4⃣5⃣: preparation

1.3K 115 11
                                    

Momy tai saurin dirowa daga inda take zaune taje ta kama kafafun Alhaji cikeda nadama a tareda ita nan ta soma magiya tana matsanancin kuka, wannan ya karyar da jikin maryam ta tashi ta fita tana mai tare kukanta, "tasan momy bata kyauta ba, ko kadan amma meyasa takejin zafin momy, damuwarta take tabata... " ta fita dagudu tai wajen pool, shima dake tsaye shigowarshi kenan ya hangeta ya bita....

Dady ya fincike kafarshi yana mai jin tsanarta har ranshi, wacce a sanadinta yayi rashin mahaifiyar abdallah matarshi ta amana, kuma a sanadinta yaronshi yayi maraicin uba bayan yanada gata da dangi gaba da baya, ko waiwayenta beyi ba tana ta magiya amma sam yaqi juyowa, haka ta durqushe gurin tana zubda hawayen nadama, shikuwa hafiz tuni ya fece dan yana tsoron a hadashi da hukuma,

Ta tsugunna a bakin pool din tana kallan yadda iska ke kada ruwan yana motsawa kadan, ko ba komai momy jinina ce itace nake gani tmkr mahaifiyata watakil shiyasa damuwarta ke tabani, bayan kuma kauna data nuna min tun yarintata, zan iya cewa bata taba nuna ni ba diyarta bace inbama tabbaci datake bani kullum na nidin diyarta ce ta hanyar abubwn datake min"
Taji kalaman sun subuce mata tana fadinsu,

"Nikuma taki damuwar kan tabani amma na rasa dalili...."
Kalaman dataji ne yasata firgita ta jya da sauri a firgice... Yana tsugunne shima a dan bayanta kadan, ta dafe kirji tana dubanshi idanu waje,
"Ya khalil? Kaine? Yaushe kazo? Ina wuni" ta fada tana kokarin seta numfashinta saboda tsoratan data danyi

Yayi murmushi ya miqe tsaye yana folding hannayensshi yace lpiaa lau ya gida? Yi haquri na baki tsoro, Ta girgiza kai kawai, itama ta miqe...

Tsit falourn kowannensu ya gaza magana har momy taje ta dau akwatinta, ta zuba kayanta ta fita,
Halima,samir,Abdallah, Ruma, dukkansu kowanne bece mata ko uffan ba, dukka suna alhini, ita kuwa maryama batasan tafiyar momy bama sakamakon khalil daya janye mata hankali da hira dan rage mata damuwa, kuma yaci nasara din,

A bangaren Abdallah babu abinda yafi tsaya mishi a ranshi kmar halima, ko kadan bayason hada ruma da halima matsayin matanshi dan bayajin ze iya musu adalci, kuma ubangiji yace ".....in kana tsoron bazaka iya adalci ba to ka auri daya" gashi baze iya kallan tsabar idon halima ko dady yace ze rabu da ita ba, bayan duk kokarin datayi na ganin ta gyara kuskurenta, abin zeyi mata yawa idan yace ze saketa she'll be terrified

Bayan kwana 1
Things seem to be okay a gidan Alhaji Abdullah, yau su Rumasa'u ke shirin komawa Abuja, flight din rana sukabi, ruma tabar Abdallah da tarin kewarshi shima a nashi bangaren haka, gabadaya Abdallah ya kasa haquri dan Abbah yaqi cewa komi, kawai dai ya zuba musu ido shida ruma sa halima, itama halima rashin maganarshi na damunta, bayan tafiyarssu rumasau ne halima ta yanke shawarar fadin abinda takeso ta fada din tun tuni, da zata fara fadawa maryama ne amma gudun kada ma ta hanata yasa ta tafi straight gun Abbah in yaso daga baya ta fadamata

Yana kishingide kawai ya tallafe habarshi yayi shiru, babu walwala a tare dashi, halima tayo sallama tana sanye da babban hijab, ya amsa kamin ya gyara zamanshi,

Ta tsugunna a gabanshi kanta na sunkuye, ta gaidashi, ya amsa saffa saffa, halima tace "Abbah dan Allah kayi haquri da abubuwan da nayi maka, wlhy ban kyauta ba sam, sharrin shedan ne wlhy Abbah da son zuciya..." Ya dan daga mata hannu alamun ya isa

Halima ta dakata tana jin bugun zuciyarta na karuwa,
Cikin murya mai sanyi Abbah yace "halima ni ai tuni na yafe miki meyasa kike ta dogon jawabi haka, kefa diyata ce babu yadda za'ai na rikeki a raina, wannan shirun nawa da kikaji, ina alhinin abinda li tamin ne, kuma ina alhinin rashin mahaifyar Amir tareda farincikin kasamcewarshi d'ana duk a lokaci guda, shiyasa na rasa me zan zaba farinciki ko akasin shi, amma ni komi ya wuce gurina Kuma tunda wadanda kikaiwa su ruma sun haqura ni mene ze dameni, nasan kinada hankali ba dabiarki bace, kuma babu wanda yafi karfin kuskure a rayuwar nan, fata dai in kayi ka gane ka nemi yafiya kuma shikkenan se a yafe maka"

Halima ta jinjina kai tana mai sake jin dadi tareda dumbin kwarin gwiwa sai tace
"Abbah" ya kalleta yace "ya akayi haliman Abbah"
"Dama So nake ya Amir ya sawwake min,"
Ya sawwaqe miki kmr ya?
Ina nufin ya sakeni Abbah

Dukkansu shiru sukayi kamin Abbah yace "amma halima meyasa kike kokkarin yanke danyan hukunci irin wannan shi amir dinne yace baze zauna dake ba?, ko kunyi fada ne?"

Halima ta sake sunkui da kantaa kas tace "Abbah, babu ko guda daya, nice dai nakeson hakan, Abbah ya Amir yana sona amma ba irin soyayyar aure ba, ya daukeni kanwarshi ne, ni nasani idan ya hadamu duka nida ruma zaman baze min dadi ba, saninshi da nayi tinda na zauna dashi, shikuma baze iya dubarmu ni da kai ba Abbah yace ze sakeni, tun farko sadaukarwa ce ta hada nima yanxu na sadaukar da tawa qaunar kuma ina fata Allah yasa haka ya zame mana alkhairi"

Abbah yace amin amin halima, jeki abinki" ta miqe ta fita hawaye na taruwa a idonta,

Dakin maryama ta wuce straight wacce ita kuma take ta alhinin rashin momy tare da tinanin kowanne hali takeciki?.....

Halima ta karasa ta zauna kusada maryama dake zaune kan kujera a dakin, maryama ta juyo ta kalleta inda ta karanci damuwa cikin kwayar idonta, ta matsa kusa da ita ta dafa kafadarta
"Sanar dani abinda ya dameki ni er uwarki ce".... Halima ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta hawaye masu dumi suka silalo mata, ta goge su ta dubi maryama tace
"Naje na sami Abbah,,,,, ta sanar da ita yadda sukai da Abbah"
Maryaama tace
"Amma halima mene ya sakaki yanke danyen hukunci irin haka, ya kike tinanin ya Amir zeji?"
Halima tace "maryama tunda akayi bikina da ya Amir babu wata alaqa data shiga tsakanina dashi, ina nufin irin ta aure"
Ta sunkui da idanuwanta suna kallan kasa,
"Nasani baya qaunar wata mace da aure idan ba rumasau ba, nasan ba lallai ne yayi adalci tsakaninmu ba, la'akari da irin son da yake mata wanda ya tattake wanda yakemin, dukda ma bana tinanin yanasona a matsayin matar aurenshi, mutun ne shi me cika alqawari, ko a da nice na rokeshi ya aureni shiyasa yanxu xan warware abinda na hada, ta hakane zasu samu kwamciyar hankali da nutsuwar a rayuwarsu, banaso na zame musu cikas a rayuwarsu ta soyayya, banaso ya Amir ya tashi da barin jiki ranar gobe, sanadin kasa yin adalci tsakaninmu..."

Maryama ta rungume halima tana mai jin wani iri a ranta, ashe irin zaman da er uwarta tayi kenan, ashe haka tai kokari ashe ta fita fuskantr kalubale,
Ita gani take in kayi aure shikkenan ka huta, ashe a can dinma akwai wasu challanges din? (Life is full of challenges and test from the almighty,,, Allah ya bamu ikon cin jarabawarmu ta rayuwa) halima itama ta rungume ta cos she needs it (comfort)....

Abbah yayi kiran Abdallah ya sanr dashi komi yadda sukai sanna yace
"Ka sawwaqe mata kmr yadda ta bukata sannan sai mu saka ranar da zamuje abuja nema maka auren ruma"

Abdallah ya dubi abbah inda abbah ya karanto irin tsantsar farincikin dayake ciki, aikuwa anan abbah ya saka ya rubutawa halima takardarta, kuma be musa ba dan shima yana ji kmar hakan daidai ne,

Rumasa'u da Abdallah suka bude sabom babin soyayya tun komawarta Abuja kusan ko yaushe suna waya, saidai be sanar da ita yadda sukai ba anan ya fada mata nan da wani satin zasu zo abuja neman aurenta,

Farinciki in kukaji anayi daya kenan, baga mufida, maryama,Dadyn ruma, samir, sannan uwa uba su masoyan

Samir ne yaje ya sanar da dady komi gameda zuwan su Abdallah nan da sati neman auren ruma to Dayake jikin dadyn yayi sauki sosai yasa ya kira ruma yace
"Ruma ki shirya gobe zamu tafi adamawa ki gano da
Tsalle da rawa ne kawai ruma bata tashi ta taka ba dan murna, ta daga hannu sama tana mai yiwa ubangiji godiya dayake samir ma na gidan yasa yace ze rakasu dan yanxu ya zama dan uwa ma,

Suna zaune cikin gidansu ruman su biyu tace
"Yayana" yace na'am dayake haka take fadamai lokuta da dama yanxu
"Wai meyasa bazaka amshi dukiyarka gurinsu Alhaji ba?"
Ya kalleta tsayin lokuta alamar maganar ta dan tabashi kuma kmr beson yinta
Ya sake kallonta sannan ya ce
"Rumasau Alhaji sunmin komi tun rasuwar iyayena suna tare dani sun kula dani har suka bani auren diyarsu beside we re family, they my family my family are me, idan nace zan amsa yanxu ze jawo rabuwar kai da hayaniya, and Alhaji zeji ba dadi kuma ina aikina, ina da abin hannu, ba dole se na shiga duniya ta sanni ba,  kuma tuni ma na bar mashi, dan Allah karki sakemin tmbya makamanciyar wannan" ruma ta gyada kai kawai

Hlo dear, good day, hop u all doing good masha Allah... Love u all

Pls kindly follow our insta page at unique_arewa_novels #dont ignorre

Follow,vote,repost love yeah

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now