3⃣4⃣: Decision

1.4K 104 10
                                    

Nasani ban kyauta ba dana bar masoyana suna jiran update, amma kuyi haquri dan Allah, yanxu hakama zanyi summarizing littafin naga na kammalashi da wuri saboda abubuwan da sukamin yawa ban samun ishasshen time Ayshab na alfahari da masoyanta a duk inda kuke.....

Ya kankame hoton a kirjinshi da karfin gaske har saida glass din yayi rawa... Ma'ana ya dan tsage, zuciyarshi zafi take mai sosai ji yake kamar yaci amanar Rumasa'u ne, yana tsananin son ganin Ruma a yanxu yanaso ya ganta koda sau daya ne yayi mata bayanin gaskiyar lamarin amincewar aurenshi da halima,,,, sai kuma ya rage rikon dayyiwa hoton kamin ya saukeshi kan cinyarshi yana kallon zanen fuskar kuruciyar Rumaisa nshi, a hankali memory dinsu na baya ya soma mai yawa cikin ka, kamar ana rewinding film har ya tsaya a ranar da suka fara haduwa... Ita da mufida a garden din makarantarsu suka taimaka mai da abinci, zuwa sanda Ruma ta cigaba da taimakonshi a sanda yake abin kyama da lokutan da sukan tsaya yin hira in an tashi kamin azo daukanta, kalamanta, nutsuwarta, hankalinta uwa uba tsantsar kulawar da Ruma ta nuna akan Abdallah sun isa ya fad'a mata.... 'Soyayyar farko kuma soyayyar karshe' .......
Abdallah ya tattara ya koma makaranta tun hutunsu be kare ba dan ji yake kamar tsikarinshi akeyi, yama manta da waccen maganar ta neman ruma da yayi niyyaryi idan ya dawo da kuma neman wacce ta kawo hafiz dan gabadaya tunaninshi ya dagule. Ya dauki zanenshi yayi gaba inda yake sake jadddawa halima aurensu fa ba kan soyayya bane ta sa a ranta ya kubutar da itane daga auren hafiz na wannan lokaci inda hali ma ta fidda miji kafin lokacin bikinsu.... Halima a nata bangaren tadaijishi ne kawai bawai dan ta yarda ba, ta kudire yin amfani da duk wata hanyar gaskiya da zatabi dan karkato da hankalinshi , dan sam batajin kishin Ruma dan a ganinta mene abin kishi da wacce ma bata santa ba kuma babu ranar haduwarsu da Abdallah, zatayi kokarinta ta ba ya Amir din rayuwa mai cike da farinciki da jin dadi.......

Bayan shekaru 3

Ta rungume gawar a jikinta tana mai tsanata kukanta..... Tafi mintuna 10 a haka tunda ta fahimci mutuwa tayi  rayuwar tayi ta zafi ashe dai idan baka dashi babu mai kulaka kowa kyamarka yake, ta gaji da rayuwa ta gaji da zaman wahala ta rintse idonta gam hawaye na cigaba da kwaranya kan fuskar gawar momy, Ashe haka Abdallah yaji sanda ya rasa mahaifiyarshi, itakam kamar bazata iya jurewa, ga wulaqancin duniya gana rashin mahaifiya dama haka Abdallah yakeji shima? ..... Dady ya hdiyi wani abu mai daci kamin ya garo kekenshi zuwa kusa da diyar tashi ya dafata da hannunshi mai lpia yan mai jin zafi fiyeda wanda takeji, Annabi yayi gaskiya dayace ku tausayawa mai arzikin da karayar arziki ta sameshi, gashi sunaji suna gani saboda rashin kulawa da kudin magani da diet sun rasa momy, be iya ce mata komai ba shima, jikinta yayi sanyi sosai zuciyarta na bugawa tmkr zata bude kirjinta ta fito lokaci guda tana mata wani radadi da zugi,, ta daga kai ta kalli dady daya dafata, ya rame ya kanjame yayi baki kuka ya taso mata mai ciwo, bazata iya rasa dady ba, abin ze mata yawa.... Dakyar da sidin goshi da taimakon makota aka kai momy gidanta na gaskiya wacce ciwon sugar yayi ajalinta, tun watanni tara aka gane tanada ciwon ashe ko a lokacin ma yayi mata mummunan kamu, bayaga hawan jini da jiri da haki da matsanancin migraine wanda lokuta da dama yake haifar mata da blurredvision duka take fama dasu sauki sai a gurin jalla ashe lokaci ne yayi.... Allah yaji kan dukkan al'umar musulmi da suka rigamu gidan gaskiya mukuma Allah ya kyauta namu zuwan Amin

Hmmm fadin tashin hankali da rashin sukunin da zafin mutuwar da ruma ta shiga ma bata bakine, ko dasy ya danne yayita lallashi amma inaa kamar kurma bata gane komai, Rumasa'u ta sanya hijab dinta ta zauna cikin en zaman makokin da yawanci makobta ne da suke kirki sosai dan Ruma ba daga nan ba, duk wanda yazo mata gaisuwa se abin ya sake dawo mata sabo dal, idanuwan nan sunyi jajir ciki da kan fatar, tayi duhu ta rame dama ba wani jikin arziki ba sai ta sake zukewa, haka a daddafe har akayi sadakar uku, addu'a kuwa Ruma yi takeyi ma momy kamar ba gobe, ko dady se ya haqura ya zuba mata ido, haka kawai zata dauro alwala tayita sallah tana kuka ana haka ciwon dady ya tashi jiki ya rikice
Rumasa'u na zaune kan dadduma da daddare tana jero addu'o'i wa momyntata, bayan ta idar ta zauna tayi jigum har aka kira asuba tana nan, bayan ta idar da tata asubar tana kokarin kama dady shima yayi tashi kamar yadda suka saba ne sai taga sam beyin motsi sabanin da da yana dan kokartawa, jijjigashi take amma babu mtsi, hankulanta suka dugunzuma ta soma kakkarwa jikinta na bari tana kallon dady, dan Allah dady karka tafi ka barni cikin wannan rayuwar banda gatan kowa daga Allah sekai dady kaf duniya kaine gatana, wata ajiyar zuciya taji yayi wanda ya dawo da hankalinta ta gane yana raye, haka ta ciccibeshi zuwa asibitin kusa dan bashi taimakon gaggawa

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now