1⃣4⃣: farewell

1.2K 98 6
                                    

♥💍 *ZUCIYAR ABDALLAH*💍♥

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Abdallah ya gyara tsaiwa ya zubawa kalla ido kamar zai cinyeshi ya kagu yaji sakon Ruma,, kalla ya zayyanewa Abdallah duk yadda sukayi da Ruma, harda maganar kudin datace Abdallah ya bawa kalla, Abdallah yace dan jirani, ya shige gidan da zumudi sosai, Abdallah ya karasa ya ciro kudi ya dawo, ya miqawa kalla dubu daya yace gashi, kafi karfin hakama domin sakon daka kawo yafi duk wata dukiya, sai yace muje ka rakani na sayi layin, kalla yace "ai a shirye nazo" kalla yasa hannu a aljihu ya ciro layi sabo fil a ledarshi" dadi ya ishi Abdallah ya rumgume kalla yana murna, ya amshi layin ya miqawa kalla naira dubu nanma, yace ya rike duka daga haka sukayi sallama, Abdallah haka ya cinye daren da tunani kwalli daya wato tunanin Ruma, yana tsananin son ya ganta, sai juyi yake kan tabarmar dayake kwance akai,

kashegari... Abdallah tunda sassafe ya karasa gidansu Ruma, dayake dama yasan gidan nasu, ya kaiwa baba maigadi lambar layin a jikin takarda, sannan ya tsallaka titin dake gaban gidansu ruma ya samu guri can nesa jikin wata bishiya kasancewar unguwar bamai yawan jama'a bace ya zauna kurum yana kallon titin da kuma gidansu Ruman yana jira tareda saka ran zaiga Rumasa'u koda sau dayane, Ruma kuwa da sassafe ta tashi, tayi wanka ta shirya kanta saboda flight din nasu na karfe 9 ne tunda ta tashi take saka da warwara tana tunanin ta bawa baba maigadi wayarta ta kano data saka a drower ya bawa Abdallah tunda dady yace zai siya mata wata...., karfe 8 na safe momy tazo tayi knocking dakin Ruman, Ruma da gama shirinta kenn ta bude kofar tana ma momy murmushi, momy ta kalleta tace "lallai princess kinaso kije kano, Ruma tayi murmushi kurum, momy tace to kiyi breakfast kafin mu gama shiryawa, daga haka momy ta fice itama Ruma ta sakko ta cika cikinta..... qarfe 9 jirgin nasu ya tashi zuwa birnin kano... guraren karfe 11 saura suka sauka, straight gidan suka wuce, daidai sunzo kofar gidanne... Abdallah ya zubawa motar ido, lokaci guda Ruma ma tanata waige waige, saidai dayake yana kasan bishiya yasa bata hangeshi ba... Abdallah dayaga motar ta nufi gidansu Ruman ne ya tabbatr mai lallai zuciyartashi ce ta dawo... ya miqe da sauri yana son ganin muradin ranshi amma yasan hakan bazatayu ba saboda akwai tint a motar, haka motar ta shige gidan aka maida gate aka rufe, tuni hankalin Abdallah yayi gun Ruma bayaji bakuma ya gani, da sauri ya tashi yayi gaba da gudu da matsanancin shauqin son ganin rabin jikinshi, ko kadan bai lura ba da irin gudun da motar ke filfilawa tunda titine da baida jama'a, shidai burinshi ya karasa gurin sahibar tashi, duk yadda drivern motar yaso yaci birki ya kasa saboda ba karamin gudu yakeyi ba dan ansan titine dayake shiru babu yawan motoci, Abdallah na tsakiyar titin drivern na tayi mishi horn amma inaa,,,, wata irin kara taji cikin tsakiyar kwanyarta da dodon kunnenta, Ruma tayi hanzarin toshe kunnenta da hannu biyu jin kamar kanta zai tarwatse, take taji gabanta ya buga ta dafe kirjinta da sauri tana addu'a,,, ta furta ya Abdallah... shine abu na farko dayazo cikin kwanyarta, ta goge zufar dake tsattsafo mata da matsanaciyar fargaba hadi da tsoro... tunawa tayi da abinda ya faru bayan shigowarsu, momy da dady sukace mata zasu je cikin gari saboda aiwatar da ayyukan da suka kawosu itakuma ta hau sama tanaso ta kwanta, kurum taji Abdallah na fado mata a ranta, da dan hanzari ta sakko kasa ta karasa gurin baba maigadi ta gaidashi, sannan ta tambayeshi ko an bashi sako, nan baba maigadi ya dakko mata takardar da mufida suka rubuta mata dakuma lambar layin da Abdallah ya kawo jiya... Ruma ta karba tayiwa baba maigadi godiya sanann ta koma falour ta zauna tana karanta wasiqar tana murmushi bakadan ba taji dadi dataji suna lpia kuma suna rokarta ta kula da kanta, sai kuma ta kalli takardar da Abdallah ya kwafi number ta kurawa nambobin ido, kana kallo zakasan bai iya rubutu ba, kwafa yayi dakyar, Ruma tace insha Allah next session zaka shiga makarantar boko zamu cika burikanmu na zama likitoci dukka mu uku (including mufida)....wajen la'asar su momy suka dawo tanata jiran su dawo ta fita saboda duk babu mototci a gidan yanxu, amma suna dawowa suka soma shiri jirginsu ya kusa tashi, haka Ruma tanaji tana gani ta tafi ta bar kano gashi babu hali ta bawa baba maigadi wayarta saboda shima gobe zai bar garin kuma za'a rushe gidan, ranta babu dadi, bacci Ruma tayi cikin jirgin saboda batajin dadi hakan yasa batasan irin dadewar da sukayi a sararin samaniya ba...

"Alhaji Abdallah hakika akwai complication gameda yaron gaskiya, akwai matsananciyar yunwa a tattare dashi ulcer ce dashi kuma tana hankoran taba hanjinshi, amma za'a iya dorashi kan magunguna, sannan kuma yana da bukatar kayan abinci masu gina jiki da kara lpia, kuma babu ishasshen ruwa a jikinshi, ga rashin ishasshen jini kuma baya samun bacci da alama ma damuwa tayi mishi yawa, bayaga aikin dayakeyi dayafi karfinshi, wadannan abubuwan sune wadanda muka gano yanxu kuma idan ba'ayi fixing da wuri ba zasu bata rayuwarshi gabadaya.." Alhaji Abdallah ya sauke wani nannauyan numfashi cike da tausayi fal ranshi, ya dubi likitan yace "yanxu likita yaushe kake ganin zai farka kuma a sallameshi, likita yace "ko yau da daddare za'a iya sallamarshi amma munyi mishi allurar bacci yanxu dan yanada bukatar hakan kuma zamu sakeyi mishi wata anjima akalla yayi kwana biyu yana bacci,,, karfe 9 na dare aka sallami Abdallah dake kwance magashiyyan batareda yasan inda kanshi yake ba bayan yasha karin ruwa da jini, anyi mai dressing duk ciwukanshi na kafa da goshi da hannu, an sallameshi ne akan likitoci zasu dinga kulawa dashi har ya farka....

kallan su momy tayi da tambayoyi kwance kan fuskarta momy tayi mata murmushi mai kyau sannan tace "princess welcome to saudiyya" Ruma da murna ta kalli momy ta rungumeta, haqiqa duk cikin kasashen duniya babu kasar datafi kauna kamar saudiyya, dama tanaso ta kara dawowa wancan zuwan ba wani so tayi ba, sai gashi sun kara dawowa din kuwa.....

bayan kwana daya da yini
qarfe 5 na yammaci ya bude idanunshi da sukayi nauyi, dakyar, inda yake ya soma bi da kallo, dakine na en gayu, royal bed ne mai tsada blue colour, jiri yaji yana dibanshi dakyar ya miqe zaune yana kara kallan ko ina da tarin tambayoyi a ranshi, sai ya kalli kanshi ganin bandage hannu da kafa, damm yaji gabanshi ya buga tunawa da abinda ya faru, yasan ya miqe yana so yaje yaga Rumasa'u, sai karan dayaji a kunnenshi daga nan komai ya dauke mishi, Abdallah ya rike kanshi dayaji zai tarwatse, ya sakko a firgice yanaso yaje yaga Ruma kafin ta koma saboda tunawa dayayi yau zata tafi, Allah yasa Ruma bata tafi ba, ya fada yana sauke kafafunshi daga kan gadon, miqewa yayi amma inaa yaji baze iya ba saboda yawan raunukan dake kafar tashi, da dingishi ya soma dingisawa yana tafiya, bai karasa bakin kofar dakinba aka turo kofar, Abdallah ya dan dafa bango ya tsaya yana jiran ganin wanda zai shigo, wata macece ta shigo wacce bata haura shekaru 30 da doriya ba, sai yarinyar da bazata wuce shekara 10 ba rike da hannunta, wani kallon banza tayi ma Abdallah "me zakayi daka tashi ina zakaje?" ai ko saurarenta baiyi ba ya cigaba da tafiyarshi, har ya dangana da kofa abin mamaki ko kallonshi batayi ba balle ta tsaidashi,, yana fita wani corridor yabi sannan sai falour sai kuma ya hangi wagegiyar kofa, da azama ya karasa dukkuwa da irin azabar da kafartashi keyi amma bai kula ba, ya fito sai ya tsinci kanshi a farfajiyar gidan da aka kawata ta ta bishiyu koraye bayan gurin ajiye motoci, sai kuma gate daya hanga, gate ya nufa da sauri sauri har yana dage kafa daya, dan bayaso Ruma ta koma abuja bai ganta ba.... kafin ya karasa gate din ne yaga an wangaleshi, wata hadaddiyar mota ta kunno kai, ko kallon motar baiyi ba ya fice abinshi har yana hadawa da gudu, lokaci guda kuma idanshi na fidda hawayen azaba, "zan jure, zan jure Ruma indai zan ganki" shine kalaman da Abdallah ke furtawa, Alhaji Abdallah da shigowarshi kenan ya hangi Abdallah na fita yasa ko parking bai bari driver yayi ba ya fita a kafa dukkuwa da matsayinshi da dukiyarshi amma bai kula ba, koda ya fita ya samu Abdallah yayi nisa har ya kusa tsallaka babban tti yasan baze iya kamoshi ba hakan yasa ya koma ya kira ma'aikatanshi suje su tsaida Abdallah, shima ya biyosu.... sam Abdallah yaqi tsaiwa saida suka rirrikeshi dayake kuma karfafan maza ne, Abdallah ya hangi mutumin dake tahowa sai kuma lokaci daya ya dena jin komai ya dena ganin komai.... kashegari......
sanda ya bude ido akan gadon dai na dazu ya samu kanshi saidai yanxu akwai mutane cikin dakin, suna sanye da fararen kaya mace da namiji wanda ya tabbatr likitoci ne...

UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें