3⃣8⃣: mixed feelings:Zuciyar Abdallah

1.4K 109 15
                                    

Wani ciwo taji mai zafi a kirjinta tai saurin dafe kirjinta tana mai karanto sunayen Allah a hankali,  sai kuma taji hawaye mai ciwo dan siriri ya zubo mata, shekaru kusan goma sha daya kenan bata ganshi ba, ya sauya ya chanja gabadaya wannan dan gayu ne batareda wata wahala a tattare dashi ba kuma kyakkyawa ne, saidai duk wann baze hana tagane shi a matsayin Abdallan ta ba, Abdallah? Abdallan data bata lokuta tana jiran haduwarsu, Abdallahn datayi rejecting so many proposals saboda shi, taqi amincewa kowanne da namiji, yau Abdallah ne yama manta da ita, yayi aure, shi namiji ma ba mace ba, tafikan hannayenta biyu ta sa ta rufe fuskarta "ya'ilahi"..... tana mai jin mixed feelings, yeah mixed feelings, feeling of finally meeting Abdallah can u imagine d happiness d joy da expectations, on the other hand the disappointment of seeing him with another woman wacce ko kallan fuskarta Ruma bata tsaya yi ba, terrible feeling, heart break....... Ji tayi an dafa ta, Rumasa'u ta dago tana kallan mufida da baby wacce ke nannade cikin showel fari karr, Ruma da tuni hawayen sun kafe ta dago babu walwala sam a fuskarta, "dama wai baki shiga ciki ba kika tsaya a nan" Ruma dai batace komai ba....  Mufida ta kalli gurin "ai ban san kyawun gurinnan ya kai haka ba dayake ban taba shigowa ba" Ruma dai bata tanka ba dan batama san me take cewa ba, mufida taja hannun ruma sukayi hanyar shiga dakin, Ruma ta juyo zuwa gurin dataga Abdallah dazu amma yanxu se bata ganshi ba babu kowa ma a gurin, haka taketa waige waigenta har suka shiga dakin, kokonto ne ya fara shiga kanta"kodai ba Abdallah ta gani ba? Kodai idanunta ne ke mata gizo? Tasan Abdallan dayace itace zuciyarshi bazeci amanarta ba, da wanann ta samu hankalinta ya kwanta amma wani bangare na zuciyarta yaqi yarda bataga Abdallah ba.... Suna shiga dakin samira ta bude idonta a wahalce, tausayinta ya rufesu kaf, nurse ta miqe dan kiran likita amma samira ta riqeta alamar karta kira likita tukunna.... murya can kasa tace a nuna mata baby, mufida dake rike da baby ta matsa wajejen fuskar samira ta bude baby din dake bacci, samira ta lumshe ido gamida daga hannu da kyar ta shafi fuskarta, na barmiki ita Ruma Allah yayi mata albarka, nikuma Allah ya yafemin" hawaye masu dumi suka gangaro a idonta cikeda nadama mai tarin yawa, sai kuma ta saki nurse din data rike hannunta a hankali nurse ta fita dan kiran doctor,  Ruma ta karasa gun ta "kiyi shiru samira ki dena kuka cuta ba mutuwa bace" idanunta akan Ruma kawai tana kallanta, basu ankara ba sai ji sukayi injinan sun soma wani kara wanda da basayi, Ruma ta soma tattaba samira tana mai kiran sunanta, mufida kuma tayi waje neman likita, a hanzarce suka shigo da likitan da nurse da mufida sukayo kanta gabadaya..... Sai bayan ciwon samira ya lafa ne su samir suka shigo kamar hadin baki dukkansu a lokaci daya, yana shigowa ya karasa gun baby ya amsheta ya rungume diyar tashi, nan yayi mata huduba ya saka mata Rumasa'u, mufida da Ruma sunji dadin sunan daya sakawa babyn, sai yamma Ruma da mufida suka kama hanyar komawa suna yiwa samira fatan samun sauki, suna fitowa shima yana fitowa, kamar ance Ruma ta kalli inda yake ta kalla kuwa ta hangoshi tareda ita, "kenan idanuna ba karya sukemin ba? Dagaske wancan Abdallah ne?" jiri ne ya soma dibarta bata san sanda tayi kasa ba mufida tayi saurin tarota tana fadin Subhanallah, nan da nan nurses suka kawo agaji, Abdallah dake kokarin shiga motar ya dubi halima da har ta shiga mota yace "dan jirani kinga wata ta fadi kuma inaga patient ce, ya karasa maganar yana ajiye labcoat din hannunshi a motar kana ya karasa da sauri inda yaga ana taimakawa Ruma, nurses ya umarta su kawo gadon daukar marasa lpia, sai a lokacin ya samu karasawa inda patient din take saboda yadda mutane suka rufeta, baby na kafadar mufida itakuma Ruma na kwance kanta har zuwa haqarqarinta na kan cinyar mufidan da tayi zaman dirshan a kasa tana kokarin gane mene ya sami Ruma lokaci daya haka,  Abdallah bai ga fuskar su ba duka saboda yadda mufida ta duka tana duba Ruma yasa ta kare fuskar Ruman...

Sanda aka kawo abin dan daukar Ruma Abdallah ya sunkuyo kadan yace kawo babyn na rike miki, ba musu ta miqa mai sannan ya ja gefe, da taimakon nurse aka dora Ruma kan gadon akayi ciki da ita, mufida ta bisu Abdallah na binsu a baya, tsam Abdallah ya kama baby ya riqe yana mai jin tsananin kaunarta, ba bangaren mufida bane kuma ba bangaren su Abdallah bane hakan yasa mufida ta tsaya daga waje tunda ba field dinta bane, ganin an shiga da Ruma dakin taimako yasa ya dan tsaya daga baya ya bude fuskar baby kadan ya zuba mata idanu "fatabarakallahu ahsanul khaliq" shine kalaman daya tsinci harshenshi na furtawa, kallanta kawai yake kamar ya hadiye... Baimasan ta karaso ba se ji yayi tace "bani diyata malan" ya dago da sauri,,, amma sai yaga ta juya likita na mata bayani gameda Ruma, Ya sauke numfashi yana kallan babyn bai ankara ba ya nemeta ya rasa, ya ware idanu yana dube dube "yanxu fa ya ganta a nan amma har babu ita, ya gama waigenshi amma be ganta ba, dabara ce ta fado mai kasancewar yaga fuskar likitan da suke tare ya nufi hanyar office dinshi, yana kan kujera a zaune Abdallah ya shiga, bayan sun gaisa ne likitan yace "doc. Abdallah ina ka samo baby ko madam ta haihu ne? " Abdallah ya danyi yake kamin ya mai bayanin wacce yake nema dukda baiga fuskarta ba, Doc. Ya rike kai "ohh dr. Mufida ce iyayen shiririta, inba shiririta ba ya zata mance baby a hannun stranger.... Zauna ka jirata ko kuma ka barmin babyn zata dawo nan da mintuna kadan" Abdallah ya kalli babyn sannan yace zan jirata....

A hautsine mufida ta karasa dakin tana duban Ruma dake kwance kan gadon marasa lpian ta zuqe lokaci daya, Ruma ta bude lumsassun idanuwanta ta kalli mufida da duk ta rikice "Ruma likita yace jininki ya hau, mene ya sameki dan Allah ki fadamin meke damunki"? Ruma ta lumshe ido tana karanto siffofin Abdallanta a yanxu, a hankali ta soma fadin "dogo, fari, mai kama da Abdallah, dan hutu, amma yanada mata" mufida ta chanja fuska cikin rashin gane inda zantukanta suka dosa, me kike nufi kenan"? Ruma ta sake bude ido kamar kiftawar ido hawayen ya zubo sharrr..... Mufida ta zauna ta kamo hannayenta "Rumasa'u ki fadamin mene ne, dan Allah meke damunki" Ruma ta dafa kafadar mufida tace "kinsan dai babu abinda zan boyemiki ko? Babu abinda baki sani gameda ni ba, ki bari na tabbatr tukunna se na sanar dake please" mufida ta gyada kai kurun cikeda damuwa.....

Wayarshi tayi ringing, ya dan firgita saboda yadda ya tsirawa baby ido kuma ya lula tunani duk a lokaci daya, sunan halima daya gani kan screen din ne yasa ya tuna ya barta a mota, ya dauka yana gyaran murya, cikin sanyin murya tace ina jiranka fa ko na wuce" duk jikinshi yayi sanyi yace gani nan zuwa yanxu, ya kalli likitan yace "ana jirana bari na bar maka babyn kawai" ya fada yana shafa kan babyn cikin kulawa da kauna..... Haka ya ajiyeta kamar kar ya tafi,,,, bayan tafiyarshi da wasu dakiku mufida ta karasa office din ai tana shiga taga baby se lokacin ta tuna ma, gabadaya tinanin ta ya jagule, ta karasa da sauri ta dauketa, kamin ta kalli likitan, yayi mata murmushi kawai.....

Kin sallamar Ruma akayi likitan yace seta kwana, idan ma sunga jikin beyi yadda sukeso ba to bazata tafi gida ba, mufida tace lallai seta kwana da Ruma amma Ruma tace "a'a mufida su Abban sadiq da sadiq suna jiranki a gida akwai nurses kuma na tabbata samir zezo tunda yasan ina nan" dakyar ta lallabata ta tafi gida badan taso ba.....

Karfe 10 na dare Abdallah se juyi yake shikadai tinanin babyn dazu duk ya dameshi ji yake dama be dawo ba, kamar wanda aka tsikara ya miqe ya saka jallabiya data amshi jikinshi ta sake fidda tsayinshi, mukullin mota ya dauka yayi waje, likitan dake duba Ruma ya fito dan duba marasa lpian kafin ya tashi daidai kofar dakin da ruma ke ciki sukayi kacibus, "Ahh doctor kaine da daddare" sukayi musabiha, Abdallah ya dan shafi kanshi sannan yace "maman babyn dazu kuwa tazo? " likitan ya kalleshi "kaikam ka damu da babyn nan kodai ka santa ne"? Abdallah yace ko kadan"

Muje ka ganta... "likitan ya fada yana nuna mai dakin, Abdallah yabi likitan a baya, tana kan dadduma tana lazimi ta idar da sallah taji sallamarsu,,,, daskarewa tayi a inda take, babyn na kan gadon nannade cikin showel tana baccinta, yayinda itakuma Ruma gadon ya kareta, sunkui da kanta tayi kasa wanda ya hana suga fuskarta, Abdallah ya karasa ya dauki babyn batareda ya jira izini ba, likitan yace "Ruma ya jiki" Abdallah ya dubeshi kana ya maida kallonshi ga wadda aka kira Ruma, "Rumaisa?" ya furta, furucin nashi ya sake tabbatr mata da shidinne, Abdallanta ne, shi kadai ke kiranta da wannan salon, tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta bugun zuciyarta na karuwa...... "Ruma ya jikin? " likitan ya sake maimata mata tambayar,,,, gabadaya jikin Abdallah ya gama sanyi ya gaka saddakarwa, *the feeling of finally* ....... Is it really her?..... Shi kanshi baisan sanda ya yazo ba se ganinshi yayi a gabanta,,,, Zuciyar Abdallah? Ya fada yana cikin murya mai sanyi da jan hankali can kasan makoshi... Unintentionally ta dago, batareda tasani bama se data tsinci idanuwanta cikin nashi........

Huuuu finally... Finally, mixed feelings, zuciyar Abdallah, sabon babi ya bude
#Abdallah #Rumaisa.....

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now