3⃣7⃣: Doctors

1.4K 130 6
                                    

Samir ya tsirawa babyn tashi ido, tafi debo kamannin samira dukda ta debo nashi kamannin shima amma ta debo duk wasu kyawawan siffofin samira amma ita black beauty ce yanayin fatar Samir din, ya lumshe ido with coolness and calmness yana mai sake godewa ubangijin talikai, duk doloncin Samir yanaso yaga jininshi yanaso ya hayayyafa dayawa shima annabi yayi alfahari dashi, ya tuna fadan da sukasha yi da samira akan ta yarda ta haihu amma tace ita sam bazata yarda ba... Haihuwa ta kauyawa ce amma ina mace kamarta ina haihuwa... Ya sauke numfashi kafin kuma ya maida idanunshi kan Ruma dake kwance tana wahalallen baccin, fuskarta fayau tayi kyau sosai very fresh dan ta murmure.... Murda kofar dakin akayi aka shigo, Samir ya fadada murmushinshi ganin wadanda suka shigo din, Alhaji, maman samira da kuma ita uwar gayyar samira, dan tun da Ruma ta fara nakuda basu hadu bama dama samir ne ke kulawa da hidindimun Ruman,, ko kallan jaririyar samira batayi ba, yayinda su dady kuma sukaita sam barka ga jaririyar suna saka mata albarka...

Bayan wasu awanni Ruma ta bude idonta tana maijin ciwo a jikinta sosai, ta yatsina fuska daidai nan nurse ta shigo tana mata sannu kamin ta fada mata abubuwan daya kamata tayi da wanda bazatayi ba tace kuma gobe da safe likitan data karbi haihuwarta zatazo dubata... For d first time Ruma ta dora idanunta kan babyn daya zauna a cikinta tsawon watanni tara da dadi da ba dadi, Rumasa'u ta dan shafi kanta kana tace Allah yayi miki albarka, tana mai tsananin jin kaunar yarinyar har zuciyarta, samir ya kallesu cike da kulawa lokaci guda yaji wani abu ya darsu a zuciyarshi, wanda kuma yakejin ze sauya rayuwarshi indai hakan ze faru, anan asibitin ya kwana yana taimakawa Ruma da duk abinda ta bukata tamkar mijinta, ita Ruma tausayinshi ma takeji sosai... Kashegari Alhaji yazo ya sanar da Ruma goodnews cewar karshen watannan in Allah yaso dadynki ze dawo komai ya kammala ya murmure sosai kuma yana iya tafiya da kafufunshi" Ruma ta rintse ido tana maijin dadi a ranta sosai, finally dady yaji sauki bayan long treatment din dayasha mai daukan lokaci wanda kamar baze kareba, ta kalli Alhaji tana kai godiya ga Allah cikin ranta, dan ba kananun kudade Alhajin ya kashe kan rashin lpiar dady ba, dukka suna nan cikin dakin Alhajin ya miqe yana sake mata sannu kamin ya wuce, samir ya fita raka shi, Rumasa'u tayi shiru tana kissima abubuwa iri iri a ranta gameda tata rayuwar, aka murda kofar dakin aka shigo wanda a zaton Ruma samir ne ya dawo amma sai taji muryar mace, ta daga kanta tana kallan doctor din data shigo, cak ta tsaya batareda ta karaso gun patient din ba, Ruma dake kishingide ta soma kokarin miqewa tana sake kallan likitan, kallan kallo suke yayinda idanun likitan suka kawo ruwa,,, a hankali Ruma ta furta "kamar na sanki" ta fada tana san tuno inda tasanta.... Hawayen datake ruqewa ne suka wanke fuskarta bakinta sai kakkarwa yake hakama jikinta ta daga hannunta dake rawa ta nuna Ruma da yatsanta, sai kuma ta karasa da gudu ta rungume Ruma tana mai kara sautin kukanta, yanxu kam Ruma ta tuna inda ta santa, murya can kasa Ruma tace "mufida?" ta fada tana mai nuna alamar tambaya, se kuma tayi breaking hug din tana sake kallon likitan kafin ta kamo fuskarta da hannu biyu cikin bayyanannen farincikin da fuskarta ta kasa boyewa, mufida kece?" mufida ta gyada kai tana shatatar da hawaye... "nice Rumasa'u, bestynki mufida ce" ai Ruma sai ta sake rungumeta tana mai jin dadi a ranta "ashe zamu sake haduwa Ruma" Ruma ta sharewa mufida hawayenta "to mene abin kuka? "sai ta sake kallanta kamar me neman wani abu tace "kardai kece likitan data karbi haihuwata" mufida tayi dan murmushi nice Ruma, ashe kema kinyi aure" "wait kina nufin kinyi aure mufida?" ta gyada kai eh da yarona daya ma" sai kuma tai shiru tana nazarin Ruma tana sake mata kallon tuhuma sannan tace "no Ruma bakiyi aure ba,,,, Ruma ta dubeta da mamakin ya akayi tasan hakan,  "as far as i know patient din danayi wa aiki ba matar aure bace, anyi mata artificial ne kawai ta haihu and she's a virgin shiyasa muke ganin bazata iya haihuwa ba, muka saukaka mata muka mata aiki" sai ta sakeyin shiru tana kallon Ruma data maida kallonta zuwa gefe tana mai hadiyar abu mai daci, a hankali mufida tace "ina Abdallah?" meya faru bayan rabuwarmu, i can see there's untold stories, ki fadamin pls Ruma?.... Ruma tayi shiru tanajin wani radadi a zuciyarta mufida ta kasa haquri ta cigaba "Kema kin zama doctor?... Mun cika burinmu?  Ina dady ina momy naga kin chanza kamar bake ba...." take Ruma ta fashe da kuka, mufida tayi shiru tana kallon Ruma she knows akwai wata a kasa, ko kallan Ruma kayi zakasan bata cikin farinciki,  bata walwala ta chnja ba haka skin dinta yake ba, ba kamar waccan Ruma ba er gayu er momy er dady... Mufida ta shiga aikin lallashi kafin da kyar Ruma tayi shiru, nan ta soma amayar mata da yadda rayuwarta ta sauya cikin shekarun da suka gabata bayan rabuwarsu... Mufida ta narke kuka wiwi kamar ba likita ba, tausayin Ruma ya lullubeta, Ruma ba karamin dadi taji ba datayi kukan sai taji kamar an dauke duk wata damuwarta ne dataga mufida...... Saida Ruma ta dade tana lallashin mufida kafin ta haqura nan itama ta sanar da ita yadda rayuwa ta tafi bayan tafiyarta kaduna
"mun koma kd cikin family anan na cigaba da karatuna, nayi medicine a nan Abu zaria, tun kafin na kammala na samu miji nayi aure, ya cigaba da daukan nauyin karatuna kasancewarshi me son karatun sosai, with all his support da taimakon Allah na kaiga matsayin danake na haifi yarona daya shekarunshi 3 yanxu" ba kadan ba Ruma taji dadin yadda rayuwar mufida ta kasance, mufida tace "ko ina Abdallah yanxu?

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon