kad'ai ke iya taka mishi burki akan ball, amma shima idan ya samu dama sai ya kwarfe,
ansha zama family meeting kan san da Yuraam ke yiwa ball, fad'a da duka kam babu irin wanda baisha amma abu yaci tura,
kai duk yadda kake tunani ko jin labari ko ganin mutumin da yake ball to Yuraam kat ne, k'arshen zance ne akan ball.

Akwai 'yan ball sosai a Bugaj'es Estate, kasan ko yaya gida inda maza sai an samu masoya ball, balle mu da muke da maza da yawa, har 'yar k'aramar cinema Abba yayiwa mazan gidanmu ta kallan Ball,
idan ana musun ball a gidanmu saika d'auka kasuwa ce ko yak'i ake,
dayake mu gidanmu bamasu zafin ak'ida da tsatstsauran ra'ayi bane, bamu bawa boko mahimmanci ba, haka bamu zafafa ta fannin addini ba, komai dai-dai d'an cif da cif.

A cikin jerin abubuwan dana tsana ball tana layin farko, dan a rayuwata ban tab'a tsanar wani abu sama da ball ba, gani nake asarar lokaci da rashin aikinyi ke sawa mutum ya zauna yana kallan ball,
lokacin da tahiri ya biyo naji da kan jikan Manzan Allah Annabi Muhammad (S.A.W) aka fara yin ball a duniya naji na k'ara tsanarta fiye da komai da kowa,
dako naji Malamai na wa'azin cewa Yahudawa sun k'arfafa ball ne saboda shagaltar da musulmai da musulumci ji nayi kamar nayi hauka,
kamar yadda kowa yasan Yuraam da san ball haka kowa ya sanni da k'in ball, karkuyi zaton hakan zai kawo mana matsala ko rashin jituwa a tsakanina da Yaya Yuraam,
babu wata matsala a tsakaninmu lafiya lau muke zaune sai idan ta kama mukam d'an tab'a 'yar tsama, ba kuma dashi kad'ai ba da duk wani masoyin ball ko wanda ya bata fahimmanci nakan d'an tab'a.

Allah ya yayi ni da rigima da tsokana, saboda da wuya ka wuni bakaji inayi da wani ba, amma fa ba fad'a ba, iyaci inyi tsona Umma ko Abba su shigar min,
b'angarenmu d'aya da Yuraam amma ba wani sosai Allah ya had'a jininmu ba wata shak'uwa ta azo a gani a tattare damu,
haka babu matsala a tsakaninmu muna zaune kadaran-kadahan yadda nake da yayye na haka nake dashi, sai dai kullum muna cikin rigimar ball,
koya tsokaneni kona tsokaneshi, dan da farko na d'auka shima d'an Abbanmu ne,
a b'angaren auratayya da wuya kaga mun aure bare gaba d'ayanmu auren gida muke yi, sai d'aid'aiku da suka auro bare a waje,
kasancewar idan kace kana san bare baka da ra'ayin auren 'yar gida ba matsawa za'a baka dama, wannan shine shinfid'ar labarin zuri'ar mu.

Da sauri ya shigo yana huci kamar zaki, ko sallama bayyi ba, " Umma ina Maryama?

"Ta tafi koyo sallama, Umma ta fad'a batare data kalli inda yake ba, kanshi ya shifa yana k'ak'aro murmushi yace " yi hak'uri, kana ya koma yayi sallama ya shigo, bai bari ta amsa ba ya d'ora da " Umma kinga Maryama..?

Kallan yadda jikinshi ke rawa tayi tace " inama akan addinin Allah jikinka ke b'ari haka, " Umma.. Yace yana k'ok'arin sake tambayarta, " a'a ni ban san inda Maryama ta shiga ba, jeka can ka nemeta,
ai baima jira ta k'arasa ba ya fice, yana fita su Zanna suka shigo, " Umma kinga Maryama?

"Kai jama'a yanzu ku duka zagada-zagada har biyar kuka zo neman Maryama?

"Umma ai kema kin san halinta, duk ranar da za'a buga babban wasa saita d'auke remote ko adoptor ('yar yawo), da code ware.

"Ai dama nasan ba banza ba, tunda naga jikin Yuraam na b'ari nasan da walakin goro a biya, to bata shigo min ba kuje can ku nemata,
ba wanda yayi magana suka fice, kacib'us sukayi da Yuraam dake fitowa daga part d'in Mama a matuk'ar k'ufule danji yake kamar zai mutu, " ka ganta?

"Ina fa na ganta, kwafa yayi cikin takaici yana fad'in " wallahi yau idan na kama Maryama saita gane Allah yana da girma, Abuwar zayyi magana Rawaana yace " gata can, ya nuna ta tana sand'a zata fita,
ido ta runtse had'i da cije lips d'inta tace " oh! na shiga uku, yau sai buzuna, gaba d'aya sukayi kanta kamar zasu cinyeta d'anya,
da gudu tayi part d'in Mammadu k'anin Abba na uku, tana gudu suna binta har part d'in, da zafin rai Yuraam ya fisgota tayi baya zata fad'i,
Allah ya taimaketa ta dafe bango dataji jiki, da zai iya dukanta kam yau data sha duka amma duk da haka bazata ci banza, ya kama hannunta ya lankwasa ta baya,
ya murd'e hannun sosai, ta saki k'arar azaba, ya kama kunnenta cike da mugunta har yana cije lips d'inshi, yace " bana hanaki tab'a mana kayan kallan ball ba...?

"Sa'anninki ne mu?

"A'a Yaya Yuram.

"To meyesa kika k'ara bayan na hanaki...?

"Taurin kai da rashin jin magana ko?

"A'a Yaya ba haka bane, ta fad'a tana k'ok'arin fashewa da kuka, " ba rashin jin magana ba?

"Ki cigaba kece zaki sha wuya, " Yuraam kayi sauri an fara wasan, ai da wani irin mugun sauri ya hankad'e Maryama ta fad'i k'asa, da gudu kamar me gudun mutuwa ya nufi inda ake kallan,
tabi bayanshi da kallo tare dacewa " Allah ya isa na, yaji sarai sai dai bashi da yadda zayyi dan bazai iya barin kallan ball saboda wannan shirmen ba, dan haka kota kanta baibi ba.

Baka jin komai a gidan sai ihunn samari musamman Yuraam daya cika gaba d'aya gidan da ihuun sun ci wasa, yau kowa a gidan yasan zai sha kyauta tunda su Yuraam suka ci wasa,
dan idan suka ci wasa sayya kusa kyautar da duk abinda ya mallaka, Maryama na can kwance bak'in ciki fal da zuciyarta dan ji take kamar ta mutu,
da gudu Yuraam ya shigo d'akin da take ya duk'a yayi mata ihuuun " goooooooo munci wasa, cikin  kunnenta, hannayenta ta sanya tana k'ok'arin rufe kunnenta, ya rik'e hannayennata, suka shiga kici-kici, ita tasan ta kwace shi kuma ya rik'eta gam, Umma ta shigo ta d'ad'a mishi duka a baya, yayi saurin mik'ewa yana sosa wajen,
" kai Umma, wallahi da zafi sosai fa, " shine kazo ka saka min 'ya gaba da tsokana ko?

"Wallahi ka fita ido na tom kaji na fad'a maka, dariya yayi yace " wayace ta fito da k'iyayyarta ga ball afili?

"Mu duk wanda bai san ball muma bamu babu bashi, kuka Maryama ta saka tana fad'in " Allah bazan yarda ba saina rama, dariya yayi had'i dayi mata kwalo yace " bazaki rama ba sai dai ki rame, ta bishi da gudu ya fice, Umma tabi bayansu da kallo tana murmushi, ta d'aga murya tace " Yuraam karka sake ka cutar min 'ya, inba haka ba nida kai ne yau a gidannan,
a harabar gidan sukayi kicib'us da Abba, ai Maryama na ganin Abbanta ta soma diddira k'afa tana kukan shagwab'a, Abba ya mik'a hannu ya jawota jikinshi yana murmushi irin na cikakkun mutane masu kamala yace " waya tab'a min auta...?

"Abba ba Yaya Yuraam bane yake min ihuuu a kunne dan sunci ball, " a'a Yaya ya taro march gaskiya, " Abba ta fito k'iriri ta nuna bata yin mu, " ku bari zan baku ajiyar juna muga wa zayyi nasarar jan ra'ayin d'aya, wanda yayi nasara akwai kyauta me tsoka.

Ita bata gane inda maganar Abba ta dosa ba amma shi Yuraam ya gane Abba yana nufin zai had'asu aure kenan, " har abada bazan tab'a san ball ba Abba, Yuraam ya kwaikwayi maganarta yace " har abada bazan tab'a k'in ball ba Abba, cikin shagwab'a tace " Abba ka ganshi ko?

Ya kuma kwaikwayonta yace " Abba ka ganta ko?

Ya fad'a yana yi mata kwalo, ta bishi zata kamashi yayi cikin gida da gudu ta rufa mishi baya, Abba yabi bayansu yana murmushi tare da fad'in " k'uruci dangin hauka......



*JIDDARH*

Continue lendo

Você também vai gostar

88K 3K 60
kaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.
175K 8.4K 33
The story of Bintu,where two Brothers from a wealthy family fall head over hill inlove with her. get ready,seat back properly and read this amazing h...
94.8K 2.7K 20
Kody takes Lumine out ice skating for the first time! Boy x Boy - Lumine x Kody Disclaimer! I do NOT own any of the characters, or pictures! I only o...
49.8K 2.4K 82
What if it wasn't Japan that teleported to another world, but the superpower country on Earth, America's Cold War rival that in our OTL is collapsed...