4⃣6⃣: Adamawa

1.1K 107 3
                                    

Dady da Rumasa'u da samir suka dunguma zuwa adamawa, dayake ta flight sukabi yasa tafiyar bata musu wahala ba, dakyar dady ya gane unguwar cikin kauyen da yanxu an dan gyayyara gine-ginenshi da kwaltr sabanin da da babu ma kwalta, Rumasa'u tun tasowarta bata taba zuwa ganin enuwansu ba,

Family house ne mai girma dayake iyayen dady sun rasu dama tun yana karami, mahaifan momyn Ruma ne suka rike shi
Mahaifin momy da mahaifin dady uwa daya uba daya suke kmr yadda na fadamuku a baya auren dangi momy da dady sukai,,,

Suka shiga gidan da sallama dukkansu inda dady yaji wata nadama ta sauko mai, matar na tsugunne nesa dasu tana share kashin dabbobin da suka fita kiwo, ta amsa sallama tana mai dagowa ta kuma gyara zaman goyon bayanta sannan ta juyo,, har ta karasosu bata gane su ba, sak diyar fulani batafi shekaru 25 ba, ta gaidasu dady ya amsa kamin yace
"Dan Allah inna fa?" Dayake haka kowa ya Santa," yadda ya fadi sunan innar ne yasa ta gane shi tai dif tana son tuna sunanshi da inna kan yawan bata labari, Kardai Alhajin birni mijin yaya shamsiyya? Dayake haka inna ke kiranshi  "Alhajin birni"....

Ya jijjiga kai yana mamakin yadda ta ganeshi da wuri alhalin shima be santa ba cikin danginshi, kawai sai ta hade rai ta tamke fuska sosai, ta sake dubansu daya bayan daya kmr me gudanar da aikin bincike, to ina itakuma yaya shamsiyyar?.... Dady ya sunkui da kai, bece komi ba, kawai se ta juya ta koma gun dabbobinta ta cigaba da aikinta,...
Ruma ta tsaya tana kallon wnn sarauta ta ubangiji, tana kokonton anya kalau matrnan take,
Suna nan tsaye cirko cirko, ya shigo sabe da fatanya a kafada, cikin rigarshi da ake cewa er shara, sallamarshi ta makale sanda yayi tozali da baki en birni a tsakargidan, dukka suka juya su dady knn, yayi dan murmushi, dady da mamki yace
"Habu" (kanin momy)" habu yayi shiru yanason tinashi se kuma yace Abdul,,,, dady yayi farinciki ganin ya ganeshi

Sai bayan sun zauna kan tabarmar sun nutsu habu ya kawo musu ruwa har lokacin tsahare tana bakin garkem dabbobin batareda ta damu ba, dady yace
"Ina su inna? Kuma wace waccan?" Ya fada yana kallan inda tsahare take
Habu yace "au tsahare ce fa yarinyar gurin kishiyar abu ita nake aure yanxu"... Se yayi shiruu sannan kuma yace
"Kwana biyu kun bata an dena ganinku sam, ina yaya shamsiyya",
Dady yayi dif yana jin alhinin rasuwar momy se kuma ya soma bashi labarin yadda komai ya faru a rayuwarsu tiryan tiryan, gabadaya jikinsu yayi sanyi ,,, kuka ne me ciwo ya kufcewa habu sosai, hakan yasa tsahare ta karaso dan tasan dalilin kukan nashi dama tun dazu hankalinta na kansu,
Ta dubi dady
"Inna ta jima da rasuwa haka shima baba, ciwon amai da gudawa akai wanda yayi asarar rayuka da dama ciki hardasu"
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai suke maimaitawa, abin mamaki kawai se gani sukai dady ya soma kwalla, ya rufe fuskarshi yana mai jin dacin rasuwar inna batareda ya bata haquri ba, haqiqa sun tafka kuskure shida momy, habu ne ya dinga bashi baki
"Inna da baba sam basu rikeka ba sun riga sun haqura, duk da sunji zafin wofantr da en uwanka da kayi saboda kayi arziki amma sam basu rikeka ba, dukkanku suna kaunarku, kadai cigaba da addu'a Allah ya kyautata musu makwaci,
Anan gida suka kwana ranar kafin daga baya suka dinga zagayawa family suna gaida en uwa Ruma ta matuqar ji dadin ganin en uwanta harda sa'anninta kowa ya gansu ze dauka samir ne mijinta, dady be baro kauyen ba seda ya nemi zama da kawunnan Ruma ciki harda habu qanin momy ya sanar dasu maganar aurenta, dayake ba masu ruko bane duk suka haqura kuma suka tabbatr mai zasu zo, dan haka yace "zan aiko da kota kawai se a daukeku zefi sauki"
Kwanakinsu uku suka baro kauyen, Ruma harda zuwa su rafi dasu dandali, harda zuwa jeji tsinko en itatuwa, kuma duk inda zata samir na biye da ita dan bata kariya, amma ita tana waya da habibin nata kusan koyaushe,

Bayan dawowarsu Abuja ne kuma dady ya soma shirye shiryen tarbar sirikan nashi, dan karamin gidan nashi ya sake gyarawa Abinshi, gidane mai dakuna biyu da kuma main falour self con, kowanme daki da bandaki sannnan kuma kitchen cikin falourn a waje kuma akwai varender something like drive,,,, Ruma dama tana gidan mufida abinta, kullum mufida cikin tsokanarta take amaryar gobe amaryar Abdallah itadai sedai murmushi kurun sam bata iya cewa komai dan ita daya tasan irin tsabar farincikin datake ciki
Ana kashegari zasu zo da asuba dady ya aikawa en adamawa da mota dayake tafiyar me tsayi ce, se kusan dare suka karaso Abuja...
To gareku masoya ruma da Abdallah, masu son ganin su tare masu qaunar ganin sun zauna inuwa daya ta sunna, ina mai farincikin sanar daku an saka ranar auren Abdallah da Ruma watanni shida masu zuwa in munada sauran numfashi,, Ruma saida tai sallah dan godewa ubangiji, ji take kmr mafarki idan ta tuna halin datashiga shekarun baya se ta dauka

Not edited

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now