1⃣6⃣: Halima

1.1K 88 4
                                    


*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Abdallah ya karasa inda take tsugunne, dukda bai gane wace daga cikin yaran Alhajin ba.... Sallama yayi wanda yasata yin shiru ta dena kukan datakeyi,  ya dan tsugunna a gabanta kana yace "mene ya sameki?" bata dago ba ta girgiza mishi kai kurum,  Abdallah yayi shiru sai kuma ya dubi wankin dake gabanta yace "wannan duka nakine, ke zaki wanke?" still batace mishi komai ba,  Abdallah  shima yayi shiru sun dauki tsayin lokuta a haka, sai kuma ya miqe jin batada niyyar yin magana ya koma inda yake zaune,  shiruu bai karajin komai ba,  ya tashi ya koma dakinshi, zanen dayayiwa Rumasa'u ya dakko yana kalla,  gidane mai kyau ya zana bamai girma ba kuma ba dan karami ba,  ya dauka ya manna shi a bangon dakinshi inda babu wallpaper dan sosai gidan Alhaji Abdallah yasha decoration,  Abdallah ya fito da kayan aikinshi, yanaso ya zana fuskar Rumasa'u, saidai baisan ta ina zai fara ba..... Ana haka yaji hayaniya da alamar shigowar mutane hakan ya tabbatr mishi Alhaji ya dawo gidan,  daga tafiyar dayayi dan ya lura ba mazauni bane,  miqewa yayi ya bude window din dakinshi,  saidai window din garden yake kalla ba driven din gidan ba balle yaga motocin,  giftawar mutum Abdallah ya gani alamun wucewa da sauri amma baisan  ko waye ba,  har ya saki labulen kuma sai ya hangesu,  Halima ce da hajiya lami,  suna barin garden din,  Abdallah ya tsaya yana kallonsu da mamakin me sukeyi,  kurawa haliman ido yayi dukda su basu ganshi ba,  ya tabbat dazu itace ya gani
Har suka wuce bai dena kallonsu ba,  saida suka bace mai dagani tsayin lokuta sannn ya koma ya zauna,  yana tunani,  saboda a yadda ya gansu kamar wasu marasa gaskiya,  hajia lami sai jan Halima takeyi su bar gurin da wuri kamar sunyi wani abu na rashin gaskiya,

Zaune suke a dining, Alhaji Abdallah  yace wai hajia ina yaron nan ne, tace yana daki mana kamar wata mace ai baya qaunar fitowa ko kadan,  Alhaji Abdallah  da kanshi ya shiga dakin Abdallah yana zaune yana rike da simcard a hannu yana tunanin yaushene zai samu waya,, bayaso Rumaisa ta kira bata sameshi ba, saida Alhaji ya dafashi sannnan ya sauke ajiyar zuciya ya dawo daga dogon tunanin daya fada na Rumaisa,  tsugunnawa Abdallah  yayi har kasa ya gaida shi kamar zai tsaga tiles din ya shige dan ladabi,  Alhaji yayi murmushi yasa hannu ya dagoshi,  yace "ya kake? Ya jikinka?" Abdallah yace Alhamdulillah  na warware yanxun ai, yace to fito falour muyi dinner,  Abdallah yace to sam bai qaunar musu ko tsayawa juya magana,  aamma shi yasan dai ba'a falour yake dinner ba, ko yaushe a dakinshi yake harkokinshi,  bai fiya zuwa bangaren cikin gidan ba,

Suna zaune suna dinner, saidai daka kalli Abdallah kasan a takure yake,  bayan sun kammala ne,  Alhaji ya ciro wani kwali ya miqawa Abdallah,  yace "gashi" Abdallah ya karba yana neman karin bayani, Alhaji yace "kyauta ce na kawomaka ta tafiyar danayi,  bude ka gani waya ce,  naga kana da sim card ne amma baka da waya shiyasa na kawo maka, wani dadi ya dira a zuciyar Abdallah, lokaci daya yaji matsananciyar qaunar Alhaji ta shigeshi,  nan ya soma godiya kamar baze dena ba, har saida Alhaji yace ya isa haka Abdallah..... Alhaji da kanshi ya sakawa Abdallah  simcard din cikin wayar sannn  ya koya mishu wasu en abubuwa gameda da wayar,  number Alhaji ce kurum cikin wayar, Alhaji ya dubi hajia lami yace hajia da wanne suna kuke kiranshi ne?" inda inda ta fara Alhaji yace "kinsan sunanmu daya dashi" Abdallah da mamaki ya kalli Alhajin ashe sunansu daya bai sani ba, watakil ita kanta hajian ma bata sani ba dan da alama bata damu ta sani dinba,  shi Alhaji ya dauka akwai wata alaqa mai karfi a tsakaninsu ne, charab hajia ta samu idea tace "ai Amir muke kiranshi Alhaji", Alhaji yaji dadi a ranshi,  Alhaji yace to madalla hakan yayi,,,, Alhaji bai sake zama ba kwananshi uku ya kuma tafiya,  kuma ya tabbatr musu wanann tafiyar zatayi tsayi dan zaiyi kusan 2 to 3weeks bai dawo ba,  cikin kwanakin da Alhaji yayi Abdallah  har wani special treatment  yake samu, 

Rannan Abdallah  na zaune a garden dan tunda ya ganewa nan shikkenan ya samu gurin zama, zaman kadaici duk ya gundureshi,  yanaso yaje gidansu Rumaisa  ko zai samu wani abu gameda ita, akalla hakan zaiyi mishi dadi, gashi tunda Alhaji ya bashi wayar yake rike da ita har yau bata kirashi ba.... babu zato babu tsammani wayar dake hannunshi tayi ringing, da sauri ya dauka kamar yadda Alhaji ya koya mai ya furta Rumaisa? " sanda ya dauki kiran saidai a maimakon yaji muryar ruma sai muryar wata mata daketa turanci, hakan ya tabbatr mai kamfani ne suka kira,  wani irin mugun bakin dogon tsaki Abdallah yaji zuciyarshi kamar ta fashe dan haushi badan yana tsoron batawa Alhaji rai ba da sai yayi cilli da wayar nan, ya miqe a fusace yayi cikin gidan, saida Abdallah ya kai tsakiyar falourn sannan ya tuna ashe ba nan ne bangarenshi ba,  juyawa yayi dan ya fita amma sai ya hangeta ta window a tsugunne a kitchen din kanta a sunkuye amma ya tabbata kuka take, takawa yake a hankali har ya karasa inda take bata sani ba,  sai faman ajiyar zuciya take saukewa, a hankali ya tsugunna a gabanta yace "Halima ", a dan firgice ta dago tana kallonshi,  fuskarnan sharkaf da hawaye, ta saka dan skirt dinta tana goge hawayen da sauri, tunda yazo bai taba jin tayi magana ba,  sabanin maryama da take da fada sosai,  kusan kullum sai tayi rigima da masu aikin gidan
Halima ta zubawa Abdallah ido da tsoro kamar wacce taga zaki zai cinyeta... Miqewa tsaye tayi sai kuma ta juya dan tafiya, cafkota yayi da sauri,  sai ta saki kuka, ta juyo tana kallonshi kuma tana kukan, gabadaya kana kallonta kasan a tsorace take sosai, a take kuma ta saki doguwar ajiyar zuciya sai ta tafi luuu, ta fadi jikin Abdallah

*Banyi editing ba,  kuyi haquri yanxu typing din wahala yake bani saboda na chanja waya ne yau,  so bansaba da sabon keyboard  dinba* #onelove masoyana

*UNIQUE ONLINE WRITERS  FORUM*

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now