0⃣4⃣: girl with the beautiful smile

1.7K 104 1
                                    

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

dakinta ta shiga ta fada kan gadon ranta duk babu dadi, tunani ne ya fado mata rai, ta miqe ta fada bandaki tayi wanka ta chanja kaya zuwa wasu kananun kaya, riga da skirt blue da dan ratsin yellow ko ina a rufe a jikinta ta yafa gyale ta fito dukda karancin shekarun Rumasa'u amma saida tayi looking attractive, kasa ta sakko ta tarar da momy inda ta barta batayi mata magana ba itama momyn bata damu ba, ta wuce dining ta debi abinci taci ta dubi agogon daya sha ado ajikin bangon falourn dake walwali hasken kwan fitila ya kara haskawa, karfe 12 na safe ne yanxu, gurin momy ta karasa tace "momy zanje gidansu mufida daga nan zamuje park kuma musha ice cream" momy tace da ita "to sai an dawo" dama tasan amsar kenan, tunda sun saba din sukan fita da mufida, Rumasa'u ta koma sama taje ta debi abinda zata buqata ta feshe jikinta da turare,ta sakko tayi wa momy bye bye, itama momy sama sama ta amsa ta duk hankalinta yana kan tv din da ake wani show na Enterprenuer daze kara habaka business dinta. kai tsaye gidansu mufida driver ya wuce da ita, kamar ko yaushe momyn mufida tana kitchen tana aiki domin akwaita da kaunar girki, ta wuce dakin mufida straight, a kwance ta tarar da ita tana kallo, mufida ta miqe da murnarta ta rungume Rumasa'u, itama Ruman ta rungume bestynta tana jindadi a ranta kamar an zare mata duk wani bacin rai, tana jin dadin yadda mufidan ke nuna mata qauna, mufida da dariya tace "yanxu nacewa momy zanje gidanku mu fita shan iska tace babu driver ko daya a gida ashema kina tafe kamar kinsan weekend din baimin dadi saboda babu ke kamar ko yaushe" Rumasa'u tace "mufida wani guri nakeso ki rakani" a tunanin mufida wani sabon gurin shaqatawa ta samo musu da azama mufida ta dora after kan riga da wandon dake jikinta bata dade dayin wanka ba, Rumasa'u tace "bari naje mu gaisa da momy kafin ki gama saiki sameni a falo, daga haka ta fice zuwa kitchen din, Rumasa'u na qaunar momyn mufida saboda yadda take faran faran da jan yara a jiki, kamar ko yaushe suka gaisa da dumbin farinciki a fuskar momyn, suna nan kitchen din momy na yiwa Ruma hira tana jefa en nasihu a ciki yadda kwakwalwarta zata gane mufida ta karaso, momy ta dubeta ganinta shirye cikin black after tayi rolling, "sai ina kuma?" Rumasa'u ce tace ma momyn ai fita zasuyi, momy tace to yanxu karfe 1 ta kusa kuje kuyi sallah saiku zo kuyi lunch sannan rana ta fara sanyi sai ku fita" babu musu kuma sun gamsu, suka koma daki... saida sukayi sallah sukayi lunch tare gabadaya su ukun, sannan suka wuce da drivern Ruma tana jaddada musu kar su dade, Rumasa'u ce ta kwatanta mishi inda zai kaisu, mufida ta kalleta da mamaki, Rumasa'u tace "mufida inaso naje nayi mai bayani ne bazeyu ya dinga yimin kallon barauniya ba, nakasa jure irin bakaken maganganun daya fada akaina, Allah ya sani har zuciyata taimakonshi nakeson yi" mufida ta dafata tace nasani Ruma.... bakomai muje nima nayi mishi karin bayani, suka karasa har kofar gidan su Abdallah, Rumasa'u ce a gaba mufida nabinta a baya suka shiga gidan, a tsakargida mama na zaune gefenta kuma Abdallah ne yayi tagumi kamar me tunani, duk sunyi shiru shi ko shigowarsu ma baiji ba, sallama sukayi mama ta zuba musu ido tana kallonsu, ya mike da hanzari yana kallonsu, da dan fada fada yake tambayarsu meya kawosu?, mufida dake tsaye kusa da Rumasa'u ta soma kwararo mishi bayani "haba Abdallah mufa zuciyarmu a wanke mukazo gareka domin mu taimakeka, haduwarmu dakai ba mune muka tsara ba, hadin ubangiji ne...  ya turomu rayuwarka ne da wata manufa a boye, Ruma duk ta damu kan abinda ya faru, kasani bafa sato kudin nan tayi ba, cikin kudinta ne ta debi kadan daga ciki wanda hakan sam bai rage komai ba daga irin tarin dukiyar da Ruma keda ita", zantukan da mufida ta fadi yanxu suka saka jikin Abdallah yin sanyi, yace su zauna, ya nuna musu kan wata tabarma, suka zauna... Ruma da kanta ta fada mai itadin wacece bata boye komai gameda gidansu ba da yadda ta taso cikin kadaici sanin da tayi shima bai boye mata komai ba, mufida ta dora "Ruma tana da son jama'a tana jansu a jiki shiyasa bata taba kyamar wani ba... ita haka take" Abdallah ya kalli Ruma yanajin haushin irin yadda ya gaza fuskantarta,, Ruma tace "haduwata dakai tasa na dauka wani aikin lada ne zanyi idan na taimaki rayuwarka wanda nima zan karu dakai ko ba yanxu ba in one way or the other" a sanyaye Abdallah yace "kiyi haquri Rumaisa, saboda mummunar fahimtar da nayi miki" Ruma wani kyakkyawan murmushi ya subuce mata ko ba komai ta wanke kanta daga kallon barauniya da yayi mata, Abdallah ya zuba mata ido yana ayyana yadda murmushinta keda kyau itace mutun ta farko dayake kaunar yaga murmushinta saboda kyanshi, hira suka danyi sannan sukayi mishi sallama suka fito, ran Ruma fes wasai tamkar ta sauke wani kaya me nauyi data dauka, ice cream kawai suka biya suka siya suka sha a hanya suka koma gida, mufida suka ajiye tayiwa momy sallama ta wuce, hankalin Ruma a kwance ta cigaba da harkokinta,
monday
Ruma ta fita school da lunch box dinta biyu, bisa ga mamakinta tana karasawa ta tarar dashi a inda ya saba tsayawa, da sauri ta karaso gurinshi ta gaidashi sannan ta miqa mishi lunchbox din, ya amsa yana mata dariya yana kallan jerarrun fararen hakoranta dake shining, (Rumaisa  the girl with the beautiful smile ever) daga nan ta juya ta wuce ciki saboda kar ta makara yabita da kallo yana murmushi, shima ya koma ya kaiwa mama abincin gida,, da aka tashi a school ma Ruma na zaune zaman jiran driver sai kuwa gashi ya karaso inda take, ya zauna kusa da ita yace "yauma ba'azo daukan naki ba har yanxu" Ruma ta gyada mai kai jin annashuwa a ranta" lunchbox din ya miqa mata yace nagode sosai Rumaisa hakika kedin haske ce, zuwanki rayuwata karuwata ce nagode Rumaisa" Ruma na kaunar taji ya fadi sunanta kamar yadda shikuma yake kaunar yaga tana murmushinta mai kyau da tsada, aikuwa ta murmusa din, sai ta ciro littafi a jakarta tace yau zamu fara karatu, yace da ita to, A.B.C.D suka fara tanayi suna dawowa baya, a take kuwa ya gane tun daga A har Z saboda da waka takeyi mishi sannan ta rubuta mishi a takarda tace yaje yayi revision kafin gobe, ya karba yace da ita to, shiru ne ya biyo baya sai kuma tace "ya Abdallah nikuma me zaka dinga koyamin" yayi murmushi yace "Rumaisa aike kinada komai nine banda komai" ta girgiza kanta "yauwa dama kace kana zuwa makarantar Allo kaga nikuma ban iya komai ba, sai ka dinga koyamin karatun islamiya" Abdallah yaji dadi sosai a ranshi, hankali da nutsuwa kam Rumaisa tana dashi dukda karancin shekarunta yace "to angama insha Allah" tayi mai dariya, sai yace "meyasa kike cemin yaya?" Ruma babu wani nuku2 tace "saboda babban burina shine na samu kani ko yaya, sai kuma na hadu da kai, shiyasa na baka wannan damar" Abdallah yayi shiru yana nazari sannan yace "to shikkenan insha Allah zan zama yayan da zakiyi alfahari dashi yayan da kikeson samu" haka sukayi ta hira har akazo aka dauketa tayi mishi bye bye ta tafi

Sharee🙏🤝
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now