2⃣2⃣: Tears😭 just began to drop

1.2K 92 1
                                    


follow Ayshab Nasir @ wattpad

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Rumasa'u da momy sun kammala duk shirye shiryensu na dawowa garin kanon dabo,,  furnitures din gidan suka siyar wanda hakan yasa suka samu en kudade a hannu,  saida suka sallami banki kamar yadda sukayi alqawari sannan suka kama hanya,  shatar mota guda suka dauka zuwa garin kano,  cikin su ukun babu wanda bai jigata ba da zaman mota saboda abune da basu saba ba,  lokaci guda ruma taji yanayin jikinta ya sauya sosai,  tun kafin su karasa kano,  wani zazzabi ya rufeta dama sai jin wani iri take abinka da jikin da baisaba da wahala ba,  kafin suje zazzabi ya kwantar da ita,, abin sai yayiwa momy yawa,  ga jikin dady gana ruma, tama rasa ina zata tsoma ranta dan tashin hankali,,,

Amir ya cika wata guda a birnin london,  matuqar jin dadin karatunshi yakeyi, kusan kullum sai halima ta kirawo shi,  tun bai damu ba har ya fara damuwa saboda yadda kiran nata yayi yawa, har saida yace "ki dena damuwa halimatu ina nan lpia qalau base kin dinga kirana kullum ba" da wannan maganar yasa halima tadan tsahirta mishi da kira, halima kuwa ba er karamar kewar Yayan nata take ba,  sai yanxu take gane irin kaunar datake mishi da kuma irin shaquwar da sukayi, kullum in zasu tafi school sai taga kamar zai fito su tafi tare amma har su dau hanya baifito ba itakuma tana zubawa bangarenshi ido, sai ss3 din ya zama sam baiya mata dadi,  dan karatun da suke tare,  cin abinci,  tafiya makaranta, hira duk yanxu babu, sai ta zama kamar wata mara lpia, a wata dayan dayayi da tafiya,  saidai zuciyarta na sanar da ita wani abu,  amma takan basar saboda tasan zuciyar yayan nata ta Rumasa'u ce,,,

Sanda suka sauka garin kano,  momy ita kadai ke fafutuka takoma kamar wata sabuwar kamu,  tayi nan tayi nan,  Allah  ya taimaka ta sama musu wani gidan haya dan akwaita da kurda-kurda, kan tabarma suka kwana a wannan daren,  kashegari ta debesu duka suka tafi asibiti, duka su biyun aka basu gado,  ita Rumasa'u likitoci sukace chanjin yanayi  ne yasakata zazzabin amma zata ware nan bada jimawa ba,  aka saka mata drip na ruwa,  momy kuwa ganin en kudin hannunta na tafiya a allurai da magunguna da gashin dady yasa ta shiga kasuwa ta siyi,  er katifa da wasu abubuwan cikin gida, sannan ta zauna shawarar wacce sana'a ya dace suyi,,,
Kwanan Rumasa'u biyu aka sallameta, shima dady suka sallameshi sukace a dinga kawoshi gashi kurum danko kudin gadonma wani abu ne.... Rumasa'u batajin dadin jikinta,  su uku suka dawo gida, koda suka shiga ruma taga gidan ya chanja, an dan sassaka kayayyaki,  ruma tace "momy sannunki Allah  ya biyaki" momy dake gefen ruma tayi shiruu bata amsa ba,  hakan yaja hankalin ruma dake tura dady ta juya ta kalli momy,  bata ankara ba,  taji giff,  momy ta yanke jiki ta fadi kasa, batasan sadda ta saki wheelchair din dady ba,  tayi kan momy tana mai shiga hargitsi saboda ganin irin mummunar faduwar datayi lokaci daya kuma bata motsi,  tana kokarin dago momy ne,  taji mummunar faduwar abu,  ashe sakin datayiwa dady,  bai zauna ba,  keken ya cigaba da garawa dashi har yakai bakin rariya ya kifa kasa,,,
Kamewa tayi cikin tsananin shock, sai kuma jikinta ya soma karkarwa, ta rasa wazata kama, dady ko momy,  kawai sai ta zauna dabar,  tana mai fashewa da matsanancin kuka, hawayen nata na ambaliya kan fuskarta data sauya,  wani abu mai daci ta hadiya tana mai jan numfashi sosai,  sai kuma ta daga hannayenta sama
"ya Allah nasani kana sane damu ya Allah  ka saukaka mana, Allah  mun tuba ka gafarta mana ka yafemin nida iyayena", wannan addu'a datayi ta kara mata karfin gwiwa,  ta miqe da azama tasa gyalenta ta goge hawayenta,  sannan ta fita waje,  ta taro tazi ta kira drivern ya taimaka mata ya tayata saka dady da momy a mota, momy ko motsi batayi,  wanda hakan ke saka Rumasa'u cikin mummunar  faduwar gaba, saidai karfin zuciya da dakiya da imani yasa ta danne zuciyarta tana mai lallashin kanta,  haka aka sake bawa momy da dady gado dukkansu,  anyi exerminimg momy aka tabbatrwa da Rumasa'u cewar partial paralysis ke damunta,  amma zata ware saidai ta rage zirga zirgar datake,  nan suka rubuta mata allurai da balance dinta,  Rumasa'u dako anini batta dashi ta rike takardar tana kallo,  kamar kudin zasu fito ta ciki,  bata akara ba taji hawaye na jika takardar,  hakan yasa tayi saurin daga kanta, ta samu guri ta zauna tana tausar zuciyarta, tunani ne ya fado mata ko taje gida watakil ta samu kudi a can, hakanan ta fito ko kudin motar komawa batta dashi,  tafiya kawai take amma batasan inda take jefa kafarta ba, tunani fal a cikin ranta,  sai kumata dago karamin yatsanta,  ta juya zoben da Abdallah  ya bata,  wannan ne kadai kadarata yanxu dazan siyar dan samun abinda zamu rayu nida iyayena,  saidai na rigada nayiwa zuciya alkawarin duk rintsi duk wuya bazan siyar da abinda shi kadaine tak ke tunamin da memories dinka ba Abdallah koda kuwa zan mutu cikin talauci"..... babu zato babu tsammani taji motar ta gogeta,  wanda yasa saida ruma tayi katantanwa a titin har goshinta ya bugu jini ya fita,  ta miqe da azama ta rike goshin nata,  ta gama rudewa ma,  ashe tana tsakiyar titi ne bata lura ba,  ji tayi an rikota ana fadin "baiwar Allah  kinji ciwo jini ne ke zuba".... Daga wannan furucin bata sake sanin inda kanta yake ba dif komai ya dauke mata

Tsayin wasu dakiku Rumasa'u ta bude idanunta, cikin wani hadadden daki ta ganta, sanyin A. C na tashi sai kamshin room freshner mai dadi sosai, azababben ciwon kai taji da riketa,  ta dan tashi zaune, amma babu kowa cikin dakin,Kallon dakin take tana tunawa da nata dakin wanda ko kadan bai kama kafar wannan a kyau ba,  amma yanxu babu ko kamar wannan din ma.... Tunawa tayi da momy da dady, gabanta ya tsinke ya fadi,  ta dafe kirji nan ta soma kokarin sakkowa, tana cikin haka ne aka bude kofar wata budurwa ta shigo,  Rumasa'u ta bita da kallo, Rumasa'u ta gurmeta da kusan shekaru biyu ma, halima ta karasa kusa da ita tace "sannu baiwar Allah,  nice wacce drivernmu ya kadeki dazu,  ya jikin naki, likita ya dubaki kuma yace kina bukatar hutu sosai yakamata ki huta kinji...  A hargitse Rumasa'u ta tashi tsaye "kinga momyna da dadyna suna asibiti yanxu ma kudin bill zanje na biya ni ake jira" halima ganin irin hargitsin data shiga yasa tace "to bari na saka driver ya kaiki"....., halima da driver suka raka Rumasa'u, gida ta fara zuwa ta dakko kudi inda momy ke ajiyewa,  saidai iya kudinsu kenan dayayi saura, ta fito suka kama hanyar asibiti,  ruma kamar bazatayi magana ba, sai kuma tace "baiwar Allah  dan Allah in babu damuwa aik nakeso ko wanne iri ne,  iyayen basu da lpia duka kuma bamu da komai" ta fada kwalla na taruwa cikin eyeball dinta, halima tace "dadyna dama yace ki jirashi ya dawo,  yanxu idan mukaje asibitin sai mu koma gida ki tambayi dadyna watakila yanada aikin daze baki",,, ruma taji dadi tayi mata godiya,  haka kawai halima ta tsinci kanta da kallon Rumasa'u, a ranta tana mamakin irin wahalar da yarinya kamar wannan takesha,  babu abinda ta rasa daga fannin halitta, da watace da wani sha'anin daban zata shiga ta samu kudi kota halin kaka,,, haka sukaje asibitin aka biya kudin, lokacin dukansu daga momy har dady bacci sukeyi....  Rumasa'u ta bi halima zuwa gidansu ko Allah  zaisa ta samu aiki

#not edited👏🏻

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now