3⃣6⃣: Baby

1.3K 108 7
                                    

Ya fito daga dakin a zuciye ranshi na tafarfasa, da sauri ta biyo bayanshi hawaye suka fara zuba a idonta, cikin murya mai kaushi da bacin rai tsantsa yace "mun riga munyi yarjejeniya nidake babu wata alaqa tsakanina dake meyasa kike maida hannun agogo bayane",,,cikin shessheqar kuka da takaici halima tace "ya Amir mene laipina a matsayina na matarka dan na nemi ka bani haqqina bayan aurenmu da wata guda ba tareda wani mu'amula ba" Amir ya dubeta ya cilla mata wani kallo mai wahalar fassara kamin ya juya ya fice kamar me shirin tashi sama dan yasan idan ya kara mintuna a gurin yana iya rufeta da duka dan haushi,,,, a gurin ta durqusa tana rera kuka, ta dauka abu ne mai sauki karkato da hanklin ya Amir, ta dauka idan anyi aurensu ba yadda zeyi dole ya sota, ta dauka ze fada tarkonta ne idan tayi amfani da jikinta kamar kowanne namiji, "wai mene Ruma kike dashi wanda bani dashi,,," ta furta tana mai cigaba da kukan.... Ashe ya Amir ba haka yake ba, ashe shawo kanshi ba abu ne mai sauki ba, nikuwa nace 'Ai halima ita soyayya bafa karya bace', nan halima taci kukanta ta koshi ta gode Allah......  A nashi bangaren kuwa motarshi ya figa ya bata mai ya dinga tsula gudu a titi batareda sanin gurin zuwa ba. Ya dade yana tafiya daga baya kuma dan kanshi ya tsaya kamin yasa hannu ya bugi sitiyarin ya kwantar da kanshi kan sitiyarin yana furzar da iska mai zafi wacce take fita daga zafin zuciyarshi
Ruma a nata bangaren tana nan tana rainon jaririn cikinta ba laifi a dan zaman da tayi a Abuja yasa ta sake murmurewa ta soma maida jikinta hasken fatarta kuwa har yafi nada.... Ta dan fito daga falourn tana kallon tsarin gidan, babban gida ne sosai wanda yaro kamar samir da be wuce shekara 30 da doriya be kamata ace ya mallaki irinshi ba duba da yadda kasar tamu yanxu ta sauya, aiki yayi wuya, ga tsadar rayuwa amma sanin mahaifinshi ne yayi mai yasa Ruma tsuke bakinta, kofar dake kallon kofarta ta bude, wanda ya sadata da wani wargajejen falour an mishi ado da creamy sky blue mai taushin kallo, Rumasa'u ta rike haba tana kallon dukiya, tana tsaye a bakin kofar ta dan ji hayaniya daga can ciki sai kuma taga samira ta fito sai jaraba takeyi, Samir ma ya biyo bayanta, "wai meyasa kai ka cika takura ne fitar ma shikkenan se ka hana ni to bazeyu ba gaskiya a garke ni a gida" ta fada tana yafa wani siririn gyale wanda sam be dace ko budurwa ta yafa ba balle matar aure, basu lura da Ruma dake tsaye ba dukkansu Ruma kuma ta karewa samira kallo, wasu matsattsun riga da skirt ne a jikinta kanta yasha attach amma ta daura dankwali dukda ta fidda gashin attach din na kananun kitso, tasha hills kamar ta taka ya balle sai kuma jakarta designer dake makale a tsintsiyar hannunta, Ruma ta maida kallonta gun Samir dan taga reaction dinshi, amma ga mamakinta sai taga ya kwantar da murya a kasalance kamar maijin bacci yayi maganar dako Ruma dake bakin kofar falourn bataji me yace ba, tadaiga samiran ta daga kafada alamar ko oho sanann kuma ta nufo kofa, a lokacinne samiran da Samir dayabi samira da kallo suka lura da tsaiwar Ruma a gun, samira ta kalleta sama da kasa ta yatsina fuska ta fita ta wuce ta gefenta, Ruma ta maida kallonta gun Samir wanda shima ita yake kallo... Dan kanta ta juya ta fita ta barshi a nan....... Bayan wasu kwanaki, Ruma na zaune a pool section na gidan tana kallan ruwan cikin da iska ke kadawa,,,  tinanin rayuwarta takeyi da zaman da take a gidan Samir, Ruma ta dan lumshe ido tana karanto abinda ta fuskanta acikin gidan a dan zamanta,  Samir... Samir mutunne mai saukin kai irin mutanen da sam basu da damuwa basu san me sukeso ba ko mene basa so, basu dau duniya da zafi ba zaka iya cemai dolo ma musamman la'akari da yadda samira ke juyashi tana garashi....  Samira?, samira kyakkyawa, er gayu iyayen ado, son zuciya,  son kanta gashi bata ragawa Samir ko kadan kuma duk abinda zatayi sedai yayi mata magana cikin lumana da maslaha tamkar beda nashi ra'ayin, danko ya fadi ra'ayinshi ma bayayi mata, kuma dole ya haqura yabi nata, Rumasa'u ta sauke numfashi sanda tazo nan a tinanin.... In zata iya fada a takaice a abinda ta gane shine, Alhaji dan'ada da iyalanshi suna juya Samir ne kamar wanda besan right dinshi ba, yasa hannu ya miqo mata lemon juice, Ruma ta dago ido tana kallanshi, kafin ta dan saki fuskarta tasaka hannu ta amshi leman batareda ta dauke idanta daga kallanshi ba, sai tace "ina yini" murya can ciki yace anyini lapia momy" tayi er dariya dan yana cemata hakan idan yanaso ya tsokaneta,samir kam ba ruwanshi a nashi bangaren shima tsananin tausayin ruma yakeyi dan yasan ba karamar sadaukarwa zatayi ba kuma babu diya mai gata da zata yarda da wannan lamari....

Bayan watanni 8

A hankali hawayen ke zuba daga kwarmin idonta tana mai kankame hannunshi cikin radadi da zafin ciwo, tana kwance kan gadon marasa lapia har an chanja mata kaya aikin kawai ya rage a fara dan likitoci sun tabbatar bazata iya haihuwa da kanta ba cos she's a virgin, samir yayi wani dogon tsaki ganin yadda tun dazu likitocin sai kame kame sukeyi ya karasa gun dayansu daya tabbatr shine babba danjin meya hana a fara aikin ko se dan ya mutu a cikinta.... Likitan yace kayi haquri da munso mace tayi mata ne kuma tun dazu muke jiran zuwan.... Zancen nashi ya katse saboda karasowar da wata kyakkayawar likita tayi dagani kasan yarinya ce karatun tayi da wuri ne kawai ta dan gyara zaman Theatre dress dinta sannan tace "im really sorry" sai kuma ta kalli doctor "an gama shirya patient din" suka mata alama da eh daga nan duk suka wuce zuwa gun ruma wacce already she's set kuma zafin ma ragu, an saka abu a tsakiyarta an raba jikinta biyu, inda likitocin zasuyi aiki daban da kuma samanta, likitoci sun bawa samir shawara ya zauna yanayi mata hira, a haka har aka kammala aikin batareda dr din datayi aikin taga fuskar patient dinta ba.....Baby girl aka cirowa Ruma santaleliya tubarkallah.....

I promise Ruma zataga Abdallah a next page dan namaso su hadu a wannan page din to amma banyishi da tsayi ba saboda bansamu ishasshen time ba kuma banaso na bari banyi muku typing ba bahaushe yace da babu gara ba dadi........ But still ba lallai ne ku samu update gobe ba cos schedules dina na gobe dayawa wlhy but still i will try..... Thank you, i really appreciate each and everyone of u dayake bibiyar littafinnan Allah ya kara zumunci
#not edited

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now