3⃣1⃣: Unexpected

1.2K 99 5
                                    


Bayan watanni biyu

Kadaici ya damu Rumasa'u, tun barinta gidansu khalil, bata gane irin yadda take missing Abdallanta ba saida ta dawo coffee shop, sanda take gidansu khalil yana debe mata kewa, ko ba komai hakan na rage fadawarta tinani koyaushe, aikin datakeyi yanxu yanayi mata dadi, takan rage damuwarta a duk lokacin dataji tunanin Abdallan ya fado mata saita kunna waqar da khalil ya turo mata IWILLNEVERFORGET sanda ya siya mata waya wannan takan kara tsuma zuciyarta sosai, abu daya dayafi damin Ruma shine rashin sanin halin da khalil ke ciki dan tasan koma a wanne hali yake to itace ta jawo mai, Rumasa'u itama ringing tone din wayarta shine wanann waqar dukda bata da me kiranta din,

Xxxxxx

Ta ajiye jakarta cikin dakin sannan ta subale takalman nata, kan gado ta fada saboda wata uwar gajiya data kwaso daga makaranta, saida ta dan huta sannan ta shiga wanka, ta watsa ruwa, koda ta fito karfe 3 ne na rana, "yau kam insha Allah se naje nasha coffee dinnan" ta fadawa kanta tana mai sake tabbatrwa kanta hakan, yanxu watanni na nawa rabonda naje? Uhhhh boko ta rikeni" ta fada tana tuna sanda take da freedom kafin ta fara jami'a.... Ta kammala shiryawa cikin kaya masu saukin nauyi dazatayi harkokinta a cikin gida kafin bayan magrib ta fita shan coffee, falour ta fito ta tarad da maryama taci ado ta hakimce kan kujera tana kallo, halima ta wuce dining ta debi abinci kadan ta zauna ta fara ci, tana kai loma ta uku taji horn, kallan kallo sukayiwa juna itada maryama, kafin kace me har motocin sun shigo, lokaci daya suka hada baki dady? Fuskokinsu da alamar tambaya dan dady bayayin zuwan bazata indai ze dawo to ze sanar, momy ta fito falourn itama, irin mamakin da fuskokinsu ya dauka haka itama nata wanda ya sanar dasu lallai bata san da dawowar dadyn ba itama, suna nan tsattsaye kofar falourn ta bude, dady ya shigo yana musu dariya yadda duk fuskokinsu suka bayyana alamun mamaki karara, shigowa yayi yana fadin akwai bako a waje halima jeki shigo dashi, "shine kuma baku shigo tare ba" cewar momy ta dora "gashi bamu girka komai ba kuma kai da bako ne" dady ya sake murmushi da alama yana cikin nishadi, karki damu, halima ta fita dan cika umarnin dady

Yana tsaye jikin mota, ya lankwashe kafa daya hannayenshi suna boye cikin aljihun wandonshi, fararen kayanmu irin na gida ne, saidai ya juya mata baya, halima ta karasa da sallama sannan tace "ina wuni, " bai amsa ba kuma bai juyo ba, ta sake cewa "dady ne yace na shiga dakai ciki" wani turn yayi yana mai dora yalwataccen murmushi a kyakkyawr fuskarshi, baya halima taja da sauri lokacin da tayi ido hudu dashi, wani kara ta kwalla lokaci guda ta daka tsalle sosai ta daneshi tana mai tsananin farinciki da murnar ganinshi sanda bata zata ba, bata fuska yayi yana shan kunu yace "kefa tsiyata dake kenan wlhy har yanxu baki girma ba sakeni karki ballawa Ruma miji" lokaci daya jikin halima yayi sanyi ya tina mata da abinda ta mance, ya tuna mata shidinfa baze taba zama na wata ba idan ba Ruma ba, kwalla ce ta taru a idonta, ta hadiye tana mai maida kwallar sannan taja baya tana yake ranta babu dadi "yanxu fa idan ban bata lissafi ba shekarunki 18 ko halimatu? " ta daga kai ta kalleshi dan ya kereta a tsaye, har yanxu baka mance da kirana da wannan suna ba, yayi dariya kadan yana ayyanawa a ramshi yanxu itakuma Ruma ta cika shekaru 20 kenan, zanso naga Ruma, naga yadda ta koma data girma nasan ta sake kyau ba kadan ba, shekaru 8 kenan da rabuwarmu" duk wannan surutan cikin zuciyarshi yakeyi, halima ma ta fada nata tinanin haka suka jera har falour kowannensu da nashi sake saken, ba momy ba, har maryama saida ta yaba da zallan kyau da wayewa, iya daukar wanka da ado, jan class da dattako na Abdallah, halima da Abdallah sun cigaba da harkokinsu kamar da, sunsha hira, seda dare hafiz yazo inda Alhaji ya hadasu dan su san juna..... A ranar halima fasa fitar tayi ta bari sa je da ya Amir dinta idan ya gama huce gajiyarshi,  kashegarin ranar Alhaji Abdallah ya kira meeting na gaggawa bayan tattaunawa da sukayi da hajiya lami (momy),

Dukka yaran suna kasa, Abdallah na gefen dady, maryama na gun momy, halima kuma gefen Abdallah hafiz gefen maryama, fuskar dady kadai ta isa sanar dakai muhimmancin taron daya kira, tsit dakin yayi babu wanda yayi magana kusan shudewar dakiku da dama, dady yayi gyaran murya sannan yayi sallama muryarshi a raunane wanda hakan ya sake karyar da zukatansu banda hafiz da maryama da ba damuwa sosai tayi ba,, a hankali cikin murya mai taushi dady ke magana
" na kiraku wannan taro a wannan lokaci, kusani duk abinda zan fadamuku mai muhimmanci ne, kuma komene zan fada ku dauki hakan matsayin kaddara ga wanda ya shafa.... Haqiqanin gaskiya halima ba diya ta bace, ma'ana ba nine mahaifinta ba kamar yadda ba lami ce mahaifiyarta ba" a hanzarce Abdallah ya dago yana duban Alhaji yana mamakin wannan furuci nashi, cikin kwayar idonshi ya kalla inda ya gane shi kanshi baiji dadin furucinshi ba.... Abdallah ya maida dubanshi gun halima, amma bai gane mene ke faruwa a nata bangaren ba domin kuwa kanta na kasa ne bata dago ba kuma bata motsa ba, halima innalillahi takeja domin ta samu sassauci cikin zuciyarta, maryama kuwa wani fadi take kanta na kara girma
"dalilin dayasa na tona wannan sirri shine a bisa maganar da hajiya lami tazomin da ita kan zamu hada auren halima da yarona hafiz kuma ta tambayeshi ya amince ," numfashin halima ne ya dauke na lokuta da kyar ta samu ya dawo kafin ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya "wata sabuwa" shine furucin da Abdallah yayi
"amma bazan taba takuraki ba halima bazan miki auren dole ba, idan kinga kun daidaita to falillahil hamdi, idan ma baku daidaita ba to karki wani damu haka kuma idan kinada wanda kikeso to ki fitar keda maryama dan na aurar daku nima hankalina ya kwanta........ " wannan kenan

"saura ke maryama, ki sani kema ba diyata bace, keda halima dukkanku marayune na daukoku na rike, na kasance mutun mai sha'awar rike yara marayu musamman hadisin manzon Allah (SAW) dayake cewa, "gidan da Allah yafiso shine gidan dayake akwai maraya kuma ake kyautatamishi (karramashi)", haqiqa ni na yarda ko arzikin da Allah yayimin saboda kyautatawar danake wa maraya ne, ita sadaka bazata rage komai a cikin dukiyar dayanku ba saidai ma albarka da yalwa da zata kara mata,  tsakanin maryama, halima, Abdallah da hafiz ni duka daya na daukeku kar dan kunji wannan sirri ku sakawa ranku wani tinani, dukkanku yarana ne, naga dai lokaci yayi daya dace kusani ne.... Wannan shine kawai" idan da me tambaya ze iya yi"

Jikkunansu duka sunyi sanyi, ya kuka ganemin maryama, kwalla kurun take gogewa a ranta tana fadin ita kawai an cuceta da ba'a barta gidan iyayenta ba, halima kuwa tawakkali tayi da ganin kokarin dady sosai, shirun da akayi yasa dady sallamar kowa yana mai sake musu nasiha kan kada su saka abin a ransu kuma yace da halima tayi tinani kan shawararsu ta kula kar tayi abinda zatayi nadama......

Topa, me karatu ko me kake gani halima zata amsa? Zata duba abinda dady yayi mata ta amince da auren danshi na boge?  Ko kuma hakan zesa ta auri danshi na asali😁
Soon soon Ruma da Abdallah 😍..... heart u all

Not edited👏

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Kde žijí příběhy. Začni objevovat