2⃣1⃣: It all started

1.2K 93 2
                                    

♥💍 ZUCIYAR ABDALLAH💍♥

follow Ayshab Nasir @ wattpad

#Hausanovel #Unique #love #Happyending #seperation #loneliness #sacrifice #lovetragedy #lovetriangle



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Haka suka tattara aka kai dady zuwa asibitin dake kusa dan samun taimakon gaggawa,  momy ta hau zirga zirga hankalinta ya tashi ganin irin yanayin da dady ya shiga, da farko kin karbar dady sukayi,  sai daga baya kuma sukayi demanding kudi na cewar za'ayi examining  dinshi kafin a gane meke damunshi,, momy ce ta fita da sauri,  ta koma gida taje ta debi en sarkokinta,  takai ta siyar, ta gama hargitsewa, ta kawo musu.... Rumasa'u kam idan ba kuka ba babu abinda takeyi, likitoci sun dade akan dady kafin daga baya suzo su sanar musu cewar dady fa,  ya samu stroke ne,  shanyewar barinjiki kuma is worst sosai,  inda hali a fiddashi wata kasar, zaifi samun sauki sosai fiyeda anan,  kuka wiwi sukeyi, momy harda bubbuga cinya,  haka suketa goge majina, gwanin ban tausayi, Rumasa'u itace mai dan karfin halin yin tawakkali,  take rarrashin momy....
Amma momy ta fita hayyacinta...

To haka suka cigaba da zaryar asibiti an bashi gado,  yana dan samun taimako, dady kuwa ya zama abin tausayi sam baimasan waye a kanshi ba,  addu'a Rumasa'u takeyi mishi koyaushe saidai abin sai gaba yakeyi kamar babu wani sauki ma,  karfin imani da tawakkali yasa suke rarrashin kawunansu amma ta ciki na ciki,,,,  kwanan dady uku a asibitin momy da Rumasa'u suka yanke shawarar sallamar ma'aikatan gidan saboda sunsan yanxu basuda abinda zasu biya su,  domin en kudaden nasu sai kasa sukeyi gurin siyan magani da abincin dady,  tsakanin ruma da momy kansu ma basuyi kama da masu lpia ba, maigadi da mai aiki daya ne kurum suka rage shima dan en aikace aikacen cikin gida,,,
Watan dady daya a asbiti, amma har lokacin bai samu kanshi ba,  bai iya ko magana, momy ta fita hayyacinta, duk wani ado da kwalliya sun kare,  tayi duhu,  koyaushe cikin kuka,  saidai in bata kalli maigidan nata ba,  istigfari take kamar me?, abinda yafi bata tsoro shine yadda duk ta salwantar da en kadarorinta gurin nema mishi lpia amma abu har yanxu shiru,  tasani babu wani dan uwa dazataje tace ya bata ko asi,  dan sun rigada sun yar da wannan damar da kansu,  sunyiwa mutane kallan kaskanci a rayuwa suma yanxu ga yadda tasu rayuwar ta koma,  ashe akwai ranar da zasu rasa duk wadannan uban arzikin? Ashe akwai ranar da zatayi nadamar abubuwan data aikatawa mutane,  ashe haka akeji idan babu ta riskeka,  momy duk sai yanxu tasan da hakan,  kuma sanin hakan kan karyar mata da zuciya tayita kuka babu mai rarrashi,  saidai hakan ya kara mata imani sosai a ranta, ko bakomai ta gane wulaqanta dan adam ba abune mai kyau ba, kuma sadaka babu abinda zata rage ma dukiyar ka saidai ta kara mata albarka, hakika imani ma wani abune.....

Ana cikin wannan mawuyacin yanayin ne,  jami'ai sukazo kan yarjejeniyar da Dady yayi da banki na idan bai biya ba,  ya bada jinginar dukiyoyinshi,  sarai momy ta san da wannan yarjejeniyar dan babu abinda batasani ba kan business dinshi,  itace ma ta bashi shawarar shiga wannan bakin business dake neman tona musu asiri a duniya,

Loan din da dady yaci yanada yawan gaske,  haka Rumasa'u da momy sunaji suna gani aka karbi sauran dukiyoyin da dady ya bari ciki kuwa harda gidan da suke,  da en filayenshi harda motoci sannan aka basu notice kan suyi azamar tashi a gidan,  momy rungume Rumasa'u tayi a jikinta tana kuka itama ruman tana kuka,  babu mai lallashin wani, babu mai wata mafita,  haka sukasha kukansu suka koshi,
Momy da Rumasa'u sunsha rokon kafin suka barsu su kara wata daya a gidan, amma sauran abubuwan duk sun dauke,  abu sai ya karayi musu zafi,  zafi kan zafi kenan,  momy sai yanxune tasan tsadar zama a Abuja, Rumasa'u kuwa wani tausayin momy take da karin kaunarta a zuciyarta, yanxu tana ganin kaunar da momyn ke mata,  sai lallabata take, bataso taga bacin ranta, hakan yana karyar da zuciyar Rumasa'u,  acikin sati daya momy ta sauya kama,  ta dawo talaka,  babu ado babu gayu babu kwalliya,  ya kasamce har zannuwanta masu tsada takan kai ta siyar,  domin magungunan dady masu tsada ne,  haka kuma takan zaunar da Rumasa'u tayi mata nasiha,  musamman akan karta wukaqanta dan adam, kuma komai daren dadewa zasu nemi en uwansu,  amma ba yanxu da talauci ya samesu ba,  kuma insha Allah  wadata zata tarad dasu a gaba,,, wasu lokutan in momy na fadar hakan ruma takanyi mamaki sosai,  lallai komai ubangiji yayi akwai hikima aciki,  hakika wannan jarabawarsu ce, Allah  ya basu ikon cinyewa.....

To cikin satuka biyu zuwa uku,  dady ba laipi ya samu sauki,  akan turashi a wheelchair, kuma yana gane waye a kanshi dan yakanyi kokarin yin magana ma,,, momy na zaune kan sofa,  cikin asibitin da dady yake, dady kuma yana bacci,  Rumasa'u na zaune a kasan momy tana yima kafarta tausa a hankali a hankali,  lokaci lokaci kuma tana share kwalla saboda ganin yadda kafar momy tayi wani birtsi-birtsi kamar ba kafar da iya man da ake wanketa ma,  zai iya ciyar da wasu iyalan na fiyeda sati daya ma,,,,, momy ta rike hannun Rumasa'u  a hankali,  hakan yasa ta dago ta kalli momy,  tayi wani kala,  rana da wahala duk sun bayyana garesu duka,

Momy ta dago ruma a hankali,  ruma ta zauna gefen momy ta danyi murmushin dako makogwaro baikai ba,  momy tace "shawarace Rumasa'u nazo mana da ita,  kinga yanxu baifi saura kwanaki hudu ba,  wa'adin zaman mu cikin gidan nan ya kare....  Ruma tace "eh momy to me kike ganin zamuyi,  yanxu dai duk en kudade da kadarorin daga na dady har naki duka an siyar, har nawa ma kuma abinda ke hannu baze ishemu mu kara koda sati daya cikin garin nan ba,  duba da irin tsadar rayuwa da nan din keda ita"

Momy tace "yawwa kin dakko hanyar ganewa,  nima duk nayi la'akari da wadannan abubuwa shiyasa nakega,  meze hana mu koma kano da zama tunda can yafi saukin rayuwa,  kuma zamu samu dan aiki da zamuyi har Allah  ya kawo sanda jikin dadynki zaiyi sauki"
Rumasa'u taji wani sanyi kamar irin kana jin zafi sosai  kasha rana,  a zuba maka ruwan sanyi  ajiki,  haka Rumasa'u taji cikin ranta da jinin jikinta, sannan ta dubi momy  tace "hakika wannan itace shawara kuma mafita a garemu a yanxu a halin da muke, dan momy ko iya transport  ma wani abune a garin nan"

To da wannan shawara ne momy da Rumasa'u suka yanke hukuncin dawowa garin kano ta dabo da zama, kafin sukaga yadda jikin dady din zaiyi

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Donde viven las historias. Descúbrelo ahora