1⃣7⃣: New school

1.3K 119 2
                                    


follow Ayshab Nasir @ wattpad

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Da hanzari Abdallah ya rikota yana jijjigata hadi da matsanancin tsoro,  ruwa yasamo ya dan yayyafa mata a fuskar,  numfashi mai nauyi ta sauke kafin kuma a hankali ta samo bude idonta, karantar ta Abdallah yakeyi,  ya lura tanada zurfin ciki,  haquri,  sannan kuma akwai zuciya, koda halima ta bude idonta ta ganta a jikin Abdallah  tayi saurin dagowa, a hankali  Abdallah yayi mata murmushi,  itakuma ta tsaya tana kallonshi, daga nan kuma sai yayi ficewarshi abinshi haka dai tayita binshi da ido yana tafiya har ya bace mata da gani,  kafin ta kifta idanunta,

Bayan kwanaki biyu, Abdallah yana nan rike da wayarshi yana fata Rumaisa  ta kirashi koda sau daya ne,  ya fara karaya cewar bazata kirashi dinba,  idan ya tuna hakan yakanji ranshi yana baci, Abdallah na zaune a dakinshi yana juya wayar hannunshi, aka turo kofar a hankali,  daga ido yayi yana jiran ganin wanda zai shigo,  halima ce ta shigo sim-sim da ita kamar wacce  aka koro, Abdallah  yace "halima ya akayi? " ta zuba mai en idanuwanta na yara batace komai ba, shima kuma sai ya tsaya yana kallonta, dakyar ta bude bakinta tace "ya Amir wai wai ammm.... Wai momy tace ka fito ka dinga daukan abincinka da kanka babu mai sake kawo maka" tana gama fada ta fita,  ya bita da kallo,  sannan  ya mike domin cika umarnin momy,  ta kofar baya yabi ya shiga kitchen din,  masu aiki sai fitar da abincin suke zuwa dining, daya daga cikinsu tana ganin Abdallah tace ga abincin naka nan,  ta fada tana nuna wani wulaqantaccen kwanuka guda biyu a jere a jafita abinci dan mitsil wanda ya tabbata ko dan shekaru 8 abincin baze isheshi ba balle shi, ya sa hannu ya hada duka kwanukan biyu ya diba,  sai yaji tana cewa "kai baka ganewa ne wai,  dayane naka daya na halima ne" a mamakance yake kallon mai aikin dake mai jawabi wacce ta cika kwanon gabanta da abinci tana kai lomomi,  yace tayaya wanann zai ishi halima balle ni? " to umarnin hajia ne da kanta kuma ai ita Haliman tasan haka ake zuba mata kullum" suna haka ne saiga haliman ta shigo, straight ta karasa gunda abincin yake ta dauka,  tabi ta gefen Abdallah ta wuce ta kofar baya, mai aikin tace "to kadai gani da idonka ko? " Abdallah yace "to ina na maryama ita? " mai aikin tace "wannan  ai sarauniya ce, bakaji bama daga sunanta, maryama sarauniya",,,, kan Abdallah  gabadaya ya daure,  yabi jnda halima tabi da sauri
A gurin flowers  din gidan ya tadda ta tana zaune da kwanon abincin a gefenta, ta hada kai da gwiwa,  Abdallah ya karasa gurinta,  yarinya da ita amma tunani sunyi mata yawa,  sallama yayi daya karasa,  halima ta dago tana mai wannn kallon nata,  Abdallah yace "kinga nima irin abincinki aka bani" ya fada yana nuna mata kwanon abincinshi,, halima ta kalli kwanon kawai ta kauda kai,  a ranshi yace ita wannan bata murmushi ne, sai kuma yace "halima meyasa ake bamu abinci irin wannan?  Maryama kuma ake bata mai kyau kuma dayawa? " kamar ya kunnata kuwa ta soma yi mishi bayani da alama abin ya dade yana damunta kuma ta rasa wanda zata amayarwa da abinda ke damunta,
"Ya Amir momy batasona kuma kaima batasonka,  tafison mary.... "tun bata karasa  ba ya katseta "wace mary? " halima tace "maryam nake nufi bataso ace mata maryam,  indai nace mata haka saita zaneni da bulala kuma momy batacewa komai,  shiyasa banace mata, saboda banaso ta dukeni,  kuma momy tace ni ba 'yarta bace ni er riko ce,  amma dady yace nida mary duka yaranshi ne,
Abdallah ya kura mata ido yana mamakin lamarin dake gudana cikin gidan,  me hakan ke nufi kenan? Dagaske halima ba diyar momy bace?  Kodayake a bayyane abin yake.... Abdallah  yace to meyasa kike kuka? Halima tace yunwa nakeji kuma abincin baya isata,  tausayunta ya baibayeshi har cikin ranshi ya dakko kwanonshi yace gashi ki hada duka na baki,  halima ta karba cike da jindadi ta somaci tana mishi murmushi, shima ita yake kallo da tausayinta fal ranshi....

Kashegari, Abdallah na zaune gurin teburin karatun dake dakinshi, yana rike da pencil da eraser yanaso ya zana fuskar Rumasa'u, sai yajiyo motsi alamar faduwar abu,  da dan hanzari ya karasa bakin window din ya yaye labulen yana kallon gurin yanaso yasan mene ya fadi amma bai iya hango komai,  ya ajiye pencil din hannunshi sannan ya fita waje ya zagaya baya, 

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now