3⃣5⃣: Wedding

1.4K 107 16
                                    

Ya feshe jikinshi da turare mai matuqar dadi, har saida yaga nauyin kwalbar turaren ta ragu ma'ana ya kusa hallaka turaren.... Nasan ko haka na barku kun gane wane keyi wannan feshin tiraren, ya dubi wristwatch din dake daure a wrist nashi, karfe 7 daidai na daren ranar, a hankali ya koma ya zauna kan gyararren hadadden gadon dayasha gyara da pure white bedsheet royal design, a hankali ya furta "badan kaine ba Amir da bazan kwana banje naga Ruma ba" kasancewar be dade da sauka a kasar ba, dan za'a iya cewa saukarshi kenan ya soma shiri wanda bikinne ya dawo dashi bayan doguwar magiya da ban baki dayayiwa iyayen nashi..... Taro yayi taro, guri ya cika da jama'a kowa fuskarshi sakayu dan murna bama kamar Amaryar da bakinta yake a bude sam ta kasa rufeshi, haka ake hotunan da kana kalla kasan murnar dake kwance a fuskarta bazata misaltu ba, babban abokin ango ya karaso a makare yana mamakin yadda gyrin ya cika bayan 6 ne a jikin iv din, a ranshi yace babu ko dan african time, ya gyara zaman hular kanshi kamin ya shiga cikin hall dayasha ado decoration tako ina, straight high table ya wuce inda yasan nan gurin zaman shi yake.... Amma kamin ya zauna ya karasa gun angon da yayi kala da mara ishasshiyar lpia, ganin shi dayayi yasa ya washe baki yana mai nuna farincikin ganinshi saikuma ya tsuke fuska "yanxu kai dan Allah kana babban aboki shine se yanxu xaka karaso" khalil ya rike kunnenshi kawai alamar apologies batareda yayi kokarin bayani ba, shima angon yayi dariya alamar ya wuce daga nan suka bude hira inda yake sanar dashi ai a yau jirginsu ya sauka shiyasa be samu zuwa da wuri ba.... Yayiwa Amarya Allah ya sanya alkhairi..... Kashegarin wanann rana karfe 10 aka daura auren Halima Abdallah da Amir Abdallah, taro yayi taro hakama jama'a kowannensu farinciki ba kamar Abbah dan dadi, da yamma aka dauki amarya Halima aka kaita gidanta na aure mai cike da tarin sirrikan boye...

 Kashegarin wanann rana karfe 10 aka daura auren Halima Abdallah da Amir Abdallah, taro yayi taro hakama jama'a kowannensu farinciki ba kamar Abbah dan dadi, da yamma aka dauki amarya Halima aka kaita gidanta na aure mai cike da tarin sirrikan boye

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

   Amarya halima

Khalil be samu kanshi ba se bayan an gama kai amarya suma suka kai ango a lokacin misalin karfe 10 ne na dare.... Yana yin layin unguwarsu bai tsaya a gida ba ya zarce gidansu Ruma dan gani yake baze iya jira har gobe ba yayi mai nisa, gashi yayi loosing numberta da dadewa, baisha mamaki ba seda yaje ya tarar da kofar gidan garkame da kwado, ya tsaya kadan yana nazarin, shekaru uku zuwa hudu tun rabuwarsu, wacce rayuwa Ruma tayi bayan barinta gidansu? Ina ta koma da aiki? Ya jikin dady da momy?, wani dan saurayi ne dabai kai khalil din shekaru ba yazo wucewa, khalil yamai sallama kamin yace "masu gidannan fa?" saurayin yace "dazu da safe dai naga suna ta fito da kaya kafin daga baya wata mota tazo ta daukesu... " ya kalleshi "harda marasa lpian?  Ma'ana iyayen? " saurayin yace "ai mahaifiyar ta rasu babu dadewa dan ko bakwai ba ayi ba, mahaifinne shima jikin ya tashi" khalil ya mai godiya yana tinanin inane haka Rumasa'u ta tafi?  Kuma dagaske ne momy ta rasu, ya koma mota ya zauna yana mai jin haushi da tsanar kanshi daya gaza taimakon Ruma, tabbas mutuwar momy ta girgizashi, yasan itama Ruma haka, Allah yasa dai kar Ruma tayi hukunci batareda dogon nazari ba, yasan koma mene Ruma bazata saka kanta a hanyar  b'ata ba.....

* * * * *
Rumasa'u bata boyewa dady komai ba kan yadda sukayi da Alhaji dan'ada, dukda baze mayar mata ba amma ta sanar dashi, kamar yadda Alhajin yayi alqawari kuwa tun a airport din kano suka rabu, Ruma tayi Abuja dady kuma yayi cairo a can za'a mishi aikin dan har takardar yarjejeniya suka rubuta, da alqawarin se an fara aikin dady da wata daya sunga outcome tukunna ayi mata implanting yaron.... ( Hakika ni Aysha b na jinjinawa Ruma, domin samun diya kamarta a yanxu abune mai wahala, masu ganin laipinta danta yarda kusani su iyaye sunfi karfin komai wlhy, ko iya haifomu da sukayi bazamu taba biyansu ba, to Ruma ma ai nata da sauki tunda Alhajin ba nemanta yayi ta saba hanyar ubangiji ba ta hanayar zina ko wata bukata tashi, haifo yaro kawai zatayi kuma ta bijirewa hakan a farko amma daga karshe tayi rashin momy ku dubi condition din datake ta dade fa tana wahala in zaku tina ta dade tana aikin wahala wanda bata saba ba aiko wannan ya isa ya nuna haqurinta da tsoron Allah datake dashi, da bata fada hanyar banza ta samu kudi ba, tin sanda tayi candy take wahalar nan kusan shekaru 5)

Rumasa'u ta cika wata daya gidan Alhaji inda take zaune da matarshi da yaranshi biyu dan gidan samir da matarshi ba unguwa daya bane, cikin wata dayan tanayin waya da dady wanda mostly vedio call ne ake connecting ya ganta itama ta ganshi da wannan ta yarda aka dasa mata kwayoyin halittar samir da samira dan ta haifo musu yaro kuma tattara ta koma gidan su mai kyau na gani na fada, wani bangare aka ware mata a can ciki mai daki da falour da bandaki, ba lallai ma asan da zaman ta ba.....

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now