4⃣4⃣: explosion

1.3K 113 11
                                    

Khalil ya kira mami tazo suka gaisa da su Samir ita a zatonta Samir ne ya auri Ruma da diyansu, sakina qanwar khalil itace tazo ta shigar da Ruma ciki segashi sunata hira abinsu, hakan ya dauke mata kaso me yawa na damuwarta,

Sanda sukai sallar magariba suka danci abinci kadan sanann suka soma kimtsa kayan su domin tafiya, Rumasa'u ta fito ta tarad da khalil da samir a bakin mota, dama ta riga tayi sallama dasu hajiya tun a ciki dan haka suka dau hanyar airport, suna cikin tafiya kan titin, wayar Samir tai kara yayi mamakin ganin me kira a ranshi yace "so soon" snn ya latsa ya dau kiran, okay to gamunan maryama" sunan maryama daya kira shine yaja hankulansu, Samir yace maidamu gidan Alhaji Abdallah, Rumasa'u ta dubeshi a ranta kuwa ji tai yayi wani fari,
Da kamar khalil baze bisu cikin gidan ba amma se yaga gara ya bisu, dan baze bari aci mutuncin Ruma ba,
A zazzaune suka sami kowa a falourn, duk kowa yayi jigun jigun, maryama ta tarbesu tace "sannunku da dawowa, ta nuna musu guri suka zauna, dukansu har khalil, maryama tasa hannu ta amshi baby ta zauna kusa da Ruma tace "calm down everything will fall into place" ta fada da rada yadda babu wanda yaji se ita Ruma data rada mata, Rumasa'u ta dan gyada kai kurun, khalil kuwa yana lura da yadda maryama ke kokarin comforting Ruma duk se yaji ta birgeshi, maryama ta kalli Samir ya jinjina mata da hannunshi itama tai mai kamar yadda ya mata👍

Cikin shessheqar kuka Halima tace "dan Allah ku yafemin, duka son zuciya da rudin shedani ne" take momy taji gabanta ya fadi, hakama hafeez
"Rumasa'u sam batada laipi cikin wannan abin dake faruwa nice du na haddasa"
"lokacin da muka hadu da Rumasa'u a asibiti nai realizing itace Ruman Abdallah, a lokacinne naji kishi ya taso min dan na tabbata ya Abdallah baze zauna dani ba, saboda kaunar dayakeyiwa Ruma ni shaida ce kuma sanin da nai ya aureni ne saboda rokarshi da nai ya taimakeni banaso na auri hafeez kuma bazan iya kallon idonka dady nace banason gudan jinin ka ba ashe ma ba hafeez ne danka ba Ya Abdallah ne asalin danka,
A hankali take warware musu komi yadda akai Abdallah ya yarda da aurenta, da kuma haduwarsu da Ruma da dalilin dayasa Ruma ta kawo hafiz matsayin d'an Alhaji,,, wanann yasa kowa ya maida kallonshi ga momy,
Ta cigaba "a nawa son zuciyan nasan momy zata goyi bayana na kirata a waya na sanar da ita komi yadda akayi, nasan dole ta goyi bayana tunda bazataso nata asirin ya tonu ba tinda tasan hafiz ba yaron dady bane, itakuma momy tasan yadda tai ta hada karya da gaskiya ta fadama dady tun kafin mu dawo daga Abuja, wannan yasa ka yanke shawarar Abdallah baze auri Ruma ba, haqiqa ya Amir ban maka adalci ba duba da yadda ka taimaka min a rayuwa tin ina kankanuwa, ka samar da farinciki a rayuwata nayi kuskure danake kokarin dakushe naka farinciki abisa nawa son kan, dady ban kyauta ma ba dana barka ka yanke danyen hukunci bayan nasan Ya Amir shine danka na asali ba hafiz dan bogi ba,

Kuka takeyi mai sosa zuciya, "banida wani zabi ne a baya a tawa wautar, ina qaunarka ya Amir, to tayaya bazan qaunaceka ba, bayan a saboda ni ka kan kwanta bakaci komai ba, tun bansan wace ni ba a shigo ka haska rayuwata, ka maidani yarinya me fara'a sabanin da, ka sadaukar da farincikinka saboda ni, saboda ni ka fasa tafiya makarantar kwana duk dan kada na koma er gidan jiya na gallazawar momy,
Ta rufe fuskarta tana gunjin kuka sosai wanda ya sanyayar da jikkunanan su baki daya,

Rumasa'u ta miqe ta karasa inda halima ke zaune a kasa ta tankwashe kafa itama Ruma ta tsugunna a gefenta tasa hannu ta dafata, halima kamar jira take ta rungume Ruma kiyi haquri yaya Ruma, dan Allah kiyi haquri, Rumasa'u ta miqar da ita tsaye suka shiga ciki,, wani mugun kallo dady da afawa momy kamin ya tashi ya fice, Abdallah ya sunkuya yana mai sujjadar godiya ga Allah, momy ma ta fice hakama hafiz ya rage daga maryama se hafiz se samir da Amir

Samir yace "kin cika alqawarinki maryama sarauniya" tai murmushi" Abdallah yace wanne alqawari?
"tayimin alqawarin bazata barku ku rabu ba kaida Ruma da taimakon Allah zata seta komi, amma tayaya kikai hakan" maryama tace "ni kaina ban dauka zezo da sauki haka ba, amma kanwartawa akwai rauni kuma sam ba halinta bane, nasiha ce kawai nayi mata," ta sanar dasu yadda sukai da haliman, se gashi da kanta ta nemi kowa,
Abdallah yaji dadi sosai be taba sanin haka maryama take ba, ko a mafarki aka ce mishi zatai abinda tai baze yarda ba dubada yadda basa wami shiri, basa shiga harkokin juna, khalil yabi maryama da kallo with lots of impression gameda abinda tayi din, itama tai musu sallama tabi bayan su ruma ....Khalil ma ya wuce gida

Dakyar da shidin goshi suka samu ta dena kukan, ta kwantr da kanta a cinyar Ruma tana maida numfashi,
A ranar da yawansu a gidan basui bacci ba, ciki harda halima, momy, hafiz, amma maryama da Abdallah da Ruma bacci sukai harda minshari cikin kwanciyar hankali
Ita halima fargabar rabuwarta da Abdallah da hukuncin da dady ze yanke mata yasa ta kasa bacci, momy da Hafiz kuwa dama babu bacci a tare dasu lol
Shikam Alhaji Abdallah ya samu yayi bacci amma bame yawa ba, abubuwa dayawa ne ke yawo a cikin kanshi

Kashegarin ranar Alhaji da kanshi yayi kiran gagarumin meeting, bayan intro da batutuwa marasa yawa ya soma fadin
"Rumasa'u kimin bayani da kanki dalilin dayasa kika kawo hafiz kikace shine d'ana" Rumasa'u ta zauna taiwa Alhaji bayanin komi da momy ta sakata cikin nadamar abinda ta aikata, daga karshe ta bayyana musu dalilin barinta aiki a gidan a wancan lokacin sanda taji momy na yunkurin hadata aure da hafiz din"

Ranshi ya sake baci matuqa amma ya maze ya dubi hafiz yace "yanxu kai hafiz kasani sarai kai ba jinina bane amma shine ka biyewa naka ra'ayin kaima kuka maidani wani daban, se ya maida kallonshi ga hajiya lami wacca gabadaya tasha jinin jikinta, bakin ya mutu
"da farko dai ki sani lami na sakeki ki barmin gida, abu na biyu kuma da kaina zanje Abuja nemarwa dana auren Rumasa'u, kai kuma hafiz ka hanzarta barinmin gida tun kafin na saba maka na hadaka da hukuma" abinda kikai hajiya lami Allah ya sakamin, abinda kikaiwa mahaifiyar Abdallah itama Allah ya saka mata kije da halinki zaki gani indai daidai ne abinda kikeyi"

Sorry bani da lpia yau wlhy shiyasa beyi yawa ba

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍حيث تعيش القصص. اكتشف الآن