0⃣5⃣: the waiter

1.5K 108 1
                                    

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

kamar kowanne sati dama ranar tuesday Abdallah ke zuwa yayi aiki a garden din makarantarsu Ruma shiyasa datazo bata ganshi a waje ba bata wani damu ba ta shiga cikin school din straight ta wuce garden aikuwa sai taganshi yanata faman aiki sosai, ta tsaya tana kallonshi da tausayawa a ranta tace "he's not lazy" bakadan ba takejin tausayinshi idan ta ganshi... ta karasa gunshi da sallama, ya juyo yana muradin ganin murmushin nata, hakan kuwa ta samu dan murmushi ne kwance kan fuskarta, ta miqa mishi lunch box sannan ta wuce class, da aka fito break ma yana nan, dan haka suka kara bashi wani abincin suma sukaci sauran, da aka tashi kuma bata ganshi ba tayi sororo tana mamaki, sai kuma ta wuce gurin zaman jiran driver ta zauna, ga mamakinta sai ta hangeshi daga nesa da takarda a hannunshi, nan da nan fuskarta tayi wasai, ya karaso yayi mata sallama sannan ya zauna, nan ya miqa mata takardar jiya yace ya haddace Abcd, kuma yazo shima ya koya mata karatun Arabi kamar yadda tace mishi tanaso, nan sukayi ta karatu yana koya mata abubuwa gameda addininta saboda ya lura batasan komai a bangaren ba, itama ta koya mai wasu abubuwan gameda bokonsu, inda take koya mishi rubutu...
4 days later; sunday
momy da dady duk suna gida yau wanda hakan yana wuyar faruwa saboda idan wannan na busy to wannan yana yin wani abu, hakan yasa ba'a cika samunsu duka tare a gida da weekend ba, Ruma na dakinta tana kwance tana kallon sama tunaninta daya ne yanxu, tanaso Abdallah ya fara zuwa makaranta, tanaso ta tallafa mishi da wani abu amma tana tsoron yadda zai kalli lamarin saboda cikin kwanakin nan da suke karatu ta lura da irin hazakar shi, kuma yana da saurin dauke abubuwa, daya samu background mai kyau da irinsu ne za'a dinga misali dasu a duniya, turo kofar dakin akayi tabi hanyar da kallo dan ganin waye, momy da dady ne tare suka shigo, mamaki ne yasakata saurin mikewa tana kallonsu, i hop dai b wani mugun abunne ya faru ba ta fadawa kanta, momy ta samu bakin gadon ta zauna dady kuma ya zauna kan sofa, Ruma tayi tagumi tana kallonsu tana jiran jin abinda zai biyo baya, dady ne yace "Princess, yesterday i signed a contract which made me so happy nd im sure it will be profitable to us" momy ta karbe zancen da fadin "to shine mukeso kema ki samu wani kaso, just tell us mene kikeso yanxu anyi an gama, Ruma tayi shiru tana nazari ita sam ba kudi takeso ba, takallesu sannan tace "kome nakeso?" dady da momy suka hada baki sukace ofcourse princess, Ruma tace a hankali "momy... daddy i just want to go out with u, hav some food together as a family" dady da momy suka kalli juna su sun dauka ma zata fadi wani abu kamar toy, phone, system, dress da makamantansu, dady yace "olryt get ready we re going out" Ruma tayi tsalle ta dire, tanajin wani dadi a ranta ta rungume dady da momy tace thank you,

cikin pink attire Ruma tayi shirinta looking exactly like the princess, momy da daddy ma sunyi shigarsu mai kyau suka hau mota daya,duk suna baya Ruma na tsakiyarsu dadi ya isheta yauga momynta ga dadynta, is as if her long awaited prayers are answered, wani shahararren gurin cin abinci mai rai da motsi suka karasa, Ruma murna kamar kamar me?, suka samu table guda daya, dady yana duba menu din ya tambayi kowanensu me sukeso, duk suka sanar mishi abinda suke so, dady yayi placing order ma wani waiter dan gayu, kusan 15minutes after, Ruma ta karbi wayar momy saboda ta kosa da jira da fara game, sai kuwa taji sallama an kawo abincin, muryar wanda yayi sallamarce ta dauki hankalinta tasa take niyyar dagowa amma sai taji fada ya kaure, dady sai faman masifa yakeyi mishi wai kazami, baima iya tarar costomer ba gashi dan talakawa... Ruma ta dago tana kallonshi, duk zafin maganganun da ake fadama Abdallah saida ya mance su, saboda fuskarta da ya gani dukda ba murmushi take ba, ta nuna alamun tashin hankali, sam dady baima lura ba ya tara mutane, fada yake babu ji babu gani, yana zagin Abdallah, dady kam ya tsani talaka a rayuwa, Ruma ce ta fashe da kuka tace "dady pls" dady ya juyo ya kalleta sannan yaga mutanen dake tsaye, wanda duk ma'aikatan restuarant dinne suke ta bawa dady hakuri shikam Abdallah ya tsaya kawai dan yasan babu laipin dayayi, Ruma ta furta "he's my friend fa dady" momy da dady suka hada baki wajen furta "ur friend? Rumasa'u kikace wannan abinne friend dinki... to kinci gidanku keda friend din, ran Abdallah ya gama baci saboda yadda yaga sun koma kan Ruma suna hayayyako mata, momy ce taja ta suka fito har lokacin bata bar kukan ba kuma, can kuma saiga dady shima, suka shiga motar suka figa, dady yanata balbali, haka suka koma gida zuciyoyin kowa a bace, ita abinda ma yafi batawa Ruma rai shine basu tambayeta ya akayi ta hadu da Abdallah ba... a'a sudai kawai fadansu meyasa zatayi friend da talaka kazami kamar wannan..... Abdallah kuwa tuni ya rasa aikinshi dan dama dakyar ya samu aikin a nan din saida wani mutun da Abdallah keyiwa wanki ya saka baki suka bashi, kuma ba sonshi suke ba...
Safiyar monday;
tunda Ruma ta tashi yau duk bata wani jin dadin jikinta, aka gama shiryata dan tafiya school ta dauki 2 lunchbox dinta as always hoping zataga Abdallah ta bashi haqurin cin mutuncin da dady yayi mishi, driver yayi parking Ruma ta fito a sanyaye ganin babu shi babu alamarshi, ta qarasa gun mai gadinsu ta bashi sako kamar rannan kan ya bawa Abdallah lunchbox idan yazo, ta wuce jiki duk a sabule tana tunani kala kala a ranta, Ruma taje class ta sanar da mufida abinda dadynta yayiwa Abdallah, mufida ta kwantar mata da hankali kan cewar komai zai wuce tayi haquri, for now tayi concentrating, Rumasa'u ta kasa maida hankali, duk malamin daya shigo kallonshi kawai takeyi tana ayyana idan itace akayi mata abinda akayiwa Abdallah tasan bazataji dadi ba, aka fito break Ruma taje gate gun maigadi ya sanar da ita cewar Abdallah baizo ba, kamar zata rushe da kuka mufida ta jata suka koma, tunaninta shine Abdallah yayi fishi da ita baze zo ba, ta share kwalla har aka tashi hankalinta a tashe yake, zama sukayi ita da mufida jiran driver, sai Ruma tace "mufida kizo ki rakani naje na bawa Abdallah haquri bazamu dadeba yanxu zamu dawo" wani kallo ta watsa mata "kinada hankali kuwa wannan katon titin zamu tsallaka, mu biyu? kalla fa kigani" Rumasa'u ta dubi titi taga motoci sai figa suke suna wuce ga girma, ta dafe kanta tanaji yana sara mata, mufida ce ta dan tabata tace "Ruma kinga ya Abdallah"  ta dago da hanzari, daga nesa ta hangeshi yana tahowa, fuskarshi wasai kamar babu abinda ya faru jiya miqewa tayi tana murmushi, ya karaso ya zauna, mufida tace "ya Abdallah yau munata nemanka bamu ganka ba duk hankulanmu sun tashi" Abdallah yace kuyi haquri naje neman aiki ne shiyasa, Ruma taji duk wata damuwa tata ta kau, nan suka yi lesson dinsu kadan, saida akazo aka dauki mufida sannan Rumasa'u tace "ya Abdallah dan Allah kayi haquri gameda abinda ya faru jiya... "ya riga ya wuce Rumaisa karki daga hankalinki" tace "ka rasa aikinka saboda dadyna ko ya Abdallah?" yayi murmushi yanaso ya kawar da zancen yace "wai ni kuwa baki taba fadamin me kikeso ki zama ba nan gaba?" munubiya tayi er dariya tace "ya Abdallah likita nakeson zama in Allah yaso"

SHAREE 🙏
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum